Sanadin Caca Book 2 Complete Hausa Novel By hausanovels001
Sanadin Caca Book 2 Complete Hausa Novel By hausanovels001
-BOOK 2 (PAID)
Mallakar *SADI-SAKHNA*
09035784150
Bismillahir-rahmanir-raheem
Ki biya kan ki karantamin na biyu dan Allah 🙏🏼 ga number ta nan mai son littafi na
ɗaya yayi min magana zan bashi shi kyautane.
Ina ƴan mata dakuma Matan aure masu muradin burge mazajensu da ɗinkuna zuƙa zuƙa.
*PHEEDY TOILORING DESIGN*,suna gabatar muku da ɗinkuna kala kala wanda sukayi
daidai da zamani.
Zaku samemu a kan wannan layin waya kamar haka
09167130115
Wato a manhajar whatsapp. Domin ganin kalolin samufurin aikinmu kuma ku tuntubemu a
INSTAGRAM da kuma TIKTOK a @pheedyxacks_ragtrade
*BOOK 2*
...1...
Yana shigowa kaman yanda Sadeeq yayi shima haka yayi,ganin wani a akan kujera mai
kama da ɗansa,wanda ya fidda saka ran ganinsa tsawon shekara biyar,yau gashi yana
kallonsa a gabansa tamkar alamara.
A hankali yake tafiyah har yana dafa hannun kujera saboda kar ƙafafunsa su kasa
ɗaukarsa i zuwa ga gudan jinin nasa..
Hannu yakai wanda yake rawa kan kumatun Ahmad ɗin,wanda yayi tafiya cikin duniyar
suma bai san mai suke ba.
"Ah......ahhmmad dama kana raye duk tsawon wannan shekarun,toh ina ka shiga hakane
bamu sani ba,ya akayi labarinka ya bace ƙasa ko sama babu shi babu alamarsa?"
Ɗagowa idanuwansa yayi ya kalli detective Sadeeq bayan lokaci daya ɗauka yana
sambatu ma ɗannasa.
A tsaye yake kyam tun shigowar AM Aliyu yana kallonsu,saidai ya juyo tukunna ya
rusuna.
"Sadeeq kacemin daya shigo ƙalau yashigo,to menene ya sakashi yin haka?"
"Am Abbah Nima bansani ba,kawai kafin ka shigo ya riƙe kai,saikuma ya naga ya suma"
"Kuma mai ake jira,kalli fah jikinsa kaman bashiba,maza ka sanar da masu kulada
samfuri maza a shirya private jet na fita dashi waje,yana buƙatar a yimasa gwaje
gwaje a duba lafiyarsa,a ƙalla ya samu hutun shekara biyu kafin ya dawo""
"To abbah an gama,yanzunnan za'a shirya komai kaman yanda kace"
Yana gama faɗin hakan kuwa a take aka fara shirye shiyen fitada Gen Ahmad ƙasar
waje domin a duba lafiyarsa.
Kasancewar abune na masu hannu da shuni,kafin dare an gama komai sun ɗaga
Egypt,shikaɗai AM Aliyu ya tura shi,dan dama yawancin rayuwarsa a can yayi,bazaiji
wani wahalar zama ba.
Sameer ne a zaune a falo da remote a hannunsa,wani film ɗin sojoji yake
gani,gabaɗaya yabada hankalinsa ga wajen. Gefensa kuma Fatee Ce tayi kicin kicin
kaman zata fashe dan haushi,sai zabgawa Sameer harara take ta gefen ido,Maimuna ce
ta kulada itah,wacce take a zaune a opposite ɗinta tana danna labtop.
"Kai Fatee da wanann hararar kije ɗakinki mana kiyi,kina fah da komai a side ɗinki
ba wai bakida shi ba,menene na wannan fushin haka"
Maimuna tayi mata magana cikin sanyin rai,amma ko a jikinta kamam an mintsini
kakkausa.
"Haba anty Maimuna ya zakice haka,bakya ganine nice fah na fara ɗaukan remote ɗin
amma ya kwace,sai mutum yayi magana ace za'a dakeshi dan anfishi ƙarfi,miye abin
kallo a waɗannan gardawan"
Ta faɗa tana nuna tvn,shikuwa Sameer yana jinta amma babu abinda yace,saima ƙara
volume da yayi,tafi kowa sanin shuru yayi,ana jimawa idan ta cikashi zai mata
duka,saboda zafin zuciya gareshi kaman mahaifiyar tasu.
"Ai wlh ma saina faɗawa Abbah,yana tafiya aiki kake dawowa gida ka damu mutane"
Ajiye remote ɗin yayi tareda sakin ajiyar zuciya yanayimata kallon takaici.
"Ke wai ina wasa dakene,kodan kinga kece ƙarama a gidannan sai akace kiyi yanda
kika ga dama,ai ummah bata nan kiyi hankali kona kakkaryaki anan wajen,zakice wani
saikin faɗawa Abbah cewar ina dawowa daga wajen aiki,to in kin fasa,ko kinace banda
labarin fashin da kike na makaranta. To duk mu faɗamasa mana"
"Ehh naji amma ai bana bin saurayi yawan shaƙatawa dai"
Taƙarisa maganar tana murguɗa baki.
Sakin baki Sameer yayi yana kallonta,ya tashi zai bugeta kenan yaji wayarsa tayi
ƙara,tsayawa yayi tareda duba wayar. Wani ɗan wajen aikinsu ne ya ƙirashi dan haka
ya ƙyaleta ya ɗaga a zatonsa ko akan akinne.
Su Maimuna da suke falon sai gani sukayi ya samu waje ya zauna,tareda cewa.
"Mai kake cewa ne,yah Ahmad wai ka gani anya kuwa,kuma har abba ma yaje ya
ganshi?........"
"Wanne Ahmad ɗin?"
Yaji muryar Hajiya Maryam ta tambayeshi,wanda shigowarta kenan ta dawo daga fitar
da tayi da safe,doguwar rigace a jikinta abaya,wacce aka narka kuɗi kafin a
fansheta,saikuma gyalenta data yane kanta,jakarta da kuma takalminta suma designer
ne masu zaman kansu,wanda ko matan gwamna saisun shirya. Shi kansa AM Aliyu yana
mamakin yanda take samun waɗannan kaɗaɗe da take narkawa kanta su,wanda kuma
hakanne ya kankaro mata mutunci a wajen mutane da dama.
"Nace maka wanne Ahmad ɗin,ba tambayarka nake bane?"
Ta sake maimaita maganar tana kafe Sameer da kallo,su kansu sunsan dramar da ake
sha a gidan da mahaifiyar tasu da kuma yayannasu,idan wani ya shiga harkar wani.
"Uhm ummah dama.....dama....?"
"Dama me.!!!?"
Dafaɗa cikin ɗaga murya,shikansa da yake soja saida ya raxana daganin yanda
yanayinnata ya sauya..
"Ummah Ahmad aka gani yau da safe,abba ma yaje wajensa,saidai wai ya suma an fita
dashi ma egypt a lokacin"
"Egypt,kawai daga ganinsa sai a fitada shi akan me toh?"
"Ummah ance bashida lafiya ne bayan ya farfaɗo ɗin"
"Uhm"
Tafaɗa tana sauƙe wani numfashi mai nauyi haɗe da dunƙule hannunta,a lokacin inka
ganta zaka kasa gane inda yanayinta yake,shin baƙin ciki take ji kokuma tsoro da
fargaba.
"Ke Fatee abbanku ya dawo?"
"Ahah baidawo ba ummah"
"Inya dawo ki sanar dani"
Daga faɗin hakan bata sake cewa komai ba tayi hanyar sashenta,dan inda su Sameer
suke babban falon gidanne.
Tun a hanyar ɗakinnata ta fito da waya tana dannawa,da alama wani ko wata take nema
a wayar cikin gaggawa.
"Hello Neelah? Maza ki bincikamin yanzu,shin da gaskene wanda ya bayyana Ahmad
kokuma wani ne daban,ina son bayanai yanzu yanzu,sannan ki tabbatar ba'asan kinyi
ba,karki saka ƙungiya ma a ciki"
"To shikenan Ranki ya daɗe yanzu kuwa zan bincika"
"Idan har ya tabbata shine to da akwai gagarumar matsala,don shirin da mukeyi
gabaɗaya wargajewa zayyi,dan haka ki taka tsantsan ki ganomin komai. Am har yanzu
bakiga wani aikeba?"
"Bangani ba ranki ya dade,amma karki damu Inshaallah babu wata matsala,komai zai
tafi daidai,babu wanda zai gano komai"
"Batun akwatin fah?"
"Uhmm shima dai normal tunda babu wani zance kan gwamnati tanada shi,kokuma
bayyanar sa a wani wajen,dan haka da sannu komai zai tafi daidai"
"Wai to garin ya haka ta faru a bazata,duk shirin da mukayi na ya bata a duniya
saida ya dawo....mtswwww"
Sauƙe wayar hajiyah Maryam tayi,harta buɗe ƙofah zata shiga tajiyo fasa glass a
falon data bar su Sameer. Muryar Mulaifah tajiyo,tasan kuma dama babu mai wannan
abin sai ita,runtse ido tayi tareda jijjiga kai kana ta koma falon.
Center table ɗin tsakiyar ɗakin ta fasa raga raga,tana kuma tsaye fuska shabe shabe
da hawaye.
"Meyasa za'ayimin haka,sanin kowane duk tsawon wadannan shekarun jiran Ahmad nake
da yaƙinin dama nasan watarana zai dawo gareni,to yanzu kuma ya dawo ace wai an
fita dashi abroad batareda na sani ba?"
"Ke Mulaifah wannne iskanci kika zo kinayi a nan wajen,wanene ya damu da jiransa da
kikeyi dazaki zo kin wargazamin gida,kinyi fah ya isheni haka,zanyi mungun
maganinki idan baki nutsuba"
Hajiyah Maryam ce take maganar cikin masifah da takaici.
"Ke wacece dazaki yimin masifah iyaee,dan kina matar gida bashine zaisa ki zama
matar gidaba,kuma gidannan kokiso kokuma ki ƙi inada iko nima dashi,tunda
mahaifiyata ƴar gidance. Nasan wannan masifar da kike dan kinka duk abinda kikeyi
bai yi aikiba saida ya dawo shiyasaka,kuma ki zuba ido ki gani,auren da aka fasa
ɗaurawa saboda mutuwarsa sai an ɗaura shi yanzu ehe"
"Cabɗijan uban mai zayyi dake,kina bazawara sannan kika sani ko a inda yake yanada
mata da ƴaƴa?"
"Ahhhhh aikuwa da saina kasheta na ƙonata,Ahmad nawa ne ni kaɗai,babu wata shegiya
a bangon duniyar nan dazata rabe shi,ba'ayita ba kuma babu itah. Ke kuma ni
kikecewa bazawara ko,dan ma kema uwar taki a bazawarar aka aureta ai......"
Tass hajiyah maryam ta ɗauke Mulaifah da mari a kuncinta na dama,wanda hakan ya
tsaida ta daga masifar da take jajjagawa.
Magana Mulaifah zatayi amma ganin AM Aliyu yasa ta fashe da kuka tareda yin inda
yake.
"Abba kalli ka gani koh,yanda shararamin mari dan kawai nace Ahmad ya dawo,dama
kowa yasan sun tsaneshi basaso ya dawo,abba ka faɗamin a wace ƙasa yake zanje na
ganshi,bazan iya kwana ɗaya va batareda na ganshi ba"
Kuka take tana narkewa kaman ba ita ce ke faɗin maganganu ba a lokacin.
"Shikenan kiyi shuru haka,ke Maryam meyasa kika ........"
Maƙale maganar yayi ganin yanda ta jefeshi da wani arnen kallo mai haɗe da harar.
Juyawa tayi ma tabar wajen ƙwass ƙwass kana jin ƙarar takalminta akan tiles saboda
yanda take taka shi da ƙarfi.
Sauƙe a jiyar zuciya yayi tareda kallon Mulaifah.
"Kinga kiyi shuru haka,jeki wajen Mammah nima yanzu ina zuwa"
Daga haka shima ya wuce nasa sashen,su dai Fatee kallo ne nasu kawai a falon,dan
inda sabo sun riga sun saba da ganin wannan dramar a da,abin lafawa yayi saboda
babu wanda za'ayi rigimar akai,to yanzu da ya dawo za'a cigaba.
Heeho shagali shagali dama wlh nayi missing gidannan ba'a drama,amma yanzu tunda
yah Ahmad ya dawo nasan za'a shigaba da gashi"
"Ke Fatee kinada hankali kuwa,tashin hankali da ake a tsakanin iyayenki shine
abinda kikeso koh?"
"Ahh to ya zanyi anty Maimuna,in kaji haushima ba fasawa za'ayi ba,dan haka gwanda
ka zuba ido kayi kallo ka more....Mulaifah bazata daina haukar nunawa yah Ahmad
soyayya ba,shikuma bazai daina nasan dizgata ba kaman da,sannan mommy bazata daina
nuna masa ƙiyayya ba,yayinda shima bazai raga mata ba.....kinga kuwa ai za'a sha
drama saidai in wani ne ya sanja hali,wanda bana tunanin hakan"
Tana gama faɗin hakan tayi hanyar sashen ta tana waƙa.
A bangaren Mammah kuwa da gudu Mulaifah tashiga kaman an jefata,sakaliyace ta
zubawa a taro,duk da cewar akwaita da masifa a tantiranci,mahaifiyar ta ƙanwar AM
Aliyu ce,bayan ta rasu Mammah ce ta riƙeta maimakon gidan ubanta,wanda hakan yasa
suka shaƙu take ganinta tamkar ƴar ta.
Tun shekara goma baya da Ahmad ya dawo daga Egypt Inda yake zaune ta kamu da sonsa.
Tun yana shareta har yafara tsayar mata na shiga rayuwarsa da take,amma hakan duk a
banza,daga baya ma sai aka saka zancen manya a ciki. Ahmad yana ji yana gani aka
tsaida bikinsu itada shi badan ya so ba.
A na shirin bikinne yayi hatsari ya mutu,bayan haka Mulaifah tayi ta kuka har
ƙaramar hauka saida tayi da mutuwar tasa,tayi aure ma baije ko ina ba ta kasheshi
ta dawo gidan.
Basa shiri ko kaɗan da hajiyah Maryam saboda nuna ikon da Mulaifah take,da kuma
nunawa Ahmad so,a bangaren hajiyah Maryam kuwa kowa yasan bataso taga wani yana
baza iko a fadarta,sannan duk wani abu daya shafi Ahmad bata ko buƙatar jinsa
ballantana da dunga gani.Dan haka bata kawo Allah a wajen magance matsalarta
ballantana mutum,wanda itama Mulaifan haka take a nata bangaren.
SADI-SAKHNA CEH
09035784150
ku tuntubeni domin biyan kuɗinku ko ƙarin bayani.
*SANADIN CACA*
-BOOK 2 (PAID)
Mallakar *SADI-SAKHNA*
09035784150
Bismillahir-rahmanir-raheem
Ki biya kan ki karantamin na biyu dan Allah 🙏🏼 ga number ta nan mai son littafi na
ɗaya yayi min magana zan bashi shi kyautane.
Ina ƴan mata dakuma Matan aure masu muradin burge mazajensu da ɗinkuna zuƙa zuƙa.
*PHEEDY TOILORING DESIGN* ,suna gabatar muku da ɗinkuna kala kala wanda sukayi
daidai da zamani.
Zaku samemu a kan wannan layin waya kamar haka
09167130115
Wato a manhajar whatsapp. Domin ganin kalolin samufurin aikinmu kuma ku tuntubemu a
INSTAGRAM da kuma TIKTOK a @pheedyxacks_ragtrade
A can kuwa Cairo dake ƙasar Egypt Ahmad a kwance yake akan wani gado,jikinsa sanye
da kayan masu jinya,wasu wayoyi aka saka akannasa wanda suke shinshinar lafiyar
ƙwaƙwalwartasa.
Buɗe idonsa yayi a karon farko bayan kawoshi ƙasar,wanda kwanansa uku kenan da
zuwa..
Yauɗin kuma su Sadeeq sukazo dubashi harda Mammah da Mulaifah saikuma Saleem,dan
dama a duk cikin ƴan uwannasa yafi shaƙuwa dashi..
Bayan buɗe idon yana jiyo hayaniya daga ɗan can nesa,amma a ɗakin kam baiji motsin
mutum ba,da alama shi kaɗaine..
Tashi yayi a hankali tareda zubawa na'urar da take gabansa ido.
Waishikam duk sanda ya kwanta a asibiti zai farfaɗo ya ganshi,yaushe yazama hakane
kaman juji? Ko yaushe yana asibiti?.
Ɗan ƙaramin tsaki yaja tareda fitar da ruwa dayake shiga jikinsa,saƙƙo na ƙafafunsa
yagi akan gadon tareda niyyar sauƙa,amma sai ya tsaya jin abu ya riƙe masa kai,suma
a wayoyin cikeda bacin rai ya cire su kafin ya nufi banɗaki,wanda yagani a yamma da
ɗakin.
Fuskarsa ya wanke tareda kallon kansa a cikin madubi,ɗan razana yayi tareda ja da
baya,ganin yanda ya rame yayi baƙi,ya kuma ƙara manyanta ba kaman yanda ya sanshi
ba..
Shin dama da gaskene abinda Sadeeq ya faɗa masa,cewar shekararsa biyar da barin
gida,to a ina yake tsawon lokacinnan,bacci yake tayi sai ya yanzu ya tashi? Ko kuwa
wata rayuwa yayi da bai sani ba kai?.
Zullumine suka cunkushe masa kai,wanda hakan yasa ya fito daga banɗakin.
Cakk ya tsaya a bakin ƙofar banɗakin yana ganin tarin mutanen da suke ɗakin,wanda
duk cikinsu babu wanda kallo ɗaya bai ganeshi ba,amma sai ya basar ya nufi gadon
daya tashi yanzun..
Mammah ce tafara yimasa magana cikeda kulawa.
"Amadu ka tashi ya jikinnaka,babu inda yake yimaka ciwo,amma ka ganemu kuwa"
Kwanciya yakeson yi,amma ganin yanda take zubo tambayoyi yasaka shi kallonta tareda
sakin murmushi ɗan ƙarami.
"Mammah na ganeku mana,ƙalau nake babu abinda ya sameni ciwon kaine shima ya ɗan
sauƙa,taya zan manta ki saidai amma kin ƙara tsufa,kinfara cin goro ne"
Dariya Mammah tasaki cikin jin daɗin maganarsa ,kafin tace wani abu Mulaifah ta
dawo kusada shi da sauri kaman zata wuce jikinsa..
"Honey ka ganeni nima?"
Wani kallon matsa ki bani waje yayi mata,ganin ta dalleshi da manyan idanuwanta
yasa yayi magana cikin ƙosawa.
"Kai Mulaifah wai bazaki sauya bane,gashi a fuska kin ƙara girma amma kinanan yanda
kike,saikin shige jikina kafin ki tsaya komai?"
Bataji haushin yanda yayi mata maganar ba,ƙiran sunanta kawai da yayi ma hakan ya
wadatar da ita,kuma ya sakata cikin farinciki.
Shareta yayi tareda kallon Saleem wanda yake zaune a waje ɗaya shida Sadeeq.
"Gentle bro kaima ka girma sosai,amma yanzu kam ka zama doctor koh,sanda nasani
kana aji ɗaya"
Murmushi yayi shima daya tuna lokacin.
"Ehh nagama yah Ahmad har nafara aiki ma waccar shekarar,Sameer shima yana aiki a
barrack ɗinku,sai Maimuna tana karatun law,Fatee kuma tana makaranta"
"Ban tambayeka ya suke ba ai,naka kawai na tambaya"
Yafaɗa yana tsuke fuska,dukkan su kallon juna sukayi,har yanzu yana nan da
halinsa,ba dama ayimasa gwaninta.
"Oh AA Hamma ni baka ganni bane komai"
Sadeeq yafaɗa cikin tsokana..
"Banganka ba saida kayi magana"
Yana gama faɗin hakan ya kwanta a gadonnasa,suna ganin haka suka fita,da alama hutu
yake so.
Suna fita daga ɗakin ya tashi ya koma banɗakin,dama yayi hakanne saboda su
fita,kasancewar bai saba da zama cikin mutane ba tunda,shiyasa yajishi cikin wani
irin yanayi.
Alwala ya ɗauro ya dawo ɗakin,domin rama sallolin da ake binsa ,ya daɗe yana yi har
saida ƙarfinsa ya ƙare kafin ya dakata.
A wajen Addu'o'i ma ya daɗe nan ma kafin ya dakata.
Jijjiga kai ya fara burinsa kawai ya fitar da tunanin da suke cikin kansa,amma
hakan ya faskara.
Ƙarar buɗe ƙofa yaji,har wanda ya shigo ɗin ya zauna bai ɗaga ido yaga wanene
ba,har saida yayi magana tukunna ya gane Sadeeq ne.
"AA Hamma nasan tunani kakeyi,koma miye ka barshi ba yanzu ba,saboda a yanzu kana
buƙatar hutu sosai"
Bai saurari Sadeeq ɗin ba,saima magana daya farayi.
"Menene haka ya sameni,a ina nake tsawon lokacin nan,wacce irin rayuwa nayi duk
bansani ba Sadeeq,ka yi tunanin ya zanji a halin yanzu,sannan rayuwar wa na
shiga,cutar dashi nayi kokuma kyautata masa duk bansani ba"
"Hakane kam babu daɗi lamarin,amma babu yanda zakayi saidai haƙuri,a hankali
Inshaallah zaka tuno komai,amma yanzu karka saka damuwa a ranka,idan ba haka ba zai
dameka sosai.,Saboda hakannne ma yasa yace ka zauna anan kaman na shekara biyu ko
ɗaya kafin ka koma gida,saboda ka huta sosai"
Jijjiga kai yayi tareda cewa.
"Bazan iya zama anan ba,bayan nasan wanda ya aikata min hakan yana can hankalinsa
kwance,nikuma yasaka rayuwata cikin garari na tsawon shekara biyar"
"Wani mai kake nufi,shin kasan wanda yayi maka hakan"
"Ahah ban tabbatar ba amma nasan najikina ne yayimin,kuma komai yana alaƙa da case
ɗin BC da nake a lokacin,Sadeeq abinda zan fadamaka inaso kabarshi anan harsai na
tabbatar da hasashena. A binciken danayi harda hannun Hajiya Maryam a wani bangare
na ƙungiyar,nagano hakanne bayan na saka na'urar bin diddigi a wayarta da motarta..
Wanda kuma tasan da hakan,amma ga mamakina bata nunamin ta damu ba,hasalima wata
hidimarta tacigaba ta daban.
Sannan a ranar dazan kai wanan shaidar headquater a ranar nayi hatsari,sannan kafin
idona ya rufe dukka naga wata mata da baƙaƙen kaya tazo kaina ta ɗauki na'urar a
jikina. Daga nan bansake ganin komai ba.
Kafin duk wannan ya faru kuma dama na fara jin sauyi a jikina,sai nayi abu bansan
nayi ba,wani lokacin saina dungajin inason na aikata abinda ba daidai ba,har shaye
shaye idan naga anayi sainaji ina so nayi. Kokuma yiwa wani rauni ko lahani.
Abinnan ba ƙaramin firgitani yayi ba Sadeeq saidai babu wanda ya sani,sannan idan
nace zanyi bacci saina kasa sam. Ina cikin wannan halinne wannan abin ya sameni.
Wanda bansan mai ya faru ba sai jiya na dawo hankalina.
Kuma duk kacemin ina cikin wannan halin na zauna na huta?"
Muryar sa tana rawa ya ƙarisa magana,Sadeeq wanda ya zama tamakar gunki sai yanzu
ya motsa jin tambayar da Ahmad yayi masa a ƙarshen bayaninnasa.
"Tabbas wannan ba ƙaramin lamari bane,amma duk da haka kayi haƙuri kasake
warkewa,kafin sannan ni nayi maka alƙawarin zan taimaka maka da dukkan iyawata akan
wannan abun"
"Nagode da kulawarka zan bari na huta ɗin kaman yanda Abbah ya buƙata,amma kafin
sannan inason tambayarka.
Shin ƴan team ɗina sunan nan wanda muke aiki dasu kokuwa?"
"Ehh to Eemran yana nan da Bilal shine ma a kan case ɗin saikuma Neelah"
"Yawwa ka ƙira Neelah ka fadamata zanyi magana da itah zuwa gobe ta shirya"
"Uhm to zan bincika itama naji kaman ana cewa za'ayi mata transfer na wajen aikin"
"Zanyi magana da Abbah akan ya barta,dan a halin yanzu daka kai sai ita kawai na
yarda dasu akan case ɗinnan. Zan cigaba ne daga inda na tsaya,zama na anan bazaisa
na fasa ba"
"Am AA Hamma na manta ban faɗamaka ba,yanzu haka ma akwai wani case da akeyi da
su."
"Case wanne iri?"
"Uhhm wata uku kenan da suka sace nuclear da aka kawo,har yanzu ba gantaba,an bi
diddigi har an gaji"
"What nuclear,abinnasu har yakai hakane wai,they need to stop now"
SADI-SAKHNA CEH
09035784150
ku tuntubeni domin biyan kuɗinku ko ƙarin bayani.
*SANADIN CACA*
-BOOK 2 (PAID)
Mallakar *SADI-SAKHNA*
09035784150
Bismillahir-rahmanir-raheem
Ki biya kan ki karantamin na biyu dan Allah 🙏🏼 ga number ta nan mai son littafi na
ɗaya yayi min magana zan bashi shi kyautane.
Ina ƴan mata dakuma Matan aure masu muradin burge mazajensu da ɗinkuna zuƙa zuƙa.
*PHEEDY TOILORING DESIGN* ,suna gabatar muku da ɗinkuna kala kala wanda sukayi
daidai da zamani.
Zaku samemu a kan wannan layin waya kamar haka
09167130115
Wato a manhajar whatsapp. Domin ganin kalolin samufurin aikinmu kuma ku tuntubemu a
INSTAGRAM da kuma TIKTOK a @pheedyxacks_ragtrade
*BOOK 2*
...3...
SADI-SAKHNA CEH
09035784150
ku tuntubeni domin biyan kuɗinku ko ƙarin bayani.
*SANADIN CACA*
-BOOK 2 (PAID)
Mallakar *SADI-SAKHNA*
09035784150
Bismillahir-rahmanir-raheem
Ki biya kan ki karantamin na biyu dan Allah 🙏🏼 ga number ta nan mai son littafi na
ɗaya yayi min magana zan bashi shi kyautane.
Ina ƴan mata dakuma Matan aure masu muradin burge mazajensu da ɗinkuna zuƙa zuƙa.
*PHEEDY TOILORING DESIGN* ,suna gabatar muku da ɗinkuna kala kala wanda sukayi
daidai da zamani.
Zaku samemu a kan wannan layin waya kamar haka
09167130115
Wato a manhajar whatsapp. Domin ganin kalolin samufurin aikinmu kuma ku tuntubemu a
INSTAGRAM da kuma TIKTOK a @pheedyxacks_ragtrade
A zaune take tasaka tsinin ciki a gaba da kwanon abinci akan cinyarta..
Ta kumbura tayi ƙatuwa,ga wani uban girma da cikinnata yayi kaman an saka babban
mutum a ciki.
Hankalinta kwance take cin garin kwakin kaman ance ta cinye kan wasu su shigo.
Tun daga zaure take jiyo hayaniya tsakanin kursiyyah da Deejah,wanda abune da ya
kamata ma su saba dashi,duk sanda aka sakasu sharar gida ko ɗiban ruwa sai sunyi
faɗa. Kuma duk yawanci Deejah ce take dukan kursiyyah,gaji tayi masifar har abin ya
isheta,tunda ta kula Deejah ba rage mata takeba,gashi batajin maganar kowa idan
bata Sumaimah ba.
Yanzun ma kaman kullum shigowa sukayi kursiyyah tana kuka da fashashshen botiki a
hannunta,sai Deejah wacce tashigo tana ciccije baki,itama da botikin a hannunta
amma bai fasheba.
Hanyar ƙofar su kursiyyah tayi,yayinda Deejah kuma ta iyo inda Sumaimah take zaune
tasaka kujera a bakin ƙofar goje.
Da kallo ta bita na alamar tambaya,amma sai tayi biris kaman batasan mai take nufi
ba.
"Mai kikayi mata naga kun shigo tana kuka,waye yafasa bokitin hannunta"
Tun kafin Deejah ta buɗe baki tayi magana sukaji muryar gaji tana masifah,fitowa
sukayi da tana riƙe da hannun kursiyyah.
"Wannan wanne irin iskanci ne,komai aka ga dama sai ayimaka in kayi magana ace kai
jarababbene,to wlh bazai yiyu ba,babu wanda yake ban ci ballantana sha. An kawo
bare yazo ya kanainaye gida hadda yin aure,saboda bala'in da aka sakashi a gaba ya
gudu ana shirin shekara babu shi babu ɗuriyarsa,hakan bai isaba sai itama matar da
batada gindin zama a gidan ta kawo wata ɗosun ɗosa nan tana takurawa ƴaƴan gida? To
bazai yiyu ba haka sam"
"Kai gaji kai gaji,waini kam yaushe zaki girma ne ki daina waɗannan abubuwan"
"Dakata Mairo dama nasan zakice haka,barni nayi na more,duk tsiyata dai da masifah
ta ban kori mijina da baƙin hali ya tsallake ya barni ba"
"To ita wanene yace miki guduwa yayi ya barta,in ma guduwa mai naki na wannan
magana"
"Heee to in ba guduwa yayi ba fatalwa ya koma a gidan yake rayuwa idon mu baya
ganinsa,wayasani ma ko cikinne ba nasa ba ko kuma lasarsa take da daddare shiyasa
ya gudu"
"Gajiiiiiiii!!!!! Duk abinda zaki faɗa ki faɗa,amma ki daina sheganta min ɗa ko
kuma yimin sharrin maita,dan bazan yarda da wannan ba,akan hakan zan iya kaiki
ƙara"
Hakan da Sumaimah tafaɗa ya razana ta,domin tariga tasani duk lokacin data kai
Sumaimah bango bata jin shakkar maida mata martani.
Duk da haka da masifah tana cinta bata yi shuru,ta ɗage gefen zani sai masifa take.
Deejah wacce take tsaye abin yayi mungun isarta,gashi Sumaimah ta hanata idan gaji
tana masifa ta tanka,shiyasa babu yanda zatayi tai shuru.
Dafe goshi Sumaimah tayi tana jin gaji wacce take ta bambami akanta,marar ta taji
kaman wani abu ya keta mata,hakan yasa ta ajiye kwanon hannunta tareda da dafe
wajen.
Muryar inna taji tana magana.
"To ikon Allah Sumaimah ruwa fah kike zubarwa,ko haihuwa ce kai?"
Bin wajen da inna ta kalla tabi ta kallo itama,kaman dama wacce take jira a
gane,nishi ta fara tana kama ciki. Komawa ɗaki inna tayi da gudu ta ɗauko kayan da
suka shirya na haihuwar..
Tunga ne ya ƙira mota aka sakata zuwa asibiti,dan dama sunce idan zata haihu a
kawota asibiti kar a barta a gida. Saboda tun cikin yana ƙarami jininta ya hau,bai
sauƙa kuma sosai ba har zuwa lokacin.
Kai tsaye ɗakin labour aka wuce ta ida,harta fara fita daga hayyacinta..
Ƙarbarta nurses sukayi zuwa ciki,ganin yanda numfashinta yaka sama sama.
Inna ban kuka babu abinda takeyi,Tunga ne da Deejah basuyi kuka ba,saidai fuskarsu
ta nuna tashin hankali.
Nurse ce tafito daga cikin ɗakin fuskarta ɗauke da murmushi.
"Mashaallah ta sauƙa,saidai jikinta yayi laushi yana buƙatar kulawa."
"To amma mai ta haifa?"
Inna ta tambaya cikin nuna damuwa.
"Ta samu ɗa na miji,amma shima bazaku samu ganinsa yanzu ba,saboda baya motsi
sosai"
"To mashaallah Allah ya rayashi bisa sunnah,itama Allah ya bata lafiya. To yanzu
kuma me dame za'a buƙata wa ita mai jegon?"
"Eh to a yanzu kam babu,yawwa kada a yi mata wanka da ruwan zafi,za'a rubuta
maganin da zatayi amfani dashi"
Har ta tafi dawo tayiwa innan tuni,saboda tasan halin taurin kai irinna mu na
mutanen ƙyauye.
"To shikenan Inshaallah zamu kiyaye,mun gode sosai sosai"
Yanzu inna sai murna take kaman ba ita bace take kuka ba ɗazu.
*SUMAIMAH (POV)*
Tashina kenan ban daɗe ba,abin yaban mamaki wai kwana nayi kass ina bacci,duk ma
nasan allura ce sanadi..
Tunda na tashi ishirwa take damuna,har na shanye cikin jug nan da nan,dam ma inna
ruwan zafi take bani,gashi bana so haka na daurewa na ƙarba.
Shafa cikina nayi,duk da yana nan da girmansa amma ba kaman jiya ba,wai dama duk
ƙaton cikinnan dayake jana a hnayar makaranta ɗa ɗayane a cikinsa,kai gaskiya to
kato ne inaga..
Nikaɗai nake wannan tunanin a raina,dan bansan ya yaron yake ba,yanzu ne ma wata
nurse suka fita itada inna su kawomin shi.
Ikon Allah wai nice na haihu kuma ɗan goje,abinda ban taba kawowa a raina ba
kenan,haka wai gojen zai tafi ya barni har tsawon wannan lokacin.
Ƙarar murda ƙofa naji,hakanne yasa na juyo da kaina ina kallon mai shigowa..
Inna ɗauke da yaron a hannunta,sai Deejah wacce take binta a baya.
Tahowa take amma gani nake kaman bata sauri,domin na matsu naganshi.
Hannu nasaka na karbeshi,duk da jikina bashida wani ƙarfi sosai.
Bacci yakeyi abinsa baisan ma mai duniyar take cikiba,yana kamada goje sosai,saidai
kuma ban san miye ba amma akwai wani abu irinnawa a fuskar tasa.
"Anty Sumaimah dawa yake kama toh,nidai kama yakemin da wani ɗan jikin calender a
ƙofar chemist ɗin anguwarmu"
Kallon bakida hankali har yanzu Sumaimah tayi mata kafin tace.
"To dama dole yayi miki kamada shi mana tunda shima jinjiri ne koh"
"Ehh to hakane,ɗazu da aka shige dake inna tayi ta kuka hhjhhhh dama ashe haka take
kuka,waiwai gotal kenan"
Fashewa tayi da dariya tana nuna inna da yatsa,wanda hakan yasa ta kaimata duka
tayi waje da gudu.
Dariya mukayi nida innan,wai hakan ma da sauƙi tunda bata dukan yara a makaranta
sosai,kuma wata shekarar nakeson sakata a JSS one,tunda nayi magana sunce zasu
karbeta indai zata iya karatun. Ban faɗawa inna ba har yanzu,amma kuma kafin na
haihunnan nafara koyamata karatun secondry ɗin.
"Allah ka shirya khadija"
"Ameen fah,ai wannnan yarinya sai gyaran Allah"
Inna ta faɗa.
"Uhm inna shin wanne suna za'a saka masa ne?"
Saida nayi maganar ne na tuno ashe bamma san sunan goje ba na ainihi,wannan shi ake
ƙira gallo.
A zabure na kalli inna tareda yimata tambayar..
"Tabb inna wai menene sunan gojene na ainihi,koda gaskene sanda aka sameshi babu
wanda yasan komai nasa?"
"Uhhh Sumaimah na faɗamiki ki daina wannan zancen,kawo yaronnan nan kigani"
Jin abinda ta faɗa yasa na ɗora mata dan akan cinyarta,cikeda kulawa da ƙauna take
kallonsa har ta ɗora bakinta a kunnensa,ta ɗan dau lokaci kafin ta juyo ta kalleni.
"Nayi masa suna da Muhammad. Wato yazama Muhammad Ahmad Hamma kenan"
"Hakane sunan goje na ainihi,Allah ya rayashi,to amma taya kika san laƙaninsa?"
Nafaɗa cikeda mamaki,dan ina cikin duhu diɗim da lamarin rayuwar uban ɗannawa.
"Kinyi min alƙawarin bazaki ɗaga wannan zancen ba sai bayan kin haifi abin cikinki
kuma kin gama makaranta,dan haka dan Allah ki bar zancennan ba yanzu ba."
Ba hakan naso ba amma nariga na yarda da hakan tun watannin da suka wuce,Inshaallah
zan jira wannan lokacin har yazo.
"Amma zan iya ɗan sakaya masa sunan kaman nace Sayyid"
"Hakan ba matsala Allah ya rayashi bisa imani"
Ahmad na maimaita a raina,suna mai daɗi amma ake ƙiransa da wani goje.
A ranar aka sallamemu muka tafi gida,kasancewar na farfaɗo kuma babu wata matsala.
Tunda mukaje asibitin ammi ce kawai taje,shima ina kwance bansan taje ba.
Ranar daza'ayi dakan yaji dama ban saka a raina za'ayimin komai daga gidan mu ba.
Inna ce ta yankamin kaji guda biyu wanda take kiwo a can ƙyauyensu.
Abin suna kuwa dama tun cikina yana ƙarami ta siya ta ajiye a garinnasu,ana gobe
suna aka kawoshi,ragone amma ba babba sosai ba,saidai kuma baza'a ce masa ɗan
ƙarami ba.
A zaune nake ranar sunan da safe ina bawa sayyid abincinsa,hankalina gabadaya ya
karkata kansa,maganar Shareefah naji tamkar a sama,yaushe ta dawo na faɗa a
raina,don ita a boarding take makaranta.
"Mashaallah ƙawata da beautiful baby,sauƙata kenan a garin naji wannan labarin."
Murmushi nayi cikeda jin daɗin ganinta.
Gaisawa mukayi na yaushe gamo,miƙa mata yaron nayi sai tubarakallah take cewa,ba
yabon kai ba kam kowa yaga yaronnawa sai ya faɗa,kyakykyawa dashi gashi ba rama a
jikinsa.
Nima kuma lafiyata ƙalau,iya kula muna samu a wajen inna sosai,dan ranar sunan ma
lace ta ɗinkamin ja mai kyau.
Lokacin dana ga abubuwan da tayi mana har kuka saida nayi,domin abun ya bani mamaki
sosai,abinda inna takeyimin ko mahaifiya ta iyakaci.
Anyi daɗi anyi ba daɗi dukka a taron sunan,har aka watse kowa yakama gabansa,aka
barni dagamu sai halinmu.
Washagari da safe hayaniyar a da ake a cikin gidanne ta tasheni,dan yanzu na dawo
ɗakin inna kafin nayi arba'in.
Muryar inna ce da kuma gaji suna sa'insa.
Wai gaji ce ta tashi da sassafe ta ɗauko wuƙa zata fara aikin naman suna,ita kuma
inna tace bata yadda ba. Duk aikin da akayi a gidan babu wanda ta taya sai wannan.
"Amma dai gaji bakida kunya,tunda muka dawo daga asibiti ƙafata tana ciwo,amma baki
tayani da komai ba na aiki sai yanzu,dayake nama ne zaki fito sassafe kifara
gyarawa"
"Ohh kura kika maidani komai,kina nufin kice saboda namane shiyasa nazo nake
tayaki?"
"Ahh to da ba haka bane,kinyi wani aikinne bayanshi,dan haka ki barshi zamu
gyarashi nida Deejah,tunda na da bai kashemu ba na yanzu ma bazai kashemu ba da
ikon Allah"
"To shikenan dama ba'ayi muku gwaninta,saikuje kuyi kayanku gayyar tsiya arna a
idi,uban ɗan ma ya gudu ya barku ai ballantana wani"
Ni dariyama abin ya bani danaji maganganunnasu,narasa meyasa gaji bata jin kunyar
yin wani abun.
Gidannamu kenan ko yaushe wasu abubuwan zasu zama tarihi oho,ji nake a jikina kaman
wasan yanzu ma aka fara.
SADI-SAKHNA CEH
09035784150
ku tuntubeni domin biyan kuɗinku ko ƙarin bayani.
*SANADIN CACA*
-BOOK 2 (PAID)
Mallakar *SADI-SAKHNA*
09035784150
Bismillahir-rahmanir-raheem
Ki biya kan ki karantamin na biyu dan Allah 🙏🏼 ga number ta nan mai son littafi na
ɗaya yayi min magana zan bashi shi kyautane.
Ina ƴan mata dakuma Matan aure masu muradin burge mazajensu da ɗinkuna zuƙa zuƙa.
*PHEEDY TOILORING DESIGN* ,suna gabatar muku da ɗinkuna kala kala wanda sukayi
daidai da zamani.
Zaku samemu a kan wannan layin waya kamar haka
09167130115
Wato a manhajar whatsapp. Domin ganin kalolin samufurin aikinmu kuma ku tuntubemu a
INSTAGRAM da kuma TIKTOK a @pheedyxacks_ragtrade
*BOOK 2*
...5...
"Ke maza kiyi abu da jiki,menene haka kaman bakida laka a jikinki,idan har ya iso
baku gama komai ba sainayi mungun saba muku"
Cikeda masifa Mulaifah take magana,gabaɗaya duk ta fita daga hayyacinta,bayan
wannan tsawon lokacin yaune Ahmad ya yanke shawarar dawowa gidan,dama Abbansune ya
damu akan ya zauna jikinsa ya dawo yanda yake.
Kawai dai yana can ɗinne,amma plan ɗinsa gabaɗaya babu wanda ya tsayar dashi,komai
yana tafiya normal a tsaikaninnasu shiga abokan aikinnasa,wato Eemran da Neelah.
Yanzu ma buƙatar dawowarsa office ce ta taso shiyasa zai dawo gidan.
Hajiyah Maryam wacce ke zaune a falonta ko gezau batayi ba,tunda AM Aliyu yace mata
Ahmad zai dawo daga to bata sake tari ba.
Iya Maimuna ce da Saleem kawai suke murna,saikuma murnar Fatee wanda dan taga yanda
abin zai ƙare shiyasa takeso ya dawoɗin. Sameer kuwa an turashi can wajen gyembu
wani aiki (Zasuyi bincike akan ƙungiyar BB ta bombi dake cikin dajin)😁😁😁.(uhm
mutanen littafin BAƘAR AYAH) munayi musu fatan NASARA littafin na Maman Abdoul.
Allah ya bar ƙauna...........
Mammah wacce ta fito daga sashenta zuwa babban sashen gidan,jijjiga kai tayi ganin
yanda Mulaifah tun safe ta gagara zaunawa,ta haɗa abincin da ko mutane goma bazasu
iya cinyewa ba,duk wai akan mutum ɗaya.
Kowa tausayinta yakeji,yayinda wasu kuma irin Fatee mamaki take basu.
Daidai misalin ƙarfe 1:30 na ranar asabar ɗin jirgin nasu ya sauƙa wanda ya taho
daga Egypt ɗin.
Shine mutum na uku daya saƙƙo a jirgin,suit ne a jikinsa baƙaƙe,wanda suka dace da
fatar jikinsa wacce tasha hutu mai aji. Ahh dole kam Sadeeq da Abba suce yayi baƙi
farkon ganinsa da sukayi,danni ma yanzu na yarda da zancennasu.
Jakace briefcase a hannunsa ba wata babba ba,saikuma ɗaya hannun yana riƙe da
trolly mai matsaikacin girma.
Fuskarsa babu murmushi kana kuma babu akasinsa,a takaice dai bazakace ga abinda
yake saƙawa ba aransa.
Cikeda taƙama yake tafiyar kana ganinsa kasan babu wasa.
Tun daga nesa ya hango drivernsa na da wanda yake masa aiki,da saurayine amma yanzu
ya ƙara girma.
Lallai an ɗau shekaru kam,yafada a ransa.
Yana ƙarisowa ya miƙa masa jakarsa tareda bude bayan motar ya shiga.
Jingunuwa yayi a jikin kujerar tareda sauƙe ajiyar zuciya,ba ƙaramin gajiya yayi
ba,tun safe bayyi wani ƙwaƙwƙwaran zama ba,saboda ciku cikun dawowar tasa.
Yayi tunanin ma zaiga su Mulaifah sunzo daukarsa,da alama basu manta yanda ya tsani
yaga ana tara masa jama'a ba.
"Ya kke umaru ya bayan lokaci"
"Ahh ogah ka ganeni ne?"
"Ohh meka maidani,saboda bana nan na tsawon wasu shekaru sai akacemuku na rasa
hankalina? Bama wannan ba wanne aiki kake bayan bana nan?"
"Uhm ai ogah ina fadamaka bayan tafiyarka da wata shida nayi aure,ga aka koreni
daga aiki,na tuka wata kantar ɗiban itace haka haka dai rayuwar ta dunga
garamin,kwatsam ina zaune sai Neelah tacemin wai kana nemana na dawo aiki. Jinayi
tamkar a mafarki. Nagode nagode ogah"
Da ɗan kukansa ya ƙarisa maganar,a haka har suka isa gidan suna taba hira jefi
jefi.
Mulaifah tanajin shigowar motarsa gidan ta fito da gudu,dan dama tun ɗazu take
leƙawa,yana fitowa daga motar yaga Fatee a gabansa,a ransa yace yaushe wannan kuma
tafara murnar ganina.
"Ke kuma fah?"
"Ohh yah Ahmad murnar dawowarka nake mana,zamu sha kallon shagali a gidannan"
Kafeta yayi da ido kafin ya tureta ya wuce,yana kawar da itah yaga Mulaifah tana
tsaye ta haɗe fuska,dariyar Fatee ya jiyo a bayansa,sai a sannan ya gane ashe bawai
murnar dawowar tasa bace,tsokanar Mulaifah take. Tun sanda ya santa lokacin tana
ƙarama haka take da rigima,ashe girman ma bai saka ta daina ba.
Tahowa yayi zai wuce ta gefenta,tayi saurin tarar sa tareda narke fuska.
"Hubby ya zaka wuce,baka ganni bane,tun ɗazu nake jiran dawowarka fah"
Gaba yayi abinsa tana binsa tana surutu har suka shiga gidan..
Akan dinning ɗin da aka cika da abinci idonsa ya sauƙa,wanda yasan bazai wuce aikin
Mulaifah ba,ko cewa yace mata a tsawon lokacinnan babu abinda ya koya sai cin
abinci oho.
"Hubby ka tsaya kaci abinci mana"
Ganin yayi hanyar sashensa wanda sai anbi ta wani corridor a isa wajen,domin yana
can ƙarshen gidan.
"Hubby ko nazo na tayaka shiryawa naga ka gaji sosai"
Tsayawa yayi tareda wurga mata wani kallo,ganin da gaske take dan sakarci binnasa
zata yi,wani kallon ma amsa ce,bata san lokacin data yi burki ba.
Fatee kuwa mai take jira ta tuntsire da dariyah.
Muryar Mammah sukaji a bayansu tana magana.
"Naji ana cewa mai sunan manya ya dawo,ina yayi ne banga ya shigomin ba?"
"Mammah ya wuce sashensa,kaff a gidan ma babu wanda ya kula,har wacce tayi ta
hidima har asubar ma bata samu kallon arziƙi ba"
Jimm Mammah tayi tareda cewa.
"Ƙalau yake dai koh,inaga ya gaji ne shiyasa"
Daga haka ta juya sashennata,sauƙe ajiyar zuciya Maimuna tayi tareda cewa.
"Gaskiya yah Ahmad baya kyautawa da irin wannan halinnasa,yana nan dai wato bai
sanja ba sam"
Daga haka itama tabar wajen ranta cikeda haushin yayannata.
Banda mutuniyar ita ko a jikinta,yanzu ma zata sake zage dantse wajen ganin ta
mallakeshi.
Hannu ya saka a kunkuminsa yana kallon falonnasa,babu komai a ciki sai fararen
kujeru da Tv stand sai cerpet a tsakiya.
Ɗakuna biyune a side ɗin kowanne da banɗakinsa sai kitchen.
Ɗakin farkon ya buɗe ya shiga wanda dama shine nasa tun kafin ya tafi..
Shima kaman yanda yake a da hakan yake,kai tsaye banɗaki ya fada ya watso ruwa
tareda ɗauro alwala.
Bayan ya idar da sallah yana tun kafin yagama Addu'o'i yaji wayarsa tayi ƙara.
Miƙa hannu yayi ya ɗauka,sunan Eemran ya gani,hakanne yasa ya ɗauka da sauri.
"Hello sir barka da isowa"
"Yawwa naga ƙiranka,shi kun samu wani abinne?"
"Ehh yanzu Neelah ta ƙirani wai ta samo wani underground a nan garin,kuma bashi da
nisa da gidan ajiyar muhimman abubuwa na ƙasa,da alama dashi akayi amfani wajen
satar da akayi shekara biyu da suka wuce"
"Shikenan gani nan zuwa yanzunnan"
Da sauri ya tashi kaman an tsikareshi ya fita daga ɗakin.
Mulaifah wacce take zaune a wajen dinning sai jin motar sa tayi ya fita daga
gidan,da alama taƙofar baya ya fita da take sashensa.
Address ɗin da Neelah ta turo masa ya bi,nan da nan ya isa wajen.
Daga waje mutum zai ɗauka cewar gareji ne a wajen,sai ya shiga yaga ƙofa a wajen
wacce zata kai mutum zuwa gidan ƙasan.
Tafiya yake yana nazartar ginin wajen,mutum yana gani ma yasan akwai hannun wani
babba akan aikinnan,inba haka ba taya barayi zasu samu damar yin wannan gidan.
Ba wannan ne ya girgizashi ba saida yayi arba da harabar cikin wajen,yaushe aka
gidannan wajen toh. Yayiwa kansa wannan tambayar.
Eemran ne da Neelah suke jajjagawa suna kallon abubuwan.
Neelah ce tafara ganin shigowar Ahmad da sauri taƙame tareda sara masa,jin haka
yasa shima Eemran ya juyo yayi yanda tayi.
"Sannun ku da aiki,amma Neelah ya akayi kika san wanann wajen,bayan duk binciken da
muke babu wani clue daya kawomu nan wajen?"
"Uhm jiyane nashiga napep cikin badda kama,anan yake cemin ya taba ganin wani
jirgin sama ya sauƙa a filin waje shekara biyu baya da daddare,Sannan wasu mutane
da baƙaƙe kaya sun fito daga ciki sun shigo garejin,hakan yasa nace ya kawoni
wajen. Da nayi bincike saina na gano ashe gidan sirrine"
A dake take bada labarin babu gargada,wanda hakan yasa Ahmad jinjina mata,duk da
cewar bai daɗe yana aiki ba hatsarin ya sameshi amma yasan itaɗin jajirtacciya
ce,wanda ya gwada ta hanyoyi da dama tana tsallakewa,shiyasa ya yarda da ita sosai.
Ɗakunan cikin wajen suka fara duddubawa,anan har suka shigo ɗakin da goje ya zauna.
Wani dumm Ahmad yaji kansa yayi masa,tunda ya shigo gidan yakejin haka,wande Neelah
tana kulada shi amma banda Eemran wanda yake ta rubuce rubuce.
"Yallabai lafiya dai naga kaman kana riƙe kai"
"Cikeda kulawa tayi magana,duk da a cikin yanayin aiki tayi tambayar"
"Ahhh bakomai kawai inajin wani yanayine gameda nan wajen,bansan meyasa ba"
A haka dai suka gama dube dubensu kafin suka sanarda headquarter abinda yake
faruwa.
___∆∆∆___
Tafiya nake ina sauri na isa gida,dan nasan Sayyid Yana can ya damu inna da rigima,
dan ma nasan Deejah ta dawo daga makaranta yanzu.
Ina shawowa kwanar gidannamu naga mutane a ƙofar gidan sunyi zanga zanga,gaba nane
ya buga,don a zatona ko mutuwa akayi,saida nazo kusa kafinnaji mai suke cewa.
"Wlh bazamu yarda ba,dolene sai an biyamu kaff asarar da goje ya jawo mana a
garinnan,inba haka ba mu koreku daga garinnan"
Hasbunallahu wa ni'imal wakil,yaukuma? Meya taso wannan maganar bayan shekara
biyu,wato tunda tsoro suke kar suje ya dawo,yanzu kuma da sukaga an dau lokaci
sunsan bazai dawo ba shiyasa zasu tona mana asiri.
Wasu hawayene suka zubomin,shin da wanne mutum zaiji,da rashinsa kokuma da tashin
hankalin su.
Kaman bazan ƙarisa ba saboda tsoro da fargaba da suka kamani,amma kuma ina zan gudu
naje na bar ɗana gudan jinina,da dattijuwar dana ɗauka tamkar uwata,ko kuma
yarinyar dana ɗauka tamkar ƙanwata ta jini?
Hakan yasa nayi shahada na nufi bakin gidan,suna ganina kuwa suka yo kaina kaman
nice naci musu kuɗin.
Wasu kamma dan cin mutunci harda jan hijabi,wani baƙin cikine ya isheni,ina juyawa
naga wani saurayi ne,ana hayaniya shikuma sai ƙoƙari yake yaga ciremin
hijabina,haushine da takaici ya ɗebeni bansan lokacin dana wanka masa mari ba.
Faruwar hakanne tasa wajen yayi tsit kaman ruwa ya cinyesu,kowa kallonmu yakeyi a
wajen,yayinda shima ya kafamin ido hannunsa riƙeda kumatunsa,da alama yayi mamakin
marin danayi masan.
"Bin bashin haukane da kake shirin yimin tsirara a cikin bainar jama'a,ko kuma a
gidanku ba'a koyamaka mutunta mata ba musamman matan aure?. Kunzo ƙofar gidan
mutane kaman zaku shiga,a bayaninku naji kuna cewa kun yashe shagon da muka buɗe
muna ciyar da kanmu. Ina tun ƙahonku goje yayi muku barna,shin labari aka baku mun
boyeshi tsawom wannan lokacin,ko ba manya da masu faɗa a ji da kuke mana tujara
haka?
Kunata zaginsa cewar ya yimuku ba daidai ba,ai gwanda shima ba a taba cewa yaje ya
cutarta marasa ƙarfi ba,kokuma cin mutuncin matar wani ba,amma kufah ku kalli
abinda kukeyi mana?.
Duk abinda kuke cewa yacimuku ina a wajen caca ne kokuma in kunshiga harkasa yayi
muku,shin to ku faɗamin nina ce me,ban taba yin magana dashi ba sai sanda aka
kawoni gidansa,idan ku kuɗinku yaci ni ga nawa iyayen ɗiya ya ɗaukemusu,amma bance
komai ba banje wajen wani na roƙeshiba,na tsaya da ƙarfina muna rufawa kanmu asiri
kunzo kun wargaza komai"
Kuka ne ya kufcemin na kunci da halin ha'ula'i da suka taru sukayimin waya,yanzu
dawowa ta mungama da makaranta kenan akan bazasu bani cartificate ba saina kai dubu
hamsin, ina tunanin yanda zanyi kuma ga wannan.
Muna cikin haka inna tafito daga gidan kanta da mayafi ta jani ciki,banda kuka babu
abinda mukeyi,abinka da daman cikin ya haɗiya da yawa.
SADI-SAKHNA CEH
09035784150
ku tuntubeni domin biyan kuɗinku ko ƙarin bayani.
*SANADIN CACA*
-BOOK 2 (PAID)
Mallakar *SADI-SAKHNA*
09035784150
Bismillahir-rahmanir-raheem
Ki biya kan ki karantamin na biyu dan Allah 🙏🏼 ga number ta nan mai son littafi na
ɗaya yayi min magana zan bashi shi kyautane.
Ina ƴan mata dakuma Matan aure masu muradin burge mazajensu da ɗinkuna zuƙa zuƙa.
*PHEEDY TOILORING DESIGN* ,suna gabatar muku da ɗinkuna kala kala wanda sukayi
daidai da zamani.
Zaku samemu a kan wannan layin waya kamar haka
09167130115
Wato a manhajar whatsapp. Domin ganin kalolin samufurin aikinmu kuma ku tuntubemu a
INSTAGRAM da kuma TIKTOK a @pheedyxacks_ragtrade
*BOOK 2*
...6...
"Sumaimah me kikeyi a waje haka,dan kare yana haushi saika biyeshi kayi,ko kin
manta da matsayinki ne"
Kuka na rushe dashi tareda tsugunnawa,dan bansan mai zance mata ba,abin ya tarumin
sosai.
Tsayawa tayi da faɗan tana rarrashina,saida nayi mai isata kafin na kula da Sayyid
wanda yake hannun Deejah yana kuka. Karbarsa nayi na fara bashi abincinsa,da ni
naƙi cin nawa ba kamata shi na hanashi ba.
Sai bayan nagama bashi har yayi bacci kafin na tashi nayi alwala.
"Ya takardar gamawar kin ƙarbo ina?"
Jijjiga kai nayi bansan taya zan fara yimata bayani bama,domin maganar akwai
nauyi..
"Inna basu bani ba,sunce wai saina bada dubu hamsin tukunna,wai shine kudin da suke
bina bashi"
"Bashi bashi kaman yaya,naga yabiyasu kuɗin komai harki gama?"
"Uhm sun sani,kawai yanzu ne suka kawo maganar,ina dawowa kuma na haɗu da waɗancan
suma"
"Hmmm ƙaddarace in muka jure watarana sai labari,bari komai ya lafa saimu samu
abinda zamuyi"
"Inna inason tafiyah babban birni yin aikatau,naji ina kayi dace da gidan masu
hannu da shuni ana samun kuɗi sosai"
Zaro ido inna tayi tana kallona,da alama tayi mamakin furucina.
"A ina kikaji wannan zancen haka?"
"A makarantar islamiyya ne wata take faɗa,wai yanzu hakama wai suna shirin tafiya a
satinnan,magana tayimin akan ko zan tura Deejah,tunda yara ake turawa,shine nace
mata zan duba nagani"
"To mai yasa kikace ke zakije?"
"Inna bazan iya tura Deejah ba,har yanzu bata mallaki hankalinta ba,ina gudun wani
abun ya sameta,sannan bayan hakan nasaka a raina zan sakata tayi karatu kaman yanda
yah Musbahu ya sakani. Na yanke shawarar zuwa aikin,idan da rabo goje ya dawo sai
ku faɗamasa inda nake. Idan na turo kuɗin aikin inna ku dunga amfani dashi,harda
kudin makarantar deejan"
"Naji abinda kikace Sumaimah,irin wannan kyakykyawar niyya da Allah yabaki Allah
yabaki mai yi miki,yasa komai ya wuce sao tarihi,dama akwai wani bayani danace miki
zanmiki,ita tunanin yanda zan farashi,amma tunda kinkawo wannan zancen a ranki ta
kwana gidan sauƙi.
Nayi aiki a garin abuja tsawon shekara talatin,dan haka babu abinda bansani ba
gameda aikin,bama saikin bi waɗancan ba akwai adireshin gidan da zan baki,indai
kikace nina turoki to za'a vaki aiki,kuma a biyaki mai tsoka"
Daɗi ne yakamani jin furucin innan,duk da zuciyata nasan yimata tambayoyi amma haka
nayi shuru.
Tashi tayi ta nufi ƙarƙashin gadonta,da alama wani abun take nema..
Ban ankaraba naji mutum a jikina,ashe Deejah wacce take tsaye tana jin abinda muke
faɗa.
"Nagode anty Sumaimah da karamcinki gareni,bazan taba manta yanda kowa ya gujeni
amma keda yah Musbahu kuka taimakamin,gashi a yanzu kin kasa turani aikatau duk da
halin matsi saboda karna halaka,kin zabi kije akaina"
Kallonta nake da mamakin yanda kalaman hankali suke fita daga bakinta,ashedai tana
sane da abinda yake faruwa,katseni tayi da maganarta..
"Anty da Sayyid zaki tafi"
"Ahah ba dashi zata tafiba,idan ta tafi dashi bazatayi abinda taje yiba,sannan abin
bazai tafi yanda ake so ba"
"Wannan abu kuma inna?"
Na tambaya ta mamaki,ganin yanda take magana kaman an turani wani muhimmin aiki.
"Ohh abu nace? Ina nufin aikin dazaki je yiɗin,anan zaki barshi shima zaifi masa
sauƙi"
"Amma ......inna ban yayeshi ba fah"
"To jimin wani zance,ɗan da tun bashida wayo kike guduwa makaranta ki barshi,ana
mutuwa a bar yaro ma ya rayu ai?"
"Yawwa shikenan anty karki damu ki barmin shi,zan kula dashi tamkar kinanan"
Deejah ta faɗa cikeda farinciki,sauƙe ajiyar zuciya nayi tareda cewa.
"To shikenan khadija na barmiki shi har naje na dawo"
Daga haka ta fita tana murna,ni tausayima ta bani,ganin yanda muke ta faɗi
tashi,idan na tafi zanyi kewarsu sosai.
Wata takarda naji inna ta miƙomin bayan na tafi duniyar nazari,karba nayi na
bude,address na gida a abuja.
"Ga wannan gidan shi zaki nema idan kin isa,inkinje ki samu wata mai aiki inna
ladiyo,kice mata nina aikoki,idan kika faɗi hakan zata baki aiki"
Ɗaga mata kai nayi,na rasama mai zance,gabaɗaya a rayuwata bana kawo cewar wai
zanje neman aikatau wani garin saboda mu samu abinyi.
"Toh inna Inshaallah zanyi hakan,batun kuɗin aikin kuma zan dunga turowa Tunga sai
ya baku"
"Karma ki tayar da hankalinki,a nan ma zan samu wata sana'ar kota ɗan tallene na
lokaci kaɗan na dungayiwa Deejah,nasan kuma daman ba wai aikinne har a ranki
ba,kinasone kiyi nesa da gida saboda abubuwan da suka faru"
Sunkuyar da kaina nayi,gaskiya hadda ma hakan,tunda na rasa mijina gabaɗaya zaman
garin ma ya isheni,tun mutum yana toshe kunnuwansa da maganganu har suyi masa yawa.
Na haɗa kayana a ƙaramar jaka duk abinda nake buƙata,Deejah nake jira ta ƙiramin
mai mashin ya kaini tasha.
Kallon Sayyid nayi wanda yake tsaye da minti a hannunsa,tun shekaranjiya da nasan
ba dashi zan tafi ba na daina bashi nono,dama toh ba dogara yayi gabaɗaya a kai ba.
Amma duk da haka zuciyata saida tayi zafi da barinnasa na shiga duniya,wanda Allah
ne kaɗai yasan ranar dawowa ta.
Jiya naje gidanmu nayi musu sallama,muna zancen da ammi inna rammah tajiyo,dama
halinta ne yin lab'e idan ana zance,kafi kaceme har zance ya gama ko'ina cewar
talauci da baƙin ciki nima zai korani duniya. Wani lokacin abun ma har mamaki yake
bani,shin metasa mutane basa ta kansu saita wani ne?
Ko ma dai menene nidai yau zan barmusu garin.
In cikin hakane naji Deejah ta dawo da gudu.."
"Anty ki fito gashinan na ƙiramiki mai mashin ɗin"
"Ohh har an samu mai mashin ɗin?"
Inna tafaɗa wacce ta fito daga kewaye da buta a hannunta,tayi alwalar walaha..
"Ehh inna nasamo,saida ya ɗanani muka taho tare"
Jakata na ɗauko zan fita daga ɗakin,da sauri Sayyid ya jefar da mintin hannunsa
yana ɗagamin hannu alamar zai bini,wani kukane ya taho min ya tsaya a maƙogarona.
Inna tana ganin haka ta ɗaukeshi tareda goyonsa,dan ma yau bayyi kukan yayeba da
daddare.
Gaba na wuce suna bina a baya zuwa ƙofar gida,har raina banason barinsu,amma kuma
nasan zuciyata tana buƙatar zuwa nesa,koba komai hakan zaisa na manta da wasu
abubuwan.
Musamman yanzu dana gama karatu banida abinyi.
"Sumaimah Allah ya tsare hanya,ki kulada abubuwan dana faɗamiki jiya da
daddare,karki shiga abinda babu ruwanki,amma idan yazamo abu nakine kiyi ƙoƙarin
wajen ganin baki takura kanki kin hana kanki ba,ki zama jaruma ta yanda zaki iya
tsayawa wanda yke naki. Labarin danace zan baki kiyimin uzuri akai,zakiga abinda
zai gigitaki amma kibi komai a sannu. Sannan na miki alƙawarin duk wata tambaya da
take ranki ki adana,da zar kin dawo nikuma zan amsa miki su. Idan na faɗamiki yanzu
zai iya cutar dake,dan haka ki bi komai a sannu"
Kaina ne ya kulle da maganganun innan,nifa aikatau kawai zanje,shin mai ya haɗani
da waɗannan zantukan kuma?
"Inna shin meyasa kike min irin waɗannan zantukan?"
"Da sannu in kika inda zaki je to zaki gane,kije maza Allah ya tsare ya baki
NASARA"
Ɗaga mata kai nayi tareda yiwa Deejah da Sayyid kallon ƙarshe kana na ɗale bayan
mashin ɗin.
Ina kallon gaji ta fito daga gidan bayan mashin ɗin ya tashi. Nasan ba komai bane
banda gulma.
A raina nace kedai kika sani ni yanzu sai sanda kika ganni. Saida ba kama hanyar
naji kaman na koma nace na fasa,dan ji nake kaman wani abun zai faru. Amma ya zanyi
alƙalami ya riga ya bushe.
SADI-SAKHNA CEH
09035784150
ku tuntubeni domin biyan kuɗinku ko ƙarin bayani.
*SANADIN CACA*
-BOOK 2 (PAID)
Mallakar *SADI-SAKHNA*
09035784150
Bismillahir-rahmanir-raheem
Ki biya kan ki karantamin na biyu dan Allah 🙏🏼 ga number ta nan mai son littafi na
ɗaya yayi min magana zan bashi shi kyautane.
Ina ƴan mata dakuma Matan aure masu muradin burge mazajensu da ɗinkuna zuƙa zuƙa.
*PHEEDY TOILORING DESIGN* ,suna gabatar muku da ɗinkuna kala kala wanda sukayi
daidai da zamani.
Zaku samemu a kan wannan layin waya kamar haka
09167130115
Wato a manhajar whatsapp. Domin ganin kalolin samufurin aikinmu kuma ku tuntubemu a
INSTAGRAM da kuma TIKTOK a @pheedyxacks_ragtrade
*SANADIN CACA*
-BOOK 2 (PAID)
Mallakar *SADI-SAKHNA*
09035784150
Bismillahir-rahmanir-raheem
Ki biya kan ki karantamin na biyu dan Allah 🙏🏼 ga number ta nan mai son littafi na
ɗaya yayi min magana zan bashi shi kyautane.
Ina ƴan mata dakuma Matan aure masu muradin burge mazajensu da ɗinkuna zuƙa zuƙa.
*PHEEDY TOILORING DESIGN* ,suna gabatar muku da ɗinkuna kala kala wanda sukayi
daidai da zamani.
Zaku samemu a kan wannan layin waya kamar haka
09167130115
Wato a manhajar whatsapp. Domin ganin kalolin samufurin aikinmu kuma ku tuntubemu a
INSTAGRAM da kuma TIKTOK a @pheedyxacks_ragtrade
____∆∆∆____
Ya yage takardu sunfi guda biyar yana zubarwa,kansa ya kulle ya rasa ma mai zayyi.
Kansa ya riƙe tareda jan gwauron numfashi.
Kwanansa uku kenan da zuwa office amma yagagara yin komai kaman nada,abubuwa da
dama sun canja ciki harda tsarin wajen,abun yana cin zuciyarsa ganin duk yanda
yakeson aikinsa ya tafi a gaggawa amma abu ya gagara. Duk ƙoƙarin daya dungayi a
baya ya tara shaidu duk sun tafi kaman anyi ruwa an ɗauke.
Kansa ya ɗora a kan kujerar yana jinata a hankali idonsa ya rufe.
Yaji alamar buɗe ƙofa wani ya shigo,tun kafin ya bude ido yace.
"Eemran mai Abbah yace,ya bamu izinin binciken wanann gidan?"
"Am sorry sir amma har yanzu ya ƙi saka hannu,a cewarsa wai bai kamata ka fara
babban aiki irin wannan ba daga dawowarka"
"Hmmm kaida Neelah ku fara aiki cikin sirri,bazan iya tsayawa da aikinnan ba"
"Amma yallabai akwai hatsari muyi batareda sanin sama ba"
"Hatsari ya wuce wanda nake ciki,kullum hankalina a tashe yake da tunanin a kowanne
irin sakanni za'a iya sake farautar rayuwata ba, shin akwai abinda yafi haka
hatsari Eemran?"
Duk yanda yake boye damuwarsa tun bayan dawowar tasa,amma kana kallonsa zaka san
baƙaramin dauriya yake ba.
"Hakane kam ogah lamarin abin abun a dubane,nida Neelah Inshaallah zamu iya
ƙoƙarinmu wajen ganin komai bai sake zuwa da matsala ba.
Wanda suke aikata waɗannan abubuwan da sannu zasu zo hannu.
Hular sa ya ɗauka ya ɗora akan kayan uniform ɗinnasa,wanda suka sake fito da
jarumtarsa a fili.
Yau baizo da drivernnasa ba wai mai ɗakinsa ta haihu,dan haka da kansa ya tuƙo bai
ɗauki wani drivern ba,domin dukkansu ba yarda yayi dasu ba,yasan duk yaran hajiyah
maryam ne.
Buɗe motar yayi zai shiga,tsayawa da shiga motar yayi sanadiyyar wani akwati daya
gani a wajen zaman drivern..
Kaishi yayi ɗayan sit ɗin,sai bayan ya zauna kafin ya ɗauko shi ya buɗe..
B'era ne matacce a ciki sai wata wasiƙa da jan ink.
.........kayi hankali da rayuwarka yaro,baka san mai kake shirin tonowa ba,hakan
bazai ta'ba kyau ba,domin sakamakon dazaka gani bazai ɗauki ƙwalƙwalrwar ka ba.
Hmmm wato warning ɗin a aka baka a baya bai isheka ba saika sake aikata wani
kuskuren?.......
Ninke ta kardar yayi tareda sakata a aljihunsa,yayinda bandir ɗin kuma ya jefashi
ta windown motar,ƴar ƙaramar tsuka yaka yana cije ƙasan bakinsa,ganin bata lokacin
zayyi yawa yasa yaja motarsa zuwa gida. Wanda baya ganinsa a matsayin gidan kaman
yanda wasu ke gani,dan ɗaukar wajen yake tamkar inda duk jagayen dakayi zaka dawo
ka kwana da makashinka a ciki..
A hankali yake jan motar yana bin karatun dayake tashi a cikin motar har ya isa
gida..
Bai samu kowa a babban falon gidan ba,wanda daman hakan yakeso,in badan Abbah ya
hanashi yin amfani da ƙofar bayansa ba da babu wanda zai dunga ganinsa ma saita
kama dole.
Buɗe ƙofar shiga sashennasa yayi ya shiga,an sanja masa ajiyar fulawar da take kusa
da window,wanda daman yana zuci zucin ya kaita kusada rana ya manta..
Sannan an goge ko ina a falon ƙal ƙal sai ɗaukar ido yakeyi,duk da yanda yaɗebo
gajiya da tashin hankali amma gyaan ya burgeshi matuƙa.
Ɗakinnasa ya nufah da hularsa a hannu.
Jefata yayi akan gado,wanda aka sanja zanin gadon ba na ɗazu bane akai.
Rigar jikinsa ya cire harda singlet ɗin,domin dama ya saba duk lokacin daya dawo
sai yayi wanka tukunna ya wanke gajiyar jikinsa.
Bai shiga banɗakin ba tukunna sai ya tsaya yana aikinnasa na kullum wato tunani.
.........
Tunda naji batun biyana 20k a wata wani ƙaimi na nayin aiki yanda ya dace ya
tashimin.
Bin inna ladiyo na dungayi akan tafaɗamin yanda aikin yake.
Anan nakejin wanda zanyi wa aikin shine ɗa na fari a gidan,mahaifiyar sa bata
nan,sannan ance ya mutu a hatsarin mota tsawon shekaru,sai yanzu ya dawo.
Ba wannan na maida hankali akai ba saina halayensa da aka sanar dani.
Bayason mutane sosai, dan haka duk wacce zatayi masa aiki to fah ta tabbatar ta
gama komai kafin ya dawo,kar ta bari su dunga haɗuwa itada shi a sashennasa,bayason
yayi magana ayi banza dashi kokuma a bashi amsa da kai,ki tabbatar komai yasakaki
zakiyi da jiki,kuma karki bar ko ina da ƙazanta. Karki yi zaton ganin sakin fuska
daga gareshi,kokuma a matsayinki na mai aiki mai jini a jika kiyi tunanin zakija
hankalin sa,domin dan dole yake bari mai aikin ta yi masa hidima,saboda bai yarda
da ƴan gidannan ba kaff,itama mai aikin koya ya kamata da wani abun da bayaso a
ranar zai koreta"
Lokacin danaji waɗannan bayanan harda wanda suka fisu saida na cika da matuƙar
mamaki,shin shi wannan wanne irin mutum ne haka.
Da sauri na ɗebi abubuwan aiki na nufi sashennasa,cikin sauri sauri na gama
ayyukan,domin gaba ɗayansu banga abin wahala ba.
Yanzu ma na gama kowanne sai banɗaki,shima na kammalashi,saida na duba naga na saka
komai har turaren banɗaki da komai da komai kafin na buɗe ƙofar na fito.
Mutum na gani a tsakiyar ɗakin ya juya bayansa,hannunsa a cikin sumarsa yana
yamutsawa.
Ko ba a faɗaminba nasan shine,ƙoƙarin kawar da idona nake tareda yin istigfari a
zuciyata,ganin ina matar aure na tsura wani namijin ido,hakan ma wanda ba
muharramina ba. Lokacin danaji yin aiki a sashen wani namiji naji wani iri,amma da
akace bazan haɗu dashi ba sainaji dama dama,gashi daga farawa yau har mun haɗu. Kai
dole nayiwa inna ladiyo magana akai.
Sunkuyar da kaina nayi ina kallon ƙasa,ganin ya juyo yana kallona,ko ban ganiba
nasan yana mamakin mai ya kawoni ne.
"Wacece ke,mai kike a ɗakina"
Muryarce tayimin kamada wacce nasani,ohh no banason tuno shi a yanzu ba yanzu ba
please.
"Ba magana nake yimiki ba,meyasa bazaki kalleni ki amsa min ba?"
Gabanane ya fara dukan miliyan miliyan..
Idona nafara ɗagawa inda yaja birki a daidai kan tabon raunin dayake cikinsa da
bangaren dama,wanda yayi sakk dana mutumin da bana fatan yazama irinnasa.
Saurin ɗaga idona nayi na sauƙe akan fuskarsa.
A cikin mintuna kaɗan na daskare a wajen a daidai lokacin da ƙwayar idona ta caku a
cikin nasa idon. Duk da cewar komai nawa ya daina aiki amma kuma saida ƙaramar
ƙwaƙwalwata ta samu damar amsa kuwwar sunansa a cikin kaina.
"Gojeeeeeeeeee"
SADI-SAKHNA CEH
09035784150
ku tuntubeni domin biyan kuɗinku ko ƙarin bayani.
*SANADIN CACA*
-BOOK 2 (PAID)
Mallakar *SADI-SAKHNA*
09035784150
Bismillahir-rahmanir-raheem
Ki biya kan ki karantamin na biyu dan Allah. ga number ta nan mai son littafi na
ɗaya yayi min magana zan bashi shi kyautane.
Ina ƴan mata dakuma Matan aure masu muradin burge mazajensu da ɗinkuna zuƙa zuƙa.
*PHEEDY TOILORING DESIGN* ,suna gabatar muku da ɗinkuna kala kala wanda sukayi
daidai da zamani.
Zaku samemu a kan wannan layin waya kamar haka
09167130115
Wato a manhajar whatsapp. Domin ganin kalolin samufurin aikinmu kuma ku tuntubemu a
INSTAGRAM da kuma TIKTOK a @pheedyxacks_ragtrade
*BOOK 2*
...9...
Ban tashi sallahar asuba ba yau,saboda bana cikin tsarki,dama na gayawa inna ladiyo
kada ta tashe da asubar.
Hasken rana nagani ya shigo da windown ɗakin,kasancewar muna idon inda ranar zata
fito.
Mutstsike idona nayi na tashi.
Brush ɗina na ɗauka da toothpaste na fita waje..
A barandar naga wata fashashshen kasko na ƙasa.
Zaro ido nayi,wai dama abinda ya faru jiya da daddare dagaskene ba mafarki ba?
Ƙafata na ɗago wacce nabuge a garin gudu,ɗan yatsan wajen ya kumbura yayi ja,banji
zafin da yakeyimin ba sai yanzu dana kulada shi. Zatona duk abinda idona ya ganemin
jiya mafarkine bada gaskeba.
Dabas nayi zaman ƴan bori a barandar yayinda na koma baya lokacin danayi arba da
mata guda biyun,wanda suke sanye da riguna ja da baƙa,sun rufe kansu..
To su waye haka,mai yasa suka fito daga cikin gidan suka wuce ta nan,kuma a hakanma
bata get ba ta jikin katanga. Sannan jiyan nayi ta tashin inna ladiyo na faɗa mata
amma shuru kamar gawawwaki haka najisu. To ko gamo nayi da aljanu kai,kai amma
aljanune zasu dunga zancen kowa yayi bacci,mutanene kuma nasan a gidannan suke duk
yanda akayi.
Tashi nayi tareda kakkaɗe jikina na nufi katangar inda naga sun bace taciki.
Daga nesa babu komai a jiki,amma dana isa jikin katangar indai ba idona ƙarya
yakemin ba to naga wata Da'irah (circle),a jikin katangar,anyi wani rubutu rubutu a
wajen da jar kala.
Haka kawai naji gabana yana bugawa da ganin abin.
Kai gaskiya gidannan yanada matuƙar hatsari ba ƙarami bama kuwa,kaman yanda inna
ladiyo tafaɗa dolene sai mutum yayi taka tsantsan Sannan ya riƙe Allah. Anan ina
buƙatar yin aiki da kula da kuma ilimi.
"Inkin gama kallon ƙyauyen a jikin katanga kizo ga abincinki nan inna ladiyo tace
na kawo miki"
"Waiwayowa nayi na kalleta,dan murmushi nayi mata gajere,yanda inna ladiyo tafaɗa
nima na fara ganin hakan,halinta ne wani iri,amma batada mungun nufi koma dai
menene zan bibiyeta nagani.
"Bayan haka kuma mai tace?"
Na ƙwala maganar tunda tafara yin nisa"
"Tace mutum ya shirya yaje aikinsa,idan ba haka ba kuma a koreshi kowa ma ya huta"
Dariya nayi ina jijjiga kai,in haka take to lallai zamuje da ita.
Brush ɗin da banyi ba nayi,kana naje inda abincinnawa yake..
Dankalin turawa ne da ƙwai,tabbbb muma masu aiki shi zamu dunga ci?.
Ɗauka nayi nakai bakina,babu abinda ya faɗomin sai inna Deejah da kuma ɗana,Allah
sarki kome sukaci yanzu oho?.
Hawayene ya zubomin nayi saurin sharewa,ina kewarsu sosai da sosai.
Da sauri sauri na gama komai na fito daga sashennamu.
Kitchen ɗin kai tsaye na nufah da kwanon a hannuna.
Inna ladiyo batanan sai iya ammi kawai tana wanke wanke.
Ajiye mata nayi tareda fara yimata ɗauraya.
"Ummi barka da safiya ya aiki?"
"Kafinna amsamiki barmin aikina kije kiyi naki,kina ɗaukar aikinki da sauƙi amma
yafi na kowa taka tsantsan,idan kika makara ko kuma kika je da wuri duk laifi
zakiyi"
Ban bata amsar maganar ta ba,saima wata tambayar da nayi mata.
"Ina inna ladiyo banganta ba"
"Ta tafi kaiwa hajiya tea ɗinta"
"Uhm ta fita jiya da daddare?"
Kallon ya akayi kika sani tayimin kafin tacigaba da abinda takeyi,kaman bazata bani
amsa ba saikuma tace.
"Wani lokacin dama takan fita da daddare,saida safe ta dawo kokuma ta dawo a daren,
naji ance wai gidan marayu ta buɗe,idan abu ya faru na gaggawa takan fita ko
yaushe"
Uhm gidan marayu koh,wato haka tace kenan,to amma mai kuma take itada wata da
daddare jiya......ohh zargi ba kyau mutum bai tabbatar,amma biri yayi kamada mutum.
Ahmad ne yafaɗomin a rai,anya ba saka a hannunta a tafiyarsa,su suna ganin iyah
hatsarin motane yasakashi manta gida,to amma rashin baccin dayake yi a da fah,da
kuma sai yani inbai abin Allah wadai ba bayajin daɗi.
Nasan indai itace to yanzu ma bazata haƙura ba sam,dole zata sakeyin wani abun. To
amma taya zan taimakeshi wannan karonm. Idan a da ta turashi duniya na haɗu dashi
yanzu zata iya turashi wani wajen daban kokuma ta rabashi da duniyar gabaɗayar.
Tunanin hakan baƙaramin firgici yasakani ba.
"Ke keee Sumaimah lafiyarki ƙalau kuwa,ya naga gabadaya annurin fuskarki ya
sauya,harda kuka fah kikeyi?"
Cikeda mamaki takeyimin tambayar,shin mai zan ce mata,taya zance ƙalau nake koba
ƙalau nake ba. A iya rayuwata a wannan duniyar naga abu da yawa,har yanzu ma ba wai
nagama ganin bane,inda raima saidai nace yanzu nafara gani.
"Ahah babu komai ummi,barina tafi aiki,nasan yanzu kam ai ya fita"
Daga haka nayi hnayar sashennasa da sauri,a jiya haushinsa nakeji ganin ya
mantani,amma yanzu tausayinsa nakeji da ɗamarar taimaka masa da dukkan iyawata.
Tafiya nake tunani fall raina har bansan lokacin dana ci karo da mutum.
Goshina na riƙe lokacin da mukayi gwaren,na manta ma da sashenwa nazo.
"Bayan kallon mutum kaman zaki cinyeshi hadda rashin kallon gabanki ma?"
Ɗaga ido nayi na kalleshi,ya hade girar sama data ƙasa kaman bai taba dariya ba,uhm
nasan irin wannan side ɗin,yayi kyau kuma.
Bangajeni yayi ya wuce,ohh ko gaisheshi banyi ba,gashi kaman jiya yauma na cigaba
da kallonsa,duk laifin zuciyata ce,wai miyasa takemin hakane?.
Ciki na wuce,yau banyi kalle kalle kaman jiya ba, shigowata jiya nazone na niyyar
aiki a biyani,amma yanzu jina ke kaman nazo masa gyaranne a matsayinsa na mijina.
Hhhh saina tuno ɗakinsa lokacin dayake goje,wa zai haɗashi da wannan.?
Falon bayyi datti ba,dan haka sama sama na kaɗeshi na shiga ɗakin.
Nan ma banyi wani aiki sosai ba,iyah gyara zaman kayansa nayi da kuma shirya wasu
takardu tana gani a kan wardrop.
Har zan saka sakasu a cikin drawer idona ya hangomin abinda aka rubuta a jiki.
MISSING NUCLEAR INFORMATION....criminals (BC GANG).
Ajiye sauran takardun nayi na duba iya na hannunnawa,hoton akwatin da goje yakoma
dashi gida bayan sunje wannan satar nagani. BC? Itace kenan sunan kungiyar dayakewa
aiki wancan lokacin,tunda gashi ance su suka sace. Ko saboda itace kai aka yimasa
illa wancan karon,kuma rashin sani yaje ya Jona dasu??
"Tabɗijam wannan cakwakiyar da yawa take,shine yake jan ragamar case ɗin,kuma bayan
yarasa hankalin sa kuma yazama ɗaya daga cikinsu batareda ya sani ba. Gashi ya
manta rayuwar dayayi da goje bare yasan inda suke? To amma akwatin fah,shin na
faɗamasa nasan inda yake kokuma na bari yanzu ba? No no idan nagaya masa bazai
yarda daniba,bayan a yanzu yardarsa shine abinda zanso na fara samu tukunna"
Mayar masa da takardar nayi yanda take na ajiye,ban ɗauke hannuna ba naji an buɗe
kofar da sauri.
Turuss yayi daga bakin ƙofar ganin hannuna akan takardun,da sauri ya ƙariso ya
wafcesu har yana haɗawa da hannuna. Kallon tuhuma yake bina dasu,wanda nasan bazai
wuce na dannaga takardun bane.
"Aiki kikazo yi kokuma yimin bincike"
"Niba bincike nakeyimaka ba,kawai na tattarasu ne ganin sun wargaje a wajen"
Kaman bai yarda da abinda nace badai ya ɗiba yasake fita da sauri.
Kumkumina na riƙe ina kallon bakin ƙofar inda ya fita.
"Ikon Allah dama ko daga goje ma wannan ba ƙaramin murɗaɗɗen mutum bane,uhhh kallom
bai yarda dani ba yakemin"
Dafe goshina nayi kafin nima na fito daga ɗakin,har nazo fita daga sashen saikuma
naga wata ƙofar bayan ɗakunan gidan,nasan bazai wuce kitchen ba. Amma to mai zayyi
da kitchen bayan a kwai a can cikin gidan.
Wata zuciyar dai tacemin to jeki duba mana.
Buɗe ƙofar nayi na shiga,bansan lokacin dana toshe hanci ba saboda ƙurar da take
wajen.
Ga kitchen iya kitchen amma saikace sansanin fatalwu.
Ƙarisa shiga cikin nayi ina duddubawa,babu abinda babu a ciki na kayan amfani,haka
kawai na tsinci kaina dayin murmushi da bansan na menene ba.
Mopa na ɗauko da ruwa,ga aiki na samu.....
Ahmad (POV)......
Tunda na tashi na kasa daina mamakin abinda ya faru jiya,ina cikin aiki da daddare
naji tamkar an lullubamin bargon bacci ƙarfi da yaji.
Ko dai kai duk yanada alaƙa da ban warke ba? No amma shi bayamin haka,saidai na
ɗanji ciwon kai daga baya kuma ya tafi.
Bayan nayi sallahr asuba ban koma ta kan aiki ba,sai kawai na kwanta..
Ƙarar wayata ne ya tasheni,anan naga irin makarar danayi,tara da wasu mintunan duk
ina gida?.
A gurguje na shirya na fito daga ɗakin,hankalina na kan agogon hannuna naji nayi
gware da itah,itace dai wannan yarinyar ta jiyah. Kallona ta cigaba dayi kaman
najiya,duk da tasan na hanata,kuma ba kallon tsoro takemin ba kona shakkah,kallo
takemin kaman wacce ta sanni.
Tun jiya naso na koreta,amma data roƙeni saina tsinci kaina da kasa korar tata,ko
wani abu tayimin kai kafin tazo aikin.
To yanzu kuma komawata ɗakin a wajen takarduna na ganta,mai yakaita wajen su?
Yawancin masu aikin gidannan basu iya karatu ba,amma kuma ita batayimin kamada ƴar
kyauye wacce batayi karatu ba.
Inda bincike takeyimin da zata tsorita da ganina,amma maimakon haka saima yimin
kallon na cika ƙorafi da tayi.
"Ohhh sauri fah nake zan tafi wajen aiki,meyasa kuma na tsaya a mota ina tunanin da
bashi amfani"
Yau bazan shiga cikin gida ba,idan na dawo na shiga.
Tafiya nake sa sauri na daidai misali,yau banbi da cikin gari ba,hanyar baya na
ɗauka domin nayi,saboda kar cinkoso ya riƙeni.
Daidai zan wuce ta gaban wani hotel,na tsaya ganin wani ƙira ya shigo wayata.
Kaman ance na ɗaga idona,Mulaifah na gani itada wani zasu Fito cikin hotel ɗin.
Kenan anan ta kwana? Mammah kuwa tasani,kai ba lallai tasani ba,nasan wayo
zatayimata takawo uzurin ƙarya da gaskiya ta faɗa.
Kayan jikinta ma na fara kalla,babu ko ɗankwalin a kan ta sai wani gashin doki
kaman ba musulma ba.
Ga wasu riga da wando damammu,shi kansa wanda take tareda shi ɗin bayyi kama da
musulmin ba,in ma shine to ba hanyar daidai yake bi ba.
Aski ne kansa mai irin wani wajen akwai wani wajen babu,ya saka wata sarƙar gwal a
wuyansa.
Sai dariya suke ya wani rungumeta tamkar matarsa,wani ƙululun baƙin cikine ya
turnuƙe a zuciyata.
Hada alaƙa danayi da itah shine ya sakani jin haushinta,babban wani abin takaicin
ma wai hakan takeso na jata cikin rayuwata. Koda batada irin wadannan abubuwan ma
ita ba tsarina bace ballantana kuma yanzu.
Ina kallonsu suka shiga mota,saida suka bace kafin naja tsaki nima naja tawa motar.
Ni inaga cikin barrack ma zan koma da zama,bansan yanzu ko Abbah zai barni ba.
Fitowa nayi daga motar bayan nayi parcking,office ɗin Abbah na nufah.
Nazo shiga office ɗin kenan naji kamar muryar Sameer yana magana da Abbah.
"Abbah wlh dagaske nake maka,duk da cewa darene amma fa ni kamar shinagani a cikin
waɗannan mutanen,shima naga ya tsaya yana kallona da mamaki. Shi yafara ciremin
hula kafin nima nacire masa,zanyi masa magana kenan naji an ƙwaɗamin ƙasan bindiga
a kaina,har na jimasa ciwo ma a gefen cikinsa na dama"
"Ya isheni wannan zancen Sameer,kai kanka kasan wannan ba abune da hankali zai
ɗauka ba,ɗan uwanka bazai taba aikata abu irin wannan ba"
"Nasani Abbah shiyasa abin yabani mamaki,amma wlh....."
"Ya isa haka kaje zanyi bincike akai,koma ya ake ciki duk zakaji,shin kungama
abinda kukene naga ka dawo jiya da daddare?"
"Ahah bamu gama ba,jirgin yau da yamma zanbi na koma"
"To kaje Allah ya taimaka"
Ina nan tsaye a bakin ƙofar kamar gunki naga Sameer ya fito daga office ɗin,kallon
rashin yarda yayimin kafin ya raba ta gefena ya wuce.
Zancena suke,kaddai zancen Sameer gaskiya ne kai, ciwon dana tashi na gani a gefen
cikina na dama na shafa,kasancewar rauni ne mai girma tabonsa babbane.
Kaina ne naji yana juyamin,hakan yasa na fasa shiga office din na nufi nawa kawai.
SADI-SAKHNA CEH
09035784150
ku tuntubeni domin biyan kuɗinku ko ƙarin bayani.
*SANADIN CACA*
-BOOK 2 (PAID)
Mallakar *SADI-SAKHNA*
09035784150
Bismillahir-rahmanir-raheem
Ki biya kan ki karantamin na biyu dan Allah. ga number ta nan mai son littafi na
ɗaya yayi min magana zan bashi shi kyautane.
Ina ƴan mata dakuma Matan aure masu muradin burge mazajensu da ɗinkuna zuƙa zuƙa.
*PHEEDY TOILORING DESIGN* ,suna gabatar muku da ɗinkuna kala kala wanda sukayi
daidai da zamani.
Zaku samemu a kan wannan layin waya kamar haka
09167130115
Wato a manhajar whatsapp. Domin ganin kalolin samufurin aikinmu kuma ku tuntubemu a
INSTAGRAM da kuma TIKTOK a @pheedyxacks_ragtrade
*BOOK 2*
...10...
"Wayyo bayana"
Na faɗa ina kama kunkumi,gaskiya na dade banyi aiki mai yawa irin wannan ba.
Mopar na ɗauka da bokitin ruwan dattin na fita dasu. Dawowa nayi ina kallon
gyaran,gaskiya ya burgeni sosai,kalar kitchen ɗin ya fito sosai kaman ba shiba.
Saidai ba girki za'ayi a cikiba,dan babu kayan abinci ma a ciki,na faɗan ina
sunkuyar da kai.
Hanyar sashenmu na nufa nayi domin na tsaftace jikina,ga ƙura ga kuma dama ina son
yin wankan..
Rana tayi a lokacin,dan har an fara kiran sallah a wasu masallatan na anguwa.
Hanyar cikin gidan na nufah,anan na haɗu da wannan wacce taje sashen Ahmad jiya.
Motarta ta buɗe ta fito,hannunta ɗauke da key ɗin mota tana kakkaɗawa..
Murmushi take da alama tana cikin yanayi mai kyau kenan,bata kuladani ba tashige
cikin gidan. Nima yafimin,dan tun haɗuwar da mukayi jiya haka kawai naji bana
sonta.
"Sumaimah ina kika shigane,daga zuwa gyaran sashe ɗaya sai yanzu kika dawo? Kizo to
inna ladiyo tana nemanki,an ƙara miki aikin sashen hajiya maryam,mai aikinta bata
nan ta tafi gida anyi mata rasuwa,kuma naji ana cewa wai aure zatayi"
"Kai aure kuma,yanzu shikenan aikina ya ƙaru?"
"Ohh da kinace a iya gyaran waccan wajen za'a baki dubu ashirin,nida kika ganni nan
bayan wanke wanke ina gyaran sashen ƴan biyun gidan"
"Suwaye kuma ƴan biyu ohh sorry ashe inna ladiyo tafaɗamin yanda gidan yake da
mutanen,wacce tashigo yanzu itace Mulaifah koh?"
Naƙarisa maganar a hankali kar a jiyoni.
"Ehh itace kinga ni inada aikinyi ba surutu ba,maza kije ki kai mata abinci,babban
falo ma yana cikin sashenta,ke zaki dunga kulada shi keda Kultum"
"Wacece kuma Kultum?"
"Inkin fara aikin zaki santa ai,tana aikin kulada kaiwa abinci da kuma gyara sashen
hajiya Mammah"
Wai da alama fah saina maida hankali,naga alamar bansan abubuwan gidan ba sosai,ta
wani bangaren kuma naji daɗin yin aiki a sashen hajiyah maryam koba komai zan gano
wacece ita..
Falon nata na shiga,babu kowa sai wata mata tana rubutu a system ɗin gabanta,farace
kamar mamar tasu,tasa ƙaramin glass a fuskarta,ko ba'a fadaba nasan itace
Maimuna,don Fatee itace ƙaramace ba kaman wannan ba,shekarar ƙarshe take a jami'a.
"Barka da rana hajiyah"
Nafaɗa ina rusunawa,ɗagowa tayi ta kalleni tareda yimin murmushi.
"Yawwa barka,amma kidaina cemin wannan hajiyar,anty Maimuna ma ya isa,kece wacce
zata ƙarbi Amina kenan?"
Duk da bansan wa take nufi ba amma nasan wacce ta tafi take nufi.
"Eh nice"
"Ayya ki fara aikinki kawai,karki damu dani,amma ki fara da gyara ciki tukunna"
To nace tareda shigewa ciki,nazo buɗe ƙofar kenan naji ana magana sama sama.
"Hmmm kinji wata sabuwa kuma du,wai yanzu abin ya koma kan wa zai aura,aure ma
yanzu bai isa yayi ba,saboda hakan matsala zai jawo. Ni na gaji da wannan abun sam"
Cikin masifah take maganar,mutum bazai gane haushin maganar takeji ko kuma haushin
shi mai yin auren ba.
"Ta mutu mana ni mai ya shafeni dama yarinyar ba sonta nake ba, tunda ya dawo iya
shegenta yafi na da,nakula baya son ita take rawarta take kiɗinta...............har
yanzu babu wani zance ina gameda akwatinnan?
Gwanda ma da bai bayyana ba,dama banason yashiga wannan shugaba na ukun ballantana
kuma hannun ta,to amma a ina kikega yake?........
Uhm mtsw wancan ba? shima so yake ya kawomin ciwon kai........,kedai ki cigaba da
kulada abinda yake,nayi tunanin daya dawo zai bar wannan aikin ya kama wani,amma na
kula taurin kaine dashi,zanyi magana dashi nayi masa gargaɗi idan yaƙi dainawa kuma
bansan me zanyi ba gaba"
Maganganun sun isheni haka,a da inda zare mai baki kala kala,amma bansan a ina suke
ba. Yanzu kuma na fara kamo bakin zarurrukan. Babu makawa dasaka hannun hajiyah
maryam a dukkan komai dayake faruwa,harma da waccar ƙungiyar duk da saka hannunta a
ciki.
A zuciye na tura ƙofar na shiga ɗakin,na manta ma da cewar itace fah mai juya
komai.
Juyowa tayi ta sauri tana kallona,nayi saurin sauƙar da kaina ina rarraba ido.
"Ke kuma fah daga ina?"
"Uhm nice sabuwar mai aikin nan sashen"
"Ohh kuma shine kikayimin wannan shigowar tamkar an koroki"
"Kiyi haƙuri hajiyah,uhm barina farada banɗaki"
Cikeda tsoro da roƙon Allah yasa kada tace komai nayi hanyar banɗaki da sauri,saida
naga na shige na maida ƙyauren kafin naja ajiyar zuciya,wayyo ni Sumaimah nakawo
kaina ga hallaka.
Bayan nagama gyaran na fito kenan daga ɗakin naga wata tashigo falon da sauri tana
kuka kaman anyi mata mutuwa.
"Mommy mommy wayyo mommy"
Da ƙarfi take maganar,anty Maimuna tunda ta daga ido ta kalleta tacigaba da abinda
take,da alama kenan ta saba hakan.
Hajiya maryam ce ta fito daga ɗakin tana kallon Fatee.
Tana ganinta kuwa da sauri tazo ta rungumeta tareda ƙara sautin kukanta.
Nidai gefe na koma ina kallon ikon Allah.
"Yau kuma meya faru,ke wai bakya girmane uhm kullum kina cikin rigima?"
"Ba.....bba carry over HOD ɗin mu ya bani ba wai....kuma yana sane fah wannan ce
shakarata ta ƙarshe,naje barrack kuma na faɗawa Abbah yace wai dole saina jira wata
shekarar na gyarata,nasan da Mulaifah ce ai da yayi magana an barta ta wuce
yiiiiihhhihiiiiii"
Kuka take tsakaninta da Allah har ranta.
"Hmmm wlh mommy karki yarda da zancenta,tana sane fah da za'ayi exam ɗin amma tayi
baccinta a gida,saboda ta saba Abbah yana magana a bata ta gyara,kuma dama tun
wancan lokacin Abbah yace inta sake yin sakaci irin wannan bazai sake zuwa ba"
"Mommy karki yarda da itah wlh ba haka bane,ranar fah cikina ne yake ciwo"
"Yanzu dai duk ba wannan ba wanene HOD ɗinna ku?"
"Alh sama'ila ne"
Jeki ɗakinki ki huta kici abinci zanyi masa magana,yasaka miki gyarannata a first
semester da za'a shiga"
"Mommmmmyyyyy........"
"Ya isa haka karki dameni,tunda bakiyi ta ba dole saikin gyara,karkuma ki dameni ki
barni da abinda yake gabana"
Dariya anty Maimuna tafara yiwa Fatee wacce tacika kaman zata fashe,da tayi zaton
intayi kukan basai ta gyaraba,amma tasan tunda mommy tace zata gyara to sai ta
gyara ɗin.
"Ke kuma zan fita idan anjima,zan duba miki shari'ar ko kin gano kanta"
"Ahah mommy a dubamin,har yanzu bangano yanda zan bi da itaba"
Gwaliyo tayiwa Fatee lokacin da hajiyah maryam taje kusada ita tana duba abinda
yake cikin system ɗinnata.
Ohhh inda ranka kasha kallo,sudai wannan familyn basa zama waje ɗaya kenan suyi
shuru.
Ɗakinmu na nufa,ina shiga naji wayata tana ringing,dama jiya nayita ƙiran number
Tunga amma bata shiga,ina dubawa kuwa naga shine yake ƙirana..
Da sauri na ɗaga tareda yin sallama..
"Hello Tunga ina ka shiga baka ɗaga waya?"
"Kiyi hakuri Sumaimah wlh munje sarin dankaline wani lungu jiyan,to basuda network
wajen,ga innan dama tunda naga ƙiranki nasan su kike nema"
"Yawwa "
Muryar inna Mairo naji,bansan lokacin dana saki wani ajiyayyen murmushi ba.
"Innaaaa ina wuni ya gidan kuna nan ƙalau"
"Lafiya kalau ƴar nan ya wajen aikin,muna nan ƙalau ƙalau,gamunan ma Tunga ya kawo
mana dankali mun dafa muna ci"
"Inna dama kin sani?"
"Nasan me?"
"Goje uhm......."
"Sumaimah ki bar zancennan,nasani amma babu abinda zan iya cemiki a yanzu saidai
kiyi haƙuri da rufemiki danayi nasakaki a cikin duhu,amma babu yanda zanyi sai
hakan"
"Bakomai inna nasan bazakiyi abinda zai cutar dani ba,amma abinkam akwai ɗaure kai
sosai,kici gaba dayimin addu'a toh."
"Da yardar Allah kuwa,hakan ba zai gagaraba,nasan kinga abubuwa da dama a rayuwarki
na jarabawa,kuma kuma jure kikayi haƙuri,yanzu ma ki ƙara komai zai wuce nan kusa
da yardar Allah."
"Ina khadija da Sayyid banjisu ba?"
Na ɗauko wani zancenne saboda kawar da wancan,a tunani na babu amfani naci gaba da
faɗamata,tunda nasan hakan ba wani amfani zayyi sosai ba,saima na ƙara tada mata da
hankali. A yanda naga abubuwan suke gudana na tabbatar ba laifinta bane na boyemin
da tayi,hasalima tayine saboda hakanne kaɗai zabinta.
"Gasunan fah suna jinki,khadija ce ma yanzu tafita kaiwa su gaji ɗaukin dankali"
"Ayyah nayi kewarku sosai,Sayyid ya daina kukan?"
"Hhhhhh ya daina mana,kijimin saikace dama ba tafiya kike makaranta ki barshi a
gidaba,ya daina kuka yakama abincinsa"
"Shikenan sai anjima inna karna cinye masa katin waya,kucigaba da sakamu a addu'a"
Daga haka nayi sallama dasu na kashe wayar.
.........
Ahmad (POV)
Tun maganar danaji Sameer ya ambata har yanzu bayan na dawo office din ma na gagara
aikata komai,gabaɗaya jin ƙwaƙwalwata nake a dagule.
Duk da cewar maganar tasa batada wani ma'ana zai iya yiyuwa wani yagani mai kamada
ni,kuma dama gashi lokacin darene,amma nagagara barin zancen ya subuce a cikin
kaina..
Abin ya faru a abuja ne,sannan kumadu a abuja na tashi na tsinci kaina. Kai ina
dole sai nayi binciken wannan maganar,idan kuwa da gaske a tsawon wannan lokacin
nayi aiki dasu,to ina buƙatar wannan memoryn,domin hakan zai bani sauƙin wajen gano
inda suke.
Waya na ɗauka na ƙira Eemran akan maganar.
Bayan kaman minti talatin a zaune suke amma nagagara ce musu komai,suma kuma basuce
dani ƙala ba.
Sai can bayan na gama yamutsa gashin kan kafin na ɗago na kallesu.
"Eemran da Neelah akwai wani aiki danake so na baku,please ya shafi aikinmu amma
yafi shafar rayuwata,dan haka ban yarda kowa yaji ba harsai na gado ainihin mai
yake faruwa tukunna.
"Shekara biyu baya na tashi na ganni a asibitin WUSE dake garinnan,inason ku
samomin information na su waye suka kaini asibitin?"
Kallon juna suka farayi da alama tambayar tawa ta basu mamaki,tsawon wanna lokacin
dana tashi,banama so a ɗago min zancen nayi rayuwa biyar bansani ba,amma yanzu
inaso nagano a ina nake"
"Yallabai amma a baya idan akayi zancen bakaso,meyasa yanzu kuma lokaci
ɗaya.......?"
Neelah ce tayi tambayar amma bata ƙarisa ba,saboda tansan nagane mai take nufi..
"Buƙatar hakance ta taso,har yanzunma bawai na damu nasani ɗin bane,amma tunda har
yaci karo da wannan aikin to vanida zabi. Please ku bincika sosai,inta kama ku nuna
musu hotona ma,saboda ba lallaine da sunana nake amfani ba a da ɗin"
"To shikenan zamu iya ƙoƙarinmu akan case ɗin"
"Ogah zakaci abinci ne nayi order dakai"
Saida yayi zancen abinci ma na tuna rabona dashi tun jiya da daddare.
"Sure"
"Eh gaskiya kam gwanda ka dunka cin abinci,aiki ciki bai ɗauka bama baya tafiyah
daidai"
Cikeda zolaya yayi maganar kafin suka fita a tare,hmmm na koma tsohon aikinnawa
wato tunani.
SADI-SAKHNA CEH
09035784150
ku tuntubeni domin biyan kuɗinku ko ƙarin bayani.
*SANADIN CACA*
-BOOK 2 (PAID)
Mallakar *SADI-SAKHNA*
09035784150
Bismillahir-rahmanir-raheem
Ki biya kan ki karantamin na biyu dan Allah. ga number ta nan mai son littafi na
ɗaya yayi min magana zan bashi shi kyautane.
Sister's duk wacce batayi anfani da sabulun mg's ba ko kit dinsu inamai shaidamuku
anbarku acan baya domin duk wnd yajaraba mg's sai sanbarka duk wani Mai tantama
Akan kayan gyaranjiki toh tabbas yacire sabulun mg's domin yahadu bakarya
zegyarajiki yafidda dattin fata Dama duk wani matsalan fata duk Wanda kefama da
matsalan fata walau pimples ko spot, sunburn acne,stretch mark dama dukkan wani
prblm yajaraba mg's bi'iznillah komai zaizama labari bayan jikinku yy fresh zaisa
jikinku yy smooth yadinga glowing,gawanda basa San anfani da Mai zaku iya using
😯 wnn new soap din💣ne,😯 bama cika Baki kujaraba
mg's batare da kunbukaci wani Mai bnd
kugane ma idanku domin ance gani yakoriji Kuma siyan daya maida kudi gida
You can check pic👇for the soap reviews🥰
Soap price:4k
maiso yy mgn
08062991549
07046881166
07067210195
Call 08064532391
Instagram:glow_with_mgs
Facebook: mg's skincare
Munatura Kaya kowani gari dayardar Allah Amma delivery is not free
*BOOK 2*
...11...
.......
Neelah ce ta kalli hajiyah Maryam wacce suke zaune a cikin mota suna kallon videon
Sumaimah tana bincike ɗakin hajiya maryam.
Tun daga shigowarta ɗakin har zuwa fitarta duk suna kallonta, a cikin videon da
camera take ɗauka.
Sai bayan sun gama kafin Neelah ta kashe tana kallon hajiyah maryam.
"Kingani koh? dama saida na faɗamiki jiya ta ganmu kika ce bata ganmu,kina kallonta
kaman batasan mai take ba,amma itama ta wuce yanda kike zaton,wannan takardun na
jiya take nema"
Hajiya Maryam ce tayi maganar cikin wani murmushi na gefen baki.
Cikeda mamaki Neelah tasake kallonta a videon kafin tace.
"To ita kuma mai nata nayin wannan binciken,batasan ma takardun menene ba,idan ma
tasani mai zatayi dasu,tana bayan Ahmad ne?"
"Ohh tambaya ma kike bayan kinsan komai,uhhhh hakan da tayi kuma yasa ta
burgeni,batada tsoro da duhun kai,tasan mai takeyi sannan na kula bakaman sauran
ƴan aikin ba tasan mai takeyi,ta wuce yanda nayi zatonta ma"
"Hajiyah shikenan haka zamu barta bazamu tsayar da itah ba"
Jijjiga kai tayi tareda yin dariya.
"Batta tayi bincikenta,tana da damar yin hakan,karki hanata saima ki bata satar
amsar hanya,duk abinda ta gano zanga shin zata iya ɗauka kokuma zata kasa,duk hakan
yana cikin gwajinta kafin takai irin macen da nake so. Ko ajiyeni a wajen aiki ki
wuce,kwanannan banason yaran sojojincan sun faye caja kai.....Daga can kije ki
faɗamasa abinda na gaya miki na binciken dayace kuyi masa,karki yarda ki bari ku
ƙara daga haka"
"An gama hajiyah zamuyi yadda kika ce"
Jan motar tayi zuwa inda hajiya Maryam take aiki,wani babban wajene ya haɗa komai
da komai na taimakon talakawa da marayu,kama daga sana'a harma da koyarwa.
"Ki bari basai kin rakani ba san tafi,ki cewa samuel yazo da motata ya ɗaukeni in
anjima"
"To"
Fita tayi daga cikin motar tashiga wajen,cikin tafiyar isa da aji take tafiyah har
ta bace,a yanayin shekarunta ba mai cewa zata iya tafiya da irin wannan takalmin
idan ba gani yayi ba.
Ƙirane ya shigo wayar Neelah wacce take ƙoƙarin tada mota,dakatawa tayi tareda
dagawa.
"Ehh eemran kana inane,yanzunnan zan tafi headquater,kaima kayi sauri saimu haɗu a
can"
Taka motar tayi da gudu domin isa inda zataje akan lokaci.
A tsaye yake a gaban mutumin wanda kamanninsa suka sauya baka gane komai a fuskarsa
saboda wahala da kuma dukan dayasha.
Ɗayane daga cikin ƴan kungiyar BC wanda aka kama shekara biyu baya,duk yadda za'ayi
dashi yayi magana amma yaƙi,da haushi ya ishi masu tambayar sukayi masa lahani
sosai.
Yanzu ma cewa yace a kawo masa shi ko zai iya gane wani abun,duk sun tabbatar masa
da yazama mahaukaci ai da daɗewa,shikaɗai sai yayi ta dariyah yana cizon baki.
Anyi kimanin awa guda kenan Gen Ahmad yana gabansa,amma yaƙi cewa komai.
"Kai ɗago ka kalleni shin ka sanni?"
Amma shuru kaman yana magana da kungi,wani yashigo wajen tareda sara masa,kana
yafara da cewa.
"Gen Neelah da Eemran suna neman izinin shigowa,tun ɗazu suke waje"
"Kace musu su shigo"
Neelah ce tafara shigowa kana Eemran,gaisheshi sukayi kafin Neelah ta miƙa masa
wani file..
"Yallabai ga bayanan da muka samu a asibitin,bayan tsawon bincike bamu samu komai
ba,saida muka duba files na hotunan marasa lafiya har na shekara biyun kafin muka
gano naka."
Tun kafin ta gama bayanin ya buɗe file ɗin yana kallo.
Hotone kawai a jiki sai suna ta sign.
"Gojee???"
Shine abinda Ahmad Ya faɗa cikeda mamaki..
"Miye kuma goje,narasa sunan da zanyi amfani dashi sai goje?"
"Eh goje ƙwarai kuwa goje,shine shugaba ai na yanzu goje baaa"
Mutumin dayake gabansu ne yafara faɗa yana wasa da babyn robar da take hannunsa.
Da sauri Ahmad ya tsugunna a gabansa tareda cewa.
"Eh shi kasanshi?"
"Hhhhhhhh goje bindigar roba ba"
Tsuka yayi ya tashi tareda sake kallon su Neelah.
"Shikenan iya abinda kuka samo,waye to ya kaini asibitin,ƙungiyar BC ce?"
Jijjiga kai Neelah tayi kafin tace.
"A yanda suka faɗa mana kuma kaga wannan saka hannun,sunce matarka ce ta kawoka
asibitin,itace ma take zaune a wajenka har ranar daka tafi. Sannan bayan ka tafi
tasuma suka karbeta a asibitin,har sukayi mata test na juna biyu....bayan sun
sallameta kuma basusan ta da kuma daga inda take,amma sunce jininta ya hau sosai ga
yaron ciki,da ƙyar idan batayi barin sa ba"
Zaro ido Ahmad yayi yana kallon Neelah kamar ya samu madubi,mata da kuma ciki nasa
wai? Abin takaicin kuma bai tuna komai ba? Tabbas daya tashi kam yaga wata mace a
gefen gadonsa a kwance,kaico da bai tasheta ba,yasan da duk baisha wannan wahalar
ba.
"Taya zakuce to babu sunanta da kuma garin da take,wannna ba abune da hankali zai
ɗauka,kuxo muje asibitin ina buƙatar duk wani bayani daya shafeta"
"Am sorry sir,amma mun iya ƙoƙarinmu amma bamu samu komai ba,ƙarshe ma sai suka ce
wai anyi musu kutse waccar shekarar,to a lokacin sun rasa data da yawa na bayanai"
Wani gumi ne ya yanko masa,bai san lokacin daya samu waje ya zauna ba yana dafe
kai,wannan wane irin abune ne haka.
Tashi yayi zai fita,har yaje bakin ƙofa mai kulada wajen yayi masa magana.
"Sir ya zamuyi da wannan mutumin?"
"Zai warkene?"
"Ahah ƙwaƙwalwarsa ta lalace ba lallai va"
"To kuyi duk yanda zakuyi dashi,kai Eemran ran ka rufemin office ɗina bazan koma
ba,gida zan tafi"
A hanyar zuwa motarsa yaji wayarsa tayi ƙara,shareta yayi harta katse,saida aka
sake ƙira kafin ya fito da itah ya duba.
Hajiyah maryam ce take ƙiransa,har bazai ɗaga ba saikuma ya danna ɗauka.
"Har haka na zama a wajenka saikaga dama ka ɗau ƙirana?"
"Shin me kike buƙata?"
"So nake kazo inda nake akwai maganar dazamuyi?"
"Inada........"
"In kanaso kaji sunan matarka da kuma a wanne gari take to kazo inda nake,sannan
kayi abinda nace"
Tana gama faɗin hakan ta kashe wayar,sauƙe wayar yayi a kunnensa tareda runtse
ido,abin bai wani bashi mamaki,domin hakan ba shine farau ba. Yarigada yasan
bashida wani mutum ɗaya daya yarda dashi wanda ba nata bane.
*SANADIN CACA*
-BOOK 2 (PAID)
Mallakar *SADI-SAKHNA*
09035784150
Bismillahir-rahmanir-raheem
Ki biya kan ki karantamin na biyu dan Allah. ga number ta nan mai son littafi na
ɗaya yayi min magana zan bashi shi kyautane.
Sister's duk wacce batayi anfani da sabulun mg's ba ko kit dinsu inamai shaidamuku
anbarku acan baya domin duk wnd yajaraba mg's sai sanbarka duk wani Mai tantama
Akan kayan gyaranjiki toh tabbas yacire sabulun mg's domin yahadu bakarya
zegyarajiki yafidda dattin fata Dama duk wani matsalan fata duk Wanda kefama da
matsalan fata walau pimples ko spot, sunburn acne,stretch mark dama dukkan wani
prblm yajaraba mg's bi'iznillah komai zaizama labari bayan jikinku yy fresh zaisa
jikinku yy smooth yadinga glowing,gawanda basa San anfani da Mai zaku iya using
😯 wnn new soap din💣ne,😯 bama cika Baki kujaraba
mg's batare da kunbukaci wani Mai bnd
kugane ma idanku domin ance gani yakoriji Kuma siyan daya maida kudi gida
You can check pic👇for the soap reviews🥰
Soap price:4k
maiso yy mgn
08062991549
07046881166
07067210195
Call 08064532391
Instagram:glow_with_mgs
Facebook: mg's skincare
Munatura Kaya kowani gari dayardar Allah Amma delivery is not free
*BOOK 2*
...12...
"Okay let's go to the deal,(Aha bari muje yarjejeniyah),zan faɗamaka wacece
matarka,sannna kuma a ina take,amma da sharaɗin saika daina binciken da kakeyi a
yanzu na ƙungiyar BC,duk cewar nasan idan na kacigaban babu abinda zaka samo saidai
ka sake saka rayuwar a halaka karo na biyu.
Dan haka ka ajiye case ɗinnan ka kama wani daban,idan kayi hakan ka tsira kuma zaka
san inda matarka take"
Wani kallon kinsan mai kike fada Ahmad yayiwa hajiyah maryam,saida tagama bayanin
kafin yayi ɗan murmushi.
"Amma da kikayi wannan maganar ke kanki kinsan idan zan yarda da ita kokuma akasin
haka, babu abinda zaisa na daina wannan aikin matuƙar ba kama wanda suke da hannu
da shuni a ciki nayi ba. Batun sanin inda matata take,dama bawai saninnata ne
maƙasudin abinda yasa nake nemanta ba,bazaki san dalilin ba kuma,dan banyi maganar
da kowa ba bare ki sani"
Tashi yayi cikin bacin rai zai fita daga office ɗin,magana tasake yimasa hakan yasa
ya tsaya da fita.
"Bazaka daina ba....koda kuwa na kusada kai zasu cutu akan hakan,koda kuwa abinda
zaka tono ɗin bazai maka daɗi ba?"
"Ban damu da daɗinsa da kuma rashinsa ba,indai zanyi nasara hakan ma kaɗai ya
wadatar"
"Hmmm yaro man kaza,kanada masoya a boye,haka zalika kanada maƙiya ma a boye,abinda
yake zai bayyana maka maƙiyanka amma kuma zai cutar da boyayyun masoyanka,tunda
kace kaji ka gani na amince da zabinka,i like to see you try"
Ƙarisa maganar tayi tana ɗan sosa biro a goshinsa,bayan ya fita ajiyar zuciya tayi
tareda lumshe ido.
"Shin ya zanyi da yaronnan ne ni maryamu,gabaɗaya narasa taya zan juya akalarsa
daga kan abinda yake shirin yi"
Ƙirane ya shigo ta wayar office,hakan yasa ta ɗaga da sauri.
"Halle jikin nasreem ne?"
"Eh ranki ya daɗe,yanzu haka ma ana nemanki da gaggawa"
"Ohk ganinan zuwa"
Tana kashe wayar tafita daga office ɗin da gaggawa,wani corridor ta bi da gudu har
tana tuntube.
Ɗaki na biyar a bangaren hagun ta shiga.
Likitocine guda biyu akanta,da kuma wasu mata masu uniform ruwa kalar omo.
Ɗaya daga cikinsu ce taga shigowar hajiyah maryam ɗin,da sauri ta matsa domin bata
damar kallon yarinyar da take kan katifar.
Cije cije take da fizge fizge,gaba ɗaya bata cikin hayyacinta,fatar bakinta duk
tayi jawur saboda cizonta da take kaman zata cireta.
Ƙarisawa gabanta tayi a hankali daidai lokacin da likitar tayi mata wata allura..
Sauke numfashi tafara tana jan nishi kaman mai alamar fitar rai,can kuma sai tayi
shuru kaman wacce ta mutu,da alama bacci tayi.
"Naga tayi bacci da wuri,kenan yau da sauƙi ba kaman jiyaba da muka kai dare?"
Hajiya Maryam tayi maganar cikin tausayawa,kaman ba itace take izza ba.
"Ehh hajiyah mun samo allurar da tayi daidai da jikinta yanzu,Inshaallah zata samu
sauƙi"
"Mashaallah hakan yayi, aikinku yana kyau,ya dai sauran marasa lafiyan,da fatan
suna samun sauƙi"
"Eh suma da sauƙi,mai siyo maganin ma yanzu zai dawo,jariran har yanzu jikinsu da
zafi"
"Bakomai kada ku damu,kudai kuyi abinda ya dace,duk abinda ake buƙata ba matsala
bace"
Tashi tayi tasake kallon wacce take kwance akan gadon cikeda tausayi.
"Hmmm wanda sukayi raping ɗinki saisun biya ba ɗaukar bashi,babu wanda zai sha idan
yashiga gonata"
Lokacin da tayi maganar ta dawo ainihin kalarta,fita tayi da sauri kanajin takun
takalminta ƙwass ƙwass harta bar wajen. Wani sashen tasake shiga,wanda su kuma duk
yarane a wajen suke wasa.
Suna ganin tashi go suka fara rige rigen isa wajenta,da alama su basa tsoranta
kaman sauran mutanen waje.
..........
Yau banje sashen Ahmad gyara da wuri ba,yayi fadan har ya gaji amma ko a
jikina,dokokinsa indai ba wasu muhimmai ba babu wanda nake bi a ciki.
Tafiya nake ina kalla kalle,nazo daidai wuce na shiga sashensa kenan naji murya dr
Saleem yanamin magana.
"Malam Sumaimah barka da safiyah,ko nace safiya,da naga shabiyu ta kusayi"
"Ahh habadai da saura,ya naganka a gida baka tafi wajen aiki ba"
"Uhm na dawone,abu na ɗauka yanzu zan koma"
Uhm kawai nace fuskata ɗauke da murmushi na wuce,shikam ya fita zakka a gidannnan a
kirki.
Fulawar dana yanka nake murzawa a hannuna harna isa sashen,kaman nawa kai tsaye na
wuce.
Babu wani datti sosai saboda gyaran dayake samu daga gareni,sannan kuma ba zama ake
ba sosai.
Sama sama na gyara ko ina kafin na dawo falon ina kallonsa,kana gani kasan bana
mace bane,ga waje har waje amma fayau babu abubuwan daukar ido a ciki.
Fita nayi lambu na cinko fulawowi wanda suke cikin tukunya na saka a ƙofar inda ya
dace.
Labulayenma sanjasu nayi daga farare zuwa jajaye,irin carpet ɗin falon.
Yaraf na zube a kan kujerar falon ina maida numfashi,nikaina gyaran yayi min kyau
ba kadan ba.
Gumi naji yana yankomin saboda motsa jikin danayi,gashi bangama ba inason saka room
fresh da turaren banɗaki.
Yunƙurawa nayi na tashi na shiga ɗakin.
"Fadi ba'a sakani ba,sai gwanintar da ba godewa nake. Ohh kodayake zan samu lada a
matsayinsa na mijjna.
Bayan na gama komai har zan fito daga banɗakin sainaga yayimin kyau sosai.
Wata zuciyar ce tace nayi wankana kawai a nan basai na tafi ba,uh uhm anya
kuwa.'kiyimana da sashen mijinki ne ba laifi kikayiba.
"Uhm mijin da bai san daniba? Baridai na ɗana naji mai akeji,wannan sabulan daga
gani zasuyi ƙamshi"
Hannuna na miƙa na murɗa wata makunna dannaga ko tana aiki,ban zata ba saiji nayi
ruwa daga saman banɗakin ya yimin wankan rashin shiri daga sama har ƙasa.
Ahhh ajiyar zuciya naja,ina kallon yanda kayana suka jiƙe jaraff.
Wayyo ni wlh ba haka naso ba. Cire kayan nayi na matsesu na shanya a jikin glass
ɗin inda aka zagaye domin wanka.
Ruwa na haɗa mai ɗumi nayi wanka a cikin bahon,ina ciki idona yana kallon sama inda
wasu ƙofofi suke,gabaɗaya bantaba kulada su ba sai yanzu dasukamin wanka.
Bayan na gama fitowa nayi daga cikin bahon,towel ɗinsa da nagani a lanƙaye na
saka,hankalina kwance na fito daga banɗakin ina kallon goge gashina da hannun towel
ɗin,ɗayan kuma na riƙeshi a ƙirjina.
Nama bushe dan tun ɗazu naketa yarfe kayan su samu su bushe,dan ma nasan ba dawowa
zayyi yanzu ba sai an yamma.
Dana shigo ɗakin kaina a sunkuye yake bamma kula da mutun dayake tsaye a dakin ba
yanamin kallo ido buɗe.
Daga ido nayi na kalleshi nace.
"Ohh harka dawo yanzu,banyi zaton zaka dawo da wuri haka ba"
Ganin bai bani amsa ba kuma yana kallon jikina da mamaki yasa na tuna mai yake
jikina saida na kalla,narasa meyasa nakasa tsintar kaina da jin kunuyrsa,kodan
nasaba da ganin a haka dayake a baya?.
"Shin kekuwa mutum ce,kirasa inda zakiyi wanka sai a sashena,hakanma ki saka min
towel,sannan na shigo ko a jikinki cewa ma kike wai nadawo da wuri,babu ko damuwa a
ranki?"
"Am sorry kayi haƙuri,wani waje na murda bayan na gama aiki,shine sai ruwa ya zubo
ya jiƙemin kaya,tun ɗazu nake yarfesu amma basu bushe ba, shine na ari towel
ɗinka,kuma na fito hakanne saboda nasan bazaka dawo yanzu ba"
"Ohh yaushe aka saka min dokar bazan dawo ba sai lokacin da kika dibamin"
"Nibance karka dawo ba"
Wata harara ya zabgamin tareda nuna min ƙofa.
"Zoki fice daga sashennan,dariya yabani ganin yanda yake iya ƙoƙarinsa wajen bai
kalli inda nake ba,nikuma sainaji kaman nayi amfani da hakan.
Jin shuru banzo na wuce ba yasa ya ɗaga ido ya kalleni,kaman mai tsoron kar a
kamashi yana kallona ɗin.
"Ba magana nake miki,wanne wane irin salon karuwanci ne?"
Dumm gabana ya buga yayinda wani ƙululun baƙin ciki ya turnuƙeni,karuwanci ni ya
ƙira da karuwa.
"Karuwanci, nika ƙira da karuwa???"
Hawayene suka cicciko a ido na,yayinda muryata tafara rawa.
"Uhhhh karuwanci....bakaga karuwanci ba ai,bari kaga ainihinsa"
Sakin zanin jikinnawa nayi ya faɗi a ƙasa,wanda kuma akan idonsa,runtse ido yayi
tareda juyawa gefe.
Takawa nake cikin ƙunan rai naje tagabansa zan wuce,dagani sai pant.
Hannuna naji ya damƙo daidai lokacin dana kai hannuna zan buɗe ƙofar ɗakin na fita.
Manta komai ai ba hauka bane,kuma nima ba dutse bace,abubuwan sun fara isa ta haka.
"Ke bakida hankali ina zakije a haka?"
Duk da naji haushin maganar daya yabamin amma ta wata fuskar naji sanyin ganin duk
da bai tunoni ba amma yana kishina..dama kuma abinda nakeso naga yayin kenan bawai
fitar zanyi ba.
"Zan fitane nayi karuwanci wanda kace inayi"
"Mtsww ki koma kisaka kayanki,Idan ma so kike a ace daga wajena kike to hakan
bazayyi aikiba"
Juyowa nayi na kalleshi,wanda yayi saurin ɗauke hannunsa daga damtsena yana ja da
baya.
Har sannan baya kallon inda nake,dama bawai burina kenan ba a yanzun.
"Zan saka towel din amma da saiKa yarda zaka banni na zauna har sai kayana sun
bushe,kokuma ka tambayomin ummi tabani kayana. Inkuma kanada kayan mace toh?"
Bai bani amsa ba sai zuwa inda towel yake da yayi ya ɗakkoshi,dawowa inda nake yayi
ya rufashi a jikina,cikeda bacin rai yake kallona tareda yin magana a kusan
fuskata.
Kisaka kije ki ɗebo kayanki Ga nan dryer kiyi amfani da ita ki busar dasu.
Yana gama faɗin hakan ya fita daga ɗakin.
Juya ido nayi tareda komawa banɗakin na ɗauko kayana.
Atampa ce riga da zani,dayake cotton ce har yanzu a jiƙe suke.
Ɗakkosu nayi na dawo ɗakin na kunna dryer,ni bamma kawo wannan tunanin ba.
Ahmad (POV)
Tunda na fito daga ɗakin yaraff nayi akan kujera,dama ga gajiyar dana ɗebo .
Wai inada mata maybe hadda ɗa,maganar ta dokeni sosai ban taba tsammanin hakan ba.
Ga kuma itama waccar matar abban,shin mai na tarewa matar nan ne a rayuwarta,da im
bata shiga rayuwata ba bata jin daɗi. Idan har da tayi nasara wannan lokacin kam
bazai taba yiyuwa ba,dolene sai na binciko laifukanta a fili ta karbi hukuncinta.
Mtsww tsuka naja da hotunan waccar suka fara walƙiya a cikin kaina,shin kanta ɗaya
kuwa a abinda tayi. Amma alamunta bai nuna tanada tabin hankali ba,gabaɗaya nakasa
gane yanayinta guda ɗaya,wani lokacin taji kunya,wani lokacin tsoro,a wani yanayin
kuma kulawa,yanzu kuma na nunamin rashin tsoro da kunya. Wato ta zefar towel bata
ma ɗaukeni namiji lafiyayyeba,ko a jikinta.
Wani abun mamakin kuma batayi kama da wacce take kasa jikinta a titi,duk da abinda
tayi amma hakan yagaza sakani jin tsanarta,meyasa to mafita ɗaya ce inaga na koreta
kawai.
Buɗe idona nayi a hankali jin ƙarar bude ɗaki.
Tasaka kayannata yanzu,saidai muna hada ido ta tasakar min wani kallo najin
haushi..
To mai laifina a ciki,tayi abin karuwai na faɗa kuma yazaba abin faɗa.
"Kizo ki fita,na koreki kada ki sake dawowa,sannan koda kin roƙeni hakan bazai
amfani ba"
Ga mamakina bata ban haƙuri ba kuwa tayi hanyar waje.
Yunƙurawa nayi zan tashi sai naki cikina yayi zafi kaman an tsinkamin hanji.
Hakan yasakani sakin ƙara mai ɗan karfi.
SADI-SAKHNA CEH
09035784150
ku tuntubeni domin biyan kuɗinku ko ƙarin bayani.
*SANADIN CACA*
-BOOK 2 (PAID)
Mallakar *SADI-SAKHNA*
09035784150
Bismillahir-rahmanir-raheem
Ki biya kan ki karantamin na biyu dan Allah. ga number ta nan mai son littafi na
ɗaya yayi min magana zan bashi shi kyautane.
Sister's duk wacce batayi anfani da sabulun mg's ba ko kit dinsu inamai shaidamuku
anbarku acan baya domin duk wnd yajaraba mg's sai sanbarka duk wani Mai tantama
Akan kayan gyaranjiki toh tabbas yacire sabulun mg's domin yahadu bakarya
zegyarajiki yafidda dattin fata Dama duk wani matsalan fata duk Wanda kefama da
matsalan fata walau pimples ko spot, sunburn acne,stretch mark dama dukkan wani
prblm yajaraba mg's bi'iznillah komai zaizama labari bayan jikinku yy fresh zaisa
jikinku yy smooth yadinga glowing,gawanda basa San anfani da Mai zaku iya using
😯 wnn new soap din💣ne,😯 bama cika Baki kujaraba
mg's batare da kunbukaci wani Mai bnd
kugane ma idanku domin ance gani yakoriji Kuma siyan daya maida kudi gida
You can check pic👇for the soap reviews🥰
Soap price:4k
maiso yy mgn
08062991549
07046881166
07067210195
Call 08064532391
Instagram:glow_with_mgs
Facebook: mg's skincare
Munatura Kaya kowani gari dayardar Allah Amma delivery is not free
Sumaimah (POV)
Hmmmm daman nasan zancen gizo bai wuce na ƙoƙi,banda korar babu abinda ya iya.
Har naje bakin ƙofa zan fita naji ƙararsa,da sauri na dawo tareda nufar inda yake a
kiɗine,duk da inajin haushinsa amma kuma muradin ganin ko lafiya yake shiya rinjayi
zuciyata.
Hannuna na saka ina daga kafaɗarsa,ganin ya sunkuya yana riƙe ciki.
Jijjiga shi nafara ina tambayarsa mai yafaru,amma shuru bai bani amsa ba saima ture
hannuna da yayi.
Ɗagowa yayi idonsa yayi ja ya kalleni.
"Ke miye damuwarki ne,banace ki tafi ba?"
Tsuke fuskata nayi tareda tashi daga kan kujerar,hanyar waje nayi batareda na sake
jiyaba nasan.
(da kallo ya bita cikeda mamakin wai tafiya tayi kuwa,duk da a fili yace ta
tafin,amman wani bangare na zuciyarsa sai yaji kaman ya tsaida itah.)
Tafiya nake a sunkuye,duk ƙara taku danayi jinake kaman nakoma wajennasa,amma kuma
komin naci na ya zanyi,yace baya buƙatata.
Daga idona nayi na hango dr Saleem a lambu,har nayi niyyar sharewa saikuma na sanja
ra'ayi,ko ba komai wani abin ba laifinsa bane nawane,shi baisan ni wacece ba,nikuma
ban sanar dashi ba.
Ƙarisawa nayi inda yake da sauri fuskata ɗauke da damuwa..
"Ahh malama Sumaimah ya na ganki haka cikin bacin rai?"
"Uhm .....uhm daman Yayankane bashida lafiya yanata nishi yana riƙe ciki,na
tambayeshi menene yaƙi faɗamin"
Zaro ido yayi tareda tambayata.
"Ciki kikace ya riƙe?"
"Ehh cikinsa ya riƙe,menene wani abune a cikin nasa?"
"Shin yau kinga yaci abinci?"
"Ahah ni ban taba ganinsa ya ci abinci ba"
"Ohhh shit wai yah Ahmad meyasa yake hakane, maza jeki haɗomasa abinci a cikin gida
yanzunnan,kodayake mtsw ba lallai yaci ba don bayacin abincin gidan. Kinga jeki
ɗakko ruwan zafi haka ko shayine ya sha akwai maganinsa a drawer bari naje . kiyi
sauri"
Tunda ya fara maganar kamar hoto haka nake kallonsa,kenan wani ciwone dashi a
ciki,nikuma na dau abin kaman wasa.
Inason tambayarsa mai yake damunsa,amma dai duk ba yanzu ba.
Cikin gidan na shiga da sauri,kai tsaye kitchen na nufah.
Daidai zan shiga kitchen ɗin naji nayi gware ta mutum,ban tsaya kallon waye ba na
wuce da sauri.
Muryar danaji ta dakamin tsawane yasa na tsaya cak.
"Heyy ke jahilar inace zaki bugeni ki wuce kamar kin buge itace?"
"Am sorry sauri nakene kiyi haƙuri"
"Ina ruwana da saurinki,kiga yanda kika 'batamin jiki a cerelac"
Saida tayi maganar na kulada gaban pink ɗin rigartata yanda ya baci da yellown
abin.
Ohh ƙifta idona nayi,na kwafsa kam.
"Me kike kallo ki dauko mopa ki gyara wajennan,sannan kizo ɗakina ki karbi kayan ki
wanke"
"Okay to ina zuwa"
Nafaɗa zan zuya da sauri zuwa daukar ruwan zafin.
"Ke mikike nufi,ina zaki je"
"Kiyi haƙuri anty Mulaifah kaman yanda na faɗamiki wani abun zanyi da gaggawa,idan
na gama zan zo na gyara"
"Kutt lallai ma yarinyar nan kin rainani"
Hmmm ji saikace tafini,ina jinta tana bambaminta amma nayi cikin kitchen ɗin,komai
zatayi ma daga baya kenan,yanzu mijina yana buƙatata urgent.
Allah ya taimakeni ina zuwa naga inna ladiyo ta ɗora ruwan zafi,diba nayi a wani
jug.
A gurguje na haɗa shayin na zuba a wani flask na ɗau kofi na fita da gudu.
Duk abinda nake inna ladiyo tana kallona amma batace uffahn ba.
Har nazo na wuce ina jiyo masifar Mulaifah wanda har yanzu bata gama ba.
Magana ta ƙarshe danaji shine wai ta koreni a aiki na tattara na tafi.
Lokacin dana isa sashen babu kowa da falo,daki na shiga dannasan suna can.. A
kwance yake akan gado,Saleem kuma yana gefensa.
Yanzun baya nishin amma daga ganin yanayinsa mutum zai tabbatar yana jin jiki.
Sallama nayi da flask ɗin a hannuna,da shi muka haɗa ido,nasan yayi mamakin dawowa
ta bayan ya koreni.
Ɗauke kaina nayi tareda ajiyewa a gaban Saleem.
"Sorry na dade ban dawo ba,mun ɗan samu gwarene da Mulaifah a hanya ya jikinnasa?"
"Uhm to gashinan zuba masa tea ɗin yasha ko yaya ne sai yasha maganin"
To nace tareda zuba tea ɗin a kofi,ya ji madara kuwa da bornvita sai ƙamshi yake.
Saleem na miƙawa kofin ya karba.
"Idan ka gama ina jiranka a lambu,uhm Allah ya sawwaƙe"
Tashi nayi na ɗau kofin na fita,ina kallon Ahmad yana kallona amma na ɗauke kaina.
Wajen dana tunkuɗewa Mulaifah abinta na gyara kafin na nufi sashennata domin na
karbi rigar,duk da cewar naji tace wai saita koreni,amma ai ba ita ta ɗaukeni aiki
ba.
"Yau dama nake niyyar sanarwa Abbah yakamata a ɗago zancen aurenmu da yah
Ahmad,tunda ya huta ai,shekara biyu fah?.......aiki bari kawai za'a sha shagaline
na musamman,wannan maganin an tabbatar min da innayi amfani dashi daidai to abbah
bazai cemin ahah ba,shikuwa Ahmad bana tashi,saboda nasan indai Abbah yace masa ya
aureni aiki ya gama. Kudai ku zuba ido Kuga yadda zata kaya,Gen Ahmad hamma dan
Mulaifah aka yishi"..
Hannun ƙofar na riƙe sosai saboda jirin daya ɗebeni,no wonder ashe shiyasa take ta
masifa data ganni a sashen Ahmad,kuma ko yaushe cikin hantara ta take saboda ina
aiki a sashensa.
Kan ubancan,mutumin da kowa yake gudunsa haka na tunkareshi,na zauna dashi har
yazama mutum. Lokaci daya subucemin nasha wahalar rashinsa,yanzu kuma na sameshi
ina shirin dawo da hankalin sa gareni tace wani nata ne ita kaɗai,hadda wani dan
ita aka yi shi.
Cije bakina nayi dana tuno furucinta na ƙarshe,hmmmm ai kuwa Mulaifah zan nuna miki
wannan furucinnaki ba haka yake ba,in dai harna barmiki Ahmad ke kadai to saidai
bana numfashi,nida Sayyid muna buƙatar sa,we deserve him no matter what.
Sakin handle ɗin nayi zan bar wajen,na fasa ma yi mata wankin rigar.
Har na juya zan tafi naji muryar ta a bayana.
"Ke kuma me kike min a bakin ƙofah?"
"Babu kawai na manta hanya ne"
"Hanya??ba riga kika zo karba ba?"
"Uhmm da itace amma na fasa?"
"Kin fasa?"
"Ehhh"
Na faɗa ina juyawa muna kallon juna,idona cikinnata babu alamar zan sauƙe,zicuyata
ƙuna take da turirin kishi dayake cina,jinake komai ma zanyi a yanzun.
"Ki wanke kayarki kokuma ki bawa masu aikin da suke yin wanki,niba aikina kenan ba"
Ina gama faɗin hakan na juya nabarta a wajen baki buɗe.
Duk abinda muke wata dattijuwa tana kallonmu,inaga itace hajiya Mammah da suke
faɗa,danni bansan ta ba mu taba haɗuwa ba.
Murmushi tayimin lokacin danazo daidai fita daga sashen,kunya ce ta kamani ganin
takama ni a matsayina na ƴar aiki inayiwa jikarta kuma ƴar gida rashin kunya.
Rusunawa nayi tareda gaisheta kaina a ƙasa.
Ba yabo ba fallasa ta amsa min cikin dattako.
Tana sanye da farar riga dakuma lullubi shima fari.
"Sannu yarinya,amma ke baƙuwa ce domin ban saida ki ba"
"Ehh hajiyah satina guda kenan da zuwa"
"Ayyah ya sunan ki toh?"
"Sunana Sumaimah hajiyah"
"Mashaallah Allah ya taimaka toh,karki damu da sabaninku fah da Mulaifah kin
burgeni ma da baki raga mata ba,faɗanta yayi yawa da mutane. Inkin samu lokaci kizo
muyi hira kinji?"
"To shikenan hajiyah ba matsala nagode"
Daga haka na ra'beta na wuce,ina mamakin halinta,inaga to itah su Saleem suka iyo
rashin wulaƙanta mutanen.
A lambu na zauna na tsirawa wani waje ido,inda ruwa yake bi abin sha'awa,a zahiri
mutum zai ɗauka wajen nake kallo,amma a ciki tunanin abinda naji Mulaifah tana faɗa
nakeyi.
Zabura nayi tareda juyawa jin wani abu a jikina,ɗaga ido nayi naga ashe fulawa ya
wullomin kan cinyata.
"Sarkin tunani mai kikeyi haka,ko duk damuwar ubanginnnakine kai?"
"Uhm ya jikinnasa ciwon ya lafah,yasha maganin,tea ɗin fah shima yasha?"
Cikeda zumuɗin son sanin ya yake har ban kulaba na fara zayyano wannan
tambayoyin,sai bayan na gama furtasu danaga yanamin kallon mamaki kafinna juyar
dakai ina wayancewa.
"Shin miyasa kika damu jinyarsa kaman haka,tsakaninku bayamin kamada iya mai aiki
da ubangidanta"
Shuru nayi domin banida amsar dazan bashi a wannan maganar.
Shima ganin ban amsa ba yasa ya sauya maganar.
"Karki damu zai samu sauƙi idan har ya kiyaye. Ya taba samun raunine a cikinsa kuma
da alama ba'a kulada wajen yanda ya kamata ba,makamin da aka soka masa kuma yanada
dadi,duk da an karya ƙarfinsa amma ya tabashi sosai,to sanadiyyar haka yasa hanjin
wajen bashida ƙarfi,dole sai yana cin abinci akan kari kuma marar nauyi
sosai,saboda karya motse dayawa kuma kar ya ɗame da yawa"
"Wajen da yaji ciwo na cikinsa shekara biyu baya kake nufi,haba daman nasan bazai
tsaya iya haka,ace wai ya warke shikenan,ciwon akwai zurfi sosai"
Magana nake nayi zaton a azuciyatane,ashe Saleem ya kafeni da ido cikeda
mamaki,saida na gama yayimin tambaya.
"Ya akayi kikasan ciwon shekara biyu baya ya jishi,kuma yanada zurfi sosai?"
"Uhmm am labarin naji a gidannan,kuma um......na taba ganin tabon a cikinsa"
Runtse ido nayi lokacin dana faɗi hakan,Allah ya taimakeni ma shi mutum ne da baya
bin ƙwaƙwaf.
"To amma taya kake ganin za'a sakashi ya dunga cin abinci akai dan gudun faruwar
haka. Mai zai hana a dungayi masa girki a sashensa tunda bayason na gidannnan"
Murmushi yayi tareda gyaɗa kai.
"Ehh hakan yayi,saidai bana tunanin zai yarda"
"Zai yarda,kawai bai saniba a saka kayan abinci a kitchen ɗin"
"Waye zai dunga girka masa toh,iyah gyaran sashensa ne aikinki,bai kamata ki
ɗaurawa kanki wani abinba daban"
"Karka damu dr,indai har hakan zayyi amfani a shirye nake dayi,yanzu zan iya
ganinsa?"
Ohh Allah yasa yace ehh.
"Ehh to ni bansani ba,tsakaninku,tunda kince zakiyi kimin lissafin komai da komai
da akeda buƙata saiki bani,Inshaallah za'a kawo"
"Nagode sosai"
Daga haka na tashi na tafi,sashenmu na shiga nayi sallah na taba abinci sama
sama,kafin na fito na nufi wajen ogan ƴan tsarin.
Kaina tsaye na shige ɗakinnasa,yana kwance akan gado,daga ganin kwanciyar bacci
yake..
Gaban gadon naje na zauna tareda tsareshi da ido.
Nafi minti goma a haka ina kallonsa ko ƙiftawa banayi,tun ina kallon fuskarsa da
take gabana harna fara hasasho goje nah,mai sona da kuma ƙaunar farincikina,nayi
kewarsa sosai.
"Lafiya kikazo gaba kika kafeni da ido kaman zaki cinyeni,hadda wani kuka kaman
wanda aka ce na mutu?"
Dawowa nayi daga duniyar tunanin ina kallonsa,kama da gangar jiki suka haɗa,amma
wannan sam ba goje nah bane.
Shafa kumatuna nayi sai a sannnan naji ruwan hawayen dayake magana akai.
"Niba kai nake yiwa kuka ba,nasan ai baccin kake ba mutuwa kayi ba,kayi sallah kazo
kaci abinci kasake shan magani"
"Yaushe kika fara bani umarni,wani kekam banace kada ki sake dawowa sashennna ba"
"Ka faɗa amma na dawo,yanzu babu wani zancen kora,domin ba'a matsayin ƴar aikinka
na dawo ba,ƴar aikin mai roƙarka inka koreta to ta tafi,wannan nice amma da
banbanci da wancan"
"Mai kike nufi,ana yiwa mutum aiki dolene,nace na koreki"
"Naji ai ka koreni kuma bance maka ban koruba,in ma na kuɗin aikin daza'a vani
wanda zan taimakawa rayuwar ɗana da kuma da ƙanwata da innata kakemin buƙulun samu
to naji na gani. Amma yanzu ka sani ba'a matsayin mai aikinka nake ba,a matsayin
wacce zata taimakeka nadawo. Ruwanka ka karba kokuma akasin haka,amma ni zan
taimaka maka saboda hakan..........(jan hanci nayi tareda saita muryata da take
rawa)......buƙata ta ɗaya ka yarda dani,banida nufin cutarwa a gareka,in ka amince
kayi sallah kafito kafinnnan na gama abinci"
Inagama faɗamasa hakan na fito daga ɗakin na nufi kitchen,na ɗauko kayan abinci
daga kitchen ɗin gidan,wanda zan dafa kafin dr Saleem ya kawo kayan abincin kaman
yanda yace.
SADI-SAKHNA CEH
09035784150
ku tuntubeni domin biyan kuɗinku ko ƙarin bayani.
*SANADIN CACA*
-BOOK 2 (PAID)
Mallakar *SADI-SAKHNA*
09035784150
Bismillahir-rahmanir-raheem
Ki biya kan ki karantamin na biyu dan Allah. ga number ta nan mai son littafi na
ɗaya yayi min magana zan bashi shi kyautane.
Sister's duk wacce batayi anfani da sabulun mg's ba ko kit dinsu inamai shaidamuku
anbarku acan baya domin duk wnd yajaraba mg's sai sanbarka duk wani Mai tantama
Akan kayan gyaranjiki toh tabbas yacire sabulun mg's domin yahadu bakarya
zegyarajiki yafidda dattin fata Dama duk wani matsalan fata duk Wanda kefama da
matsalan fata walau pimples ko spot, sunburn acne,stretch mark dama dukkan wani
prblm yajaraba mg's bi'iznillah komai zaizama labari bayan jikinku yy fresh zaisa
jikinku yy smooth yadinga glowing,gawanda basa San anfani da Mai zaku iya using
😯 wnn new soap din💣ne,😯 bama cika Baki kujaraba
mg's batare da kunbukaci wani Mai bnd
kugane ma idanku domin ance gani yakoriji Kuma siyan daya maida kudi gida
You can check pic👇for the soap reviews🥰
Soap price:4k
maiso yy mgn
08062991549
07046881166
07067210195
Call 08064532391
Instagram:glow_with_mgs
Facebook: mg's skincare
Munatura Kaya kowani gari dayardar Allah Amma delivery is not free
*BOOK 2*
...14...
Jallof ɗin taliya nayi da ice fish,saina markaɗa ayah nayi kunun ayah mai kauri.
Abinda yasa nayi na kula ko lokacin da yana goje yanason a sarrafa masa taliyah..
Ina yin abincin amma gabaɗaya tunanina ya rabu gida biyu,shin zai ci kokuma
ahah,idan bai ci ba yazanyi?.
Na sauƙe abincin kenan ina sakawa kunun ayan ƙanƙara naji motsinsa falo..
Leƙowa nayi a hankali kaman munafuka,a zaune yake a akan kujera yana kallon wani
labarai a bbc.
Komawa nayi da baya ina kallon kwanukan abincin dana shirya.
Ta maza nayi tareda yin shahada na ɗauki tiren nafito zuwa falon.
Har na ajiye akan center table bai kalleni ba,nima kuma ban fasa ba. A flate na
zuba masa sai ƙamshi takeyi,dan murmushi nayi ganin yanda ya haɗiyi yawu ta gefen
idona.
Tura masa nayi gabansa bayan na saka fork akai,shima kunun ayan na zuba a kofi na
miƙa masa.
"Bismillah gashinan na gama,kaci koda kaɗanne saboda yanayin da kake ciki,barina
tafi idan kagama zanzo na ɗauke"
Yajini sarai amma bai kalleni ba sai kace gunki,a raina nace wannan inaga da a
gidan sarauta aka haifeshi bazaiyi magana ba ma.
Tashi nayi daga durkushen danake nafita daga sashen.
A bakin ƙofa na haɗu da Saleem zai shigo.
"Ahah Sumaimah ya mutuminnaki ne?"
Ƴar dariya nayi kafin nace.
"Ehh to bazance komai ba,nayi masa abinci dai,amma har na fito bai yimin magana ba"
"Iyee kafin kayan abincin suzo harkin fara girkin,toh nima cikinnawa bai ɗauka
ba,barina shiga na tayashi. Am yawwa naje na kaimusu list ɗin abinda kike
buƙata,zasu kawo a motar shagonnasu in anjima zuwa yamma"
Jagayeni nayi ya shige ciki hana murza hannu,hakan da yayi sai ya bani dariya.
Shikam babu ruwansa kaman ba ɗan gidan ba. Sashenmu na nufa,inyaso in an kawo kayan
na dawo. Ina can inata kulada shi ashe ni banci abinci ba tun safe. Cikina sai
ƙiran ciroma yakeyi.
Ina shiga akan kwanon abincin na dura babu tsayawa.
"Kina can kina aikin da ba'a sakaki ba,saida kika ɗebo yunwa kafin kikasan da nan
koh,nayi zaton ai kinci abincin a can"
Ummi ce tayi maganar tana fitowa daga banɗakinmu,fuskarta da ruwa,da alama alwalar
la'asar tayi.
"Kinci abinci ne?"
"Meyasa kika tambaya,mai zan jira?"
"Saboda naga ranar dana daɗe ban dawo ba bakisan natafi siyayya da umaru driver ba
kinyi zaton bata nayi,ko abinci baki ci ba"
"Waye yace miki,ni ban nemeki ba kawai dai banajin yunwa ne,yanzun tun ɗazu a ina
kike,nasan dai a kin daɗe kikai Azahar"
Tana maganar ne bayan ta saka hijabi tana shimfiɗa sallaya.
Kallonta nake da mamakin halinta,a yanzu in wani ya ganta zaice tafi kowa
tsanata,amma allah ne kaɗai yasan tunani da tayi da bana nan.
Fuskar damuwa na ɗora akan fuskata bayan na rufe kwanon abincin na turashi gefe..
"Hmmm bashida lafiya ne,ni bansani ba saida dr Saleem ya faɗamin ashe ciwon yayi
tsanani sosai,matuƙar bazai dunga cin abinci akan kari ba to ciwon zai tashi. Gashi
wai bayacin abincin gidannan"
"To miye naki a ciki,ƙaramin yarone da sai an faɗamasa lokacin da zaici abinci
saboda kada yayi masa illah? To yanzu da kike faɗamin mai zakiyi akai,sufah masu
kuɗinnan duk da suna burgeni to kuma suna bani haushi"
Kallonta nake yanda ta zage tana ta masifah,nayi zaton bataganin laifin masu kuɗi
sai talakawa ko ƴan ƙyauye,to ashe ba haka bane,kowama bata barshi ba,duk da cikin
zuciyarta ba hakan bane.
"Na yanke shawarar zan dungayimasa girki a sashensa,dan haka bazan dunga dawowa da
wuri ba"
"A nawa zaki dunga yimasa kuma"
"Wannan ba zancen kuɗi bane,nice na saka kaina bashi yace nayi ba"
"Tabɗi kyauta kuma,ina kanki ya shiga,ko kema sonsa kike kaman sauran wanda sukayi
masa aiki a baya kai?"
"Ahah ba haka bane,bazaki gane bane ummi amma......"
"Kinga bazan gane ba,ba kuma saina gane ɗin ba,dan haka karki takurawa kanki wajen
yin bayani,barikiga nayi sallah kar lokaci ya ƙuremin. Ohh yawwa nama manta,in
kingama aikin saka kan kada ki manta hajiyah Maryam na nemanki,yau baki gyara mata
side ɗin ta ba,bayan kuma kinshiga sa safen"
Dumm gabana ya buga,sai yanzu na tuna abinda ya faru,tabbas na shiga kaman zanyi
aiki,amma sainayi bincikena kawai na fito.
Runtse ido nayi tareda jijjiga shi,Allah gani gareka.
Ahmad (POV)
A hankali ɗabi'unta sai sanjawa suke,abin mamaki kuma na gaza cireta a rayuwata
kaman sauran mutane idan naga basuda amfani a gareni,kallon kawai idan tayimin
saina tsinci kaina da masa yimata abinda nayi niyya.
Ɗazu da baccin wahala ya ɗaukeni ban taba tsammanin zan tashi naganta a gefena
ba,nayi zaton kaman ko yaushene lokacin danake yaro,bana samun kowa a gefena a duk
sanda nake buƙatar taimako. Dana ganta a gefennawa abin sabo yazame min,kuma saina
tsinci kaina da jin daɗin hakan.
Amma kuma abin tambayar mai take anan wajen,yaushe ƴar aiki zatazo kawai ta zauna
da wanda takewa aiki dan bashida lafiya. Abinda yake haɗani da ita shine bata riƙe
mutuncinta a matsayinta na mace,amma kuma nafara kula ni kaɗai takewa hakan,ko
Saleem da suke magana bata bari suzo daf da juna,ko yaushe tana gefe idan suna
magana,kuma ta takure jikinta. Amma ni kaman ɗakin iyayenta haka take shigomin
ɗaki,yanzu harda banɗaki ma.
Har nazo shiga banɗaki maganganun da take suka tsaida ni cakk da sake ƙara ɗaga
ƙafata.
Shin mai ya haɗa rayuwata da tata da ta damu saita taimakamin,kuma hakan ma wai
ba'a matsayin mai aiki ba,har tana roqon na yarda da itah,wanda kafin ta faɗa ma na
tsinci zuciyata da fara hakan.
Maganar ta ƙarshe ta sakani jin babu daɗi,a tunanin ta baƙin cikin abinda za'a bata
a albashi wai nake? Akan meyasa toh. Wata zuciyar tacemin saboda ka koreta
mana,kaman yanda kakewa sauran masu aiki a lokacin baya,shin kasan mai suke shiga
idan kayi sanadiyyar barin aikinsu? Amma ai ba laifina bane,sune suke abinda bai
dace ba.
Abinda ya ban mamaki kuma wai tana da ɗa. Kenan tanada aure ko ta taba aure?.
Koma dai menene zan bata dama nagani.
Lokacin dana fito kafin nayi wani tunanin ƙamshin abinci ya buɗemin hanci,ohh tun
lokacin dana dawo ƙasar nan Abbah yabani sashennan ban tabajin ƙamshin abinci a
cikinsa ba sai yanxu. Sai kuma naji kamar duk tsawon lokacinnan sai yanzu yayi
numfashi ya zama rayayye,a da tamkar matacce haka yake.
Ina nan zaune kallo kawai nake amma hankalina yana kan son sanin wanne irin abinci
take. Dayake tunanina yana kan kirchen ɗin ina ganin leƙowarta kafin ta koma ta
fito da abincin.
Ɗan murmushi nayi,tanada yarinta saidai daga gani batasan tanada itaba. Bayan
takawo abincin ta ajiye magana take yi,ina jinta amma narasa mai zance da
itah,kalmomin bakina dukka sun gudu sun buya. Nasan zataji babu daɗi ganin har ta
gama maganar ta zuba abincin ta fita bance mata komai ba.
Runtse ido nayi tareda jan ƴar ƙaramar tsuka,tayimin abubuwa dayawa yau ɗinnan,ko
nuna damuwarta ma da tayi akaina abune ta ban fiya samunsa ba,atleast ta cancanci
godiya.
Na ɗau fork ɗin kenan nayi loma ɗaya,idon rufe inajin danɗanon yana ratsani naji
takun samun Saleem ya shigo. Shikenan yazo bazai bari naci a salama ba.
Bai tsaya tambayar komai ba yaja na kular kagabansa yafara ci.
Da mamaki nake kallonsa.
"Daga zuwa ba'a maka tayi ba saika fara cin abinci?"
"Nima fah kaman kai yunwar nakeji,sakacin rashin kulada lafiyarka tasa ban zauna
ba,waccar mai aikinnaka tasakani a gaba da ido cikeda hawaye. Sannan a yanda ka
rufe idonnan kana karbar saƙon girki bakada alamar yimin tayi nan kusa,ballantana
ma mai abincin tace naci ai. Shiyasa na bawa kaina kafin a bani. Wow to ya gaji
abincin yamda yayi wani ɗanɗano?"
"Uhm ba laifi kam yayi daɗi,nafada ina sake kaiwa wata lomar"
Dariyar danaji ya sheqe da ita yasakani saurin kallonsa.
"Yadai kake dariya kamar zararre,wai yaushe mutane suka fara sakewa dani ne har
suke kawomin shirme"
"Easy bro ba zarewa nayi ba,da kake faɗin haka kaima ai ka sauya sosai ba kaman da
ba"
"To meyasa kake wannan dariyar?"
"Uhmm naga ka zage sai loma kake ne,mai cewa baya iyacin plate na abinci gashi yana
shirin tashi dashi"
"Ohh nima nayi mamakin hakan,maybe yanada nasaba da rashin cin abinci a gidane
saboda abinda ya faru, cin abinci a waje kuma ba wani sonsa nake ba,idan nayi take
away kuma ina isowa gida sainaji na kasa ci"
"Ehh lallai ina Sumaimah tazo taga yanda target ɗinta ashe zai kamaka,har take
damuwa da tunanin ba zayyi aiki ba"
"Wane target,wani abu kuke shiryawa?"
"Ahah ba komai bane,kawai nayimin magana ne akan nasa a kawo kayan abinci nan
sashennaka,wai dama ta daɗe da gyarashi. Shine nace to tayi list ɗin abinda take
buƙata,ina can ta turamin ta message na faɗawa plazar,yanzu hakama nasan suna
hanyar kawowa"
Cikeda mamaki nake kallon Saleem kaman nasamu hoto,yaushe sukayi wannan maganar duk
ban saniba
"Yanzun kana nufin kace masu kawo abinci suna zuwa,meyasa baku faɗamin ba to kafin
ku aikata,yaushe na zama ƙaramin yaron da zaku dunga juya rayuwarsa da
muhallinsa?".
"Yah Ahmad bafah dan mun rainaka bane,hasalima ni bani na kawo shawarar nan
ba,itace tace zatayi da kanta,saboda jikinka yafi buƙatar abinci marar
nauyi,sannnan kuma akai akai. In mutum yanada case da abincin irin haka na siya
bazayimasa,kaikuma bakacin abinci a gida. Shiyasa tace tunda da kitchen a sashenka
a kawo komai da komai nan zata tunga yi maka.
Yah Ahmad serious bansan mai yake cikin zuciyar Sumaimah ba,amma nuna damuwa da
kulawar da take akanka baya min kamada wai so kaɗai,kuma wai kana matsayin
ubangidanta,akwai wani abun bayan haka. Bugu da ƙari abinda tafaɗa ɗazu yabani
mamaki"
"Mai tace?"
"Danayi mata maganar bakada lafiya,saboda ciwon dayake cikinka kafin nace komai
tace wai,wannan ciwon dakaji shekaru biyu baya,dama tasan dole zai jawo matsala
saboda yanada zurfi. Nayi mamakin a ina tasani.
Dana tambayeta a ina tasani sai tacemin a gidan taji,ban yarda da amsarta ba amma
koma menene da alama bataso a sani. Na zargeta da sanin wani abu akan ka,amma a
raina ina kyautata zaton batada mungun nufi akan ka. Shiyasa nayi tunanin ka barta
tayi aikin,koba komai zamanta kusanka zaisa ka sake gane wani abun."
"Hmmm inaga tanada labarin abinda ya faru dani,Allah yasa itama ba yarinyar hajiyah
maryam bace kaman sauran,shikenan zan barta tayi aikin domin na gano mai tasani
gameda ni,sannan waye ya faɗamata"
Muna cikin maganar ƙira yashigo wayar Saleem ya tashi ya fita,naji yana cewa su
shigo gidan ta wajen sashena ƙofar baya,da alama masu kayan abincinne.
Kaman yanda ya faɗa na yarda da bayaninsa,duk da ina ƙi amma rayuwata sai sanjawa
take,tana shigomin da wasu mutanen da banyi tsammanin shigowarsu ba.
Saleem ne ya shigo da bandir a hannunsa,bayan ya ajiye ya sake komawa.
Nima binsa nayi na fara ɗaukowa daga cikin motar.
"Bakada wani ishashshen lafiya,da ka bari ma zan shigar dasu dukka"
"Uhm ba matsala naji sauƙi ma,waye ya siyo kayan,a matsayin na gida ka karbo kokuma
kaine ka siya?"
"Bro kabar wannan zancen,idan so kake ka siya menene na sauri,ina wanne waje zaka
siyo inka ja girki"
Na tambayane kawai,nasan shine ya siyo kuma bazai faɗamin shiɗin bane. Kaff a
gidannamu daga shi sai Mammah su kaɗaine muke zama muyi maganar kirki,Maimuna ma
wani lokacin muka yi hirar bincike idan mun haɗu,ita ɗin ma jefi jefi ne,saboda
batada doguwar magana kamarni.
Kallon kayan abincin nayi sun cika kitchen ɗin.
"Yanzu wannan taya zasu zauna a nan wajen?"
"Zuba ido kaga idan tazo yanda zata shiryashi,bakaji akace wani kayan sai amale
ba,Aikin wani kuma wasan wani"
Ehh to hakanne nan ɗin tamkar fadarsu ce,su sukasan yanda zasu shirya komai.
Ohh ko wacce irin rayuwa zamuyi?"
SADI-SAKHNA CEH
09035784150
ku tuntubeni domin biyan kuɗinku ko ƙarin bayani.
*SANADIN CACA*
-BOOK 2 (PAID)
Mallakar *SADI-SAKHNA*
09035784150
Bismillahir-rahmanir-raheem
Ki biya kan ki karantamin na biyu dan Allah. ga number ta nan mai son littafi na
ɗaya yayi min magana zan bashi shi kyautane.
Sister's duk wacce batayi anfani da sabulun mg's ba ko kit dinsu inamai shaidamuku
anbarku acan baya domin duk wnd yajaraba mg's sai sanbarka duk wani Mai tantama
Akan kayan gyaranjiki toh tabbas yacire sabulun mg's domin yahadu bakarya
zegyarajiki yafidda dattin fata Dama duk wani matsalan fata duk Wanda kefama da
matsalan fata walau pimples ko spot, sunburn acne,stretch mark dama dukkan wani
prblm yajaraba mg's bi'iznillah komai zaizama labari bayan jikinku yy fresh zaisa
jikinku yy smooth yadinga glowing,gawanda basa San anfani da Mai zaku iya using
😯 wnn new soap din💣ne,😯 bama cika Baki kujaraba
mg's batare da kunbukaci wani Mai bnd
kugane ma idanku domin ance gani yakoriji Kuma siyan daya maida kudi gida
You can check pic👇for the soap reviews🥰
Soap price:4k
maiso yy mgn
08062991549
07046881166
07067210195
Call 08064532391
Instagram:glow_with_mgs
Facebook: mg's skincare
Munatura Kaya kowani gari dayardar Allah Amma delivery is not free
*BOOK 2*
...15...
Sumaimah (POV)
"Tambayar ki nake,meyasa yau baki yimin aikiba,kuma ance kin shigo,to me kikayi
bayan shigowar?"
Shuru nayi ina kallonta,daga baya na sunkuyar dakai,shin mai zan ce mata ne ma,ni
dai ba nace na shigo nayi mata bincike ba. Ohh wayyo Allah nah.
"Uhm Hajiyah nashigo amma kafin na fara aikin sai nace barina fara yiwa Yallabai
tukunna,to kuma danaje bashida lafiya saina manta ban dawo ba. Kiyi haƙuri hajiyah"
Tunda na fara maganar kafeni tayi da ido,da alama bata yarda da abinda nake faɗa ba
sam.
"Yaushe kika zama mahaifiyarsa da idan bashida lafiya bazakiyi wani aikin ba uhm?"
"Uhm kiyi haƙuri hajiyah,dan Allah za'a iya bani iya aikin sashensa kawai,in yaso a
ragemin albashina sai a ɗau wata"
Banida zabi daya wuce na faɗi hakan,duk da nasan hakan kasada ce,tunda banyi aikin
da nazo yi ba,shi ya riga ya koreni banida albashinsa,iyah na hajiyah maryam ne,to
ita kuma idan na haɗa da aikinta bazan samu damar kulada sashensa ba sosai.
"Meyasa kikace haka? A tunanina iya shara da goge goge kike yimasa,a kaf ma'aikatan
gidannan ke kaɗaice mai aiki kaɗan,amma a hakane zaki rasa time na yimin
aiki,lokacin da kikazo fuskarki ya nuna buƙatar kuɗin aikin ki muraran,amma yanzu
kina cewa kin yarda a rage kuɗin aikinki saboda aiki a bangare ɗaya?.
Ɗazu ance kin haɗu da hajiyah Mammah har tayimiki magana,alamu ya nuna ta yaba da
hankalin ki. Koda kin bar yimin aiki to inaso na sakaki a sashenta,zaki dunga
yimata goge goge da shara,zan sauya mai aikinta"
Meyasa zata sauya mai aikinta ta sakani,nace banason nayi mata kuma tasake turani
wani wajen?.
"Amma hajiyah....?"
"Kince bazaki yimin aiki ba na yarda toh,amma wannan ba wai turasasaki zanyi
ba,ahah ina roƙonki ne kiyimin wannan aikin,saboda dake kaɗai na yarda a kaf cikin
gidannan. So nake kiyi mata aiki amma ki zama idona da kuma kunnena a sashen. Amma
idan kinje karki sake ki nuna nina kawoki kokuma kinada alaqa dani, idan hakan ya
fito kina cikin hatsari. Ki kuma yi taka tsantsan da komai,kije inada abinyi
yanzu,gobe zaki fara yimata aiki"
Tana gama faɗin hakan ta shige banɗaki,jan numfashi nayi tareda kallon hnayar da
tabi ɗin,wannan matar mai take nufi,kota kula nayi mata bincikene shiyasa take
ƙoƙarin turani wajen waccar dattijuwar kai.
To amma meyasa naga tarin damuwa a idonta lokacin da take roqona,babu wannan jiji
da kan da kuma ɗaga kai,tayimin kama da wacce takeso ta kare wani abu nata.
Ƙarar shigowar message nagani a wayata,da bazan duba bama,domin a zatona mtn ne
zasuyimin tujarar bashin danaci.
Ba sunan mtn nagani ba,wata number ce babu suna,hakan yasa na tsaya na buɗe.
_zama dashi yasa kin fara mantawa da halin da kike ciki da kuma shi,ki kusa dashi
amma kiyi taka tsantsan,sannan duk rintsi karki bayyana masa matsayinki a
wajensa,yin hakan a yanzu hatsari ne gareki da kuma ɗanki_
Zaro ido nayi tareda maimaita saƙon akai akai har bansan adadi ba..
Waye yasan wacece ni,waye yasanni a gidannan bayan inna ladiyo ita kuwa batada waya
bare ta turomin saƙo,ba kuma Saleem bane,domin shima bai san wacece ni ba.
Shin na yarda da gargaɗin kokuma na watsar,idan da gaskene nima na fara zargin
Ahmad yana cikin hatsari a gidannasu,to amma waye yake haddasa komai,ina zargin
hajiyah Maryam,amma kuma a raina ina jin kamar ba ita kaɗai bace akwai wata.
Ajiyar numfashi na sake tareda wucewa sashenmu,naso zuwa sashensa a yanzun nayi
masa abincin dare,bashshi kawai sai gobe naje.
........
Tana maganar dama daƙyar takeyi,saboda wani abu da takeji yana taso mata a
zuciya,shiyasa tun kafin ta sallameta tayi saurin barin ɗakin ta shiga banɗaki..
Kai tsaye bakin sink ɗin ta nufah tareda fara sheqa aman jini mai kauri harda guda
guda,ta daɗe tanayi kafin ya tsagaita mata kaɗan.
Komawa tayi ta zauna akan bahon wankan dayake banɗakin,haki takeyi numfashinta yana
sama sama,riƙe ƙirjinta tayi tana runtse ido.
Ta daɗe a hakan kafin ta miƙe cikin dauriya ta fito daga banɗakin.
Wayarta ta ɗauka akan gado ta danna ƙira,bata ce komai ba har wacce ta ɗauki ƙiran
ta gaji ta kashe.
Zama tayi a bakin gadon har sannan hannunta yana kan ƙirjinta.
Banko ƙofar akayi da sauri,Neelah ce amma cikin tashin hankali ta shigo ɗakin.
Gaban hajiyah maryam ɗin taje ta tsugunnawa,idon ya cika ta ƙwallah,ganin yanda
hajiyah maryam ɗin tayi fari soll kaman fatalwaa.
Cikin rawar murya da fara magana cikeda damuwa.
"Mmm....ommy har yaushe zaki cigaba da wannan abun,ya isa haka don Allah,kinsan
muna buƙatarki bai kamata ki dunga bada rayuwarki ba,ya isa haka,kiga fah yanda
jikinki yayi,muje kiƙara jinin inyaso saimu dawo idan ya ƙare"
"Ahah Neelah nagaji da wannan irin rayuwar,wahala da kuma gudura ne gareta,idan har
ban tsayar da auren sa da kowacce mace ba hakanne zai cigaba da faruwa,nikuma na
gaji da takurawa rayuwarsa Neelah,na cutar dashi da yawa,ya isa haka,sun tabbatar
min idan har banyi wani abun ba to kona mutu bazasu tabamin ƴaƴa ba,dan haka Neelah
zan ɗau komai a kaina na tafi. Koda na tafi don Allah kici gaba da.........."
"Ahah nikam,nikam dan Allah ki daina wannan maganar,bazan jita ba banason ma na
jita,baki cancanci haka ba,su ya kamata su cutu bakeba,kin juri azabarsu tsawon
shekara da shekaru,bai kamata kici gaba da jurarta ba har yanzu,dole ne muyi wani
abun,karki damu zanji da komai. Zanyi iya ƙoƙarina wajen kin cika abinda suka ce
ɗin,badai waccar shegiyar Mulaifan suke tunani ba,to Inshaallah bazai aureta
ba,dama bata dace dashi ba ko kaɗan. Yanzu dai ki tashi muje asibitin nayiwa Dr
Mus'ab magana yana jirnmu ma yanzu haka"
Tashi neela tayi tareda zan hannun hajiyah maryam ta tashi. Amma taƙi koda motsawa.
"Yanzu Neelah haka zan dunga zuqe jinin mutane a jikina yana ƙarewa,aikina kenan"
"Ahah ba iya aikinki ba kenan,kinyi abinda wasu ma bazasu taba iyawa ba,you deserve
it"
Da ƙyara Neelah ta samu ta yani hajiyah Maryam ta tashi zasu fita,jikinta duk ya
shiga kaman wacce tayi shekara tana jinya,numfashinta ma daƙyar yake fita.
Mayafinta ta yafa mata suka buɗe ƙofar baya,ta kusan sashen masu aiki ta baya.
Lokacin ana ta ƙiran magriba a masallatu.
Daidai fitowarsu zasu wuce sai a kan idon Sumaimah wacce ta kayan wankinta da tayi
tun safe,ta manta bata debe ba.
Zaro ido tayi ganin Neelah ta riƙo hannnun hajiya Maryam suna tafiyah,yanda take
takawar kaman matar data fito daga labour,yanzunnan fah ta rabu da itah kafin
magriba?.
Kayan da ajiye a jikin ƙarfen fence ɗin lambu ta lallaba zuwa ta bayansu.
Hanyar wajen mota taga sun nufah,to amma in batada lafiya mai yasa suka fito ta
ƙofar baya,hakan ma a boye saida kowa ya tafi sallah.
Jijjiga kai tayi da alama hankalin ta bai kwanta da wannan fitar ba..
Tsayawa daga sunyi,hakanne yasa ta bar tunanin ta tattara dukkan nuturwarta akan
sanin mai zai faru ko yake faruwa.
Yunƙuri daga Hajiyah Maryam tanayi kaman mai shirin amayar da abin cikinta,zaro ido
tayi ganin yanda maimakon amai ya zubo jini ne yake zubowa.
"Hasbunnallahu menene haka"
Sumaimah ta faɗa tana saka hannunta a baki.
Saurin ƙarisawa motar Neelah tayi da itah ta rufe ƙofar..
Dawowa tayi ta ɗau wani bokiti a wajen ta tari ruwa ta sheqa. Lalleƙawa tayi ko
zataga wani yana binta,ganin babu kowa yasa ta shiga motar suka zasu.
Cije yatsa Sumaimah tayi,ranta cike fall da son sanin shi mai yake faruwa ne..
Ganin suna shirin fita daga gidan yasa ta tashi ta bisu a baya.
Neelah ce tafita ta buɗe get ɗin gidan,dayake mai remote,ana kunnawa yake buɗewa
kuma kaman abin haɗin baki babu kowa a wajen.
Binsu tayi a baya ganin da gaske fita zasuyi.
Babu kowa a bakin titin sai napep kaɗan kaɗan da suke wucewa,ga motar su hajiyah
maryam tana yin nisa.
"Hajiyah wani wajen zakije ne naga kin tsaya kina leqa hanya?"
Wani mai taxi ne yayi mata magana.
Kallon kayan jikinta tayi,doguwar rigace saita ɗaura dan kwalinta.
Sinceshi tayi tareda yimasa yafin gyale.
Ƙofar motar ta buɗe tareda faɗawa ciki.
"Waccar baƙar motar zaka bi don Allah,kayi sauri kada su bace dare yafara yi"
"To shikenan"
Tada motar yayi yabi bayan su Neelah.
"Mommy ki daure mun kusa isa"
Raba hankalin ta tayi biyu,ɗaya na kan hanya ɗaya kuma yana kan hajiyah Maryam
wacce take nishi ɗaɗɗaya..
Ma'aikatarta ta marayu suka nufah,kasancewar babbace sosai akwai part na abubuwa
kala kala a ciki,har asibiti.
A bakin wajen mai motar ya ajiye Sumaimah,anan gizo yake saƙar batada kuɗin mota.
"Hajiya kuɗinki ɗari biyar"
Wuri wuri tayi da ido,domin batasan ta inda zata samo kuɗin ba sam.
"Mallam kayi......."
Tun kafin ta gama maganar wata ta miƙama ɗari biyar.
Karba yayi yaja motarsa ya tafi.
Cikeda mamaki ta juya ta kalli matar data biyah kuɗin,wata dattijuwa ce amma ba
sosai ba,murmushi tayiwa Sumaimah tareda cewa.
"Neelah ce tacemin akwai wacce ta biyosu naje na biya kuɗin taxi ɗin,tasan baki
ɗakko kuɗi ba daga gida"
Sororo tayi tana kallonta,kenan dama sun san tana binsu,mai yasakata yin wannan
garajen hakane,duk ta makance akan neman gaskiya,ji inda ta tsinci kanta da daren
Allah.
"Mai kika tsaya yi,tace na shigo dake inda suke,suna bangaren asibiti na nan
wajen,koba tare kuke ba kai?"
"Ahah ......uhmm tare muke"
"To biyoni na nuna miki,suna saurine shiyasa basu jiraki ba inaga,ciwon hajiyanne
ya tashi,naga na yau ma yafi na kullum tsauri,Allah sarki tana shan wuya wannan
baiwar Allah"
Cikeda tausayi tayi maganar,jin abinda ta faɗa yasa Sumaimah tambayarta..
"Batada lafiyane hajiyan?"
"Ohh baki sani ba? Ai kusan duk wata saita sha ledan jini,wani ciwo ne da ita yake
zanye mata jini"
Hmmm ko basu san tana shigewa da bango bane,nasan yanzu haka shine yake zuqe mata
jini.
Wacce na ganta da ita kuma yanzu haka wannan matar ce tasuka zo tare,dama ina yawan
ganinta tashiga sashenta ta ƙofar baya. Gashi na biyosu sun ganni,sunsan ina
bibiyarsu. Anya kuwa bazan gudu ba,kar naje na shiga a ɗau nawa jinin a saka mata .
tunda suka biyamin kuɗin taxi zasu fanshe a jinina,koma mai sukamin nina jawowa
kaina,tunda ƙafata ce ta kawo ni.
Wannan tunanin Sumaimah take tayi a cikin kanta sinka sinka,yayinda a zahiri kuma
take ɗaga ƙafarta tana bin matar duk lungun data bi,kaman wanda aka ɗaura mata
igiya akace saita je.
"To mun iso wajen,waccen ɗakin zaki shiga suna ciki,nasan an fara ɗaura mata
jininma"
"To ki rakani mana meyasa zakice na shiga?"
Jijjiga kai tayi tareda cewa.
"Bana son ganinta a wannan yanayin,bama haka ba kuma ba'a son mutane da yawa
wajennata harsai ta tashi tukunna"
"Nikuma an yarda na shiga?"
"Ehh Neelah tace ki shiga,domin cewa tace na taho dake idan na biya kuɗin taxi
ɗin,sannan batace ki tsaya a waje ba,kinga kuwa tana nufin ki shiga kenan,sai
anjima barinaje kar yaran danake kula dasu su nemeni"
Tana gama faɗin hakan ta bar wajen.
Aka bar Sumaimah ta tunanin ta tura ƙyauren ɗakin tashiga kokuma ta juyah.
SADI-SAKHNA CEH
09035784150
ku tuntubeni domin biyan kuɗinku ko ƙarin bayani.
*SANADIN CACA*
-BOOK 2 (PAID)
Mallakar *SADI-SAKHNA*
09035784150
Bismillahir-rahmanir-raheem
Ki biya kan ki karantamin na biyu dan Allah. ga number ta nan mai son littafi na
ɗaya yayi min magana zan bashi shi kyautane.
Sister's duk wacce batayi anfani da sabulun mg's ba ko kit dinsu inamai shaidamuku
anbarku acan baya domin duk wnd yajaraba mg's sai sanbarka duk wani Mai tantama
Akan kayan gyaranjiki toh tabbas yacire sabulun mg's domin yahadu bakarya
zegyarajiki yafidda dattin fata Dama duk wani matsalan fata duk Wanda kefama da
matsalan fata walau pimples ko spot, sunburn acne,stretch mark dama dukkan wani
prblm yajaraba mg's bi'iznillah komai zaizama labari bayan jikinku yy fresh zaisa
jikinku yy smooth yadinga glowing,gawanda basa San anfani da Mai zaku iya using
😯 wnn new soap din💣ne,😯 bama cika Baki kujaraba
mg's batare da kunbukaci wani Mai bnd
kugane ma idanku domin ance gani yakoriji Kuma siyan daya maida kudi gida
You can check pic👇for the soap reviews🥰
Soap price:4k
maiso yy mgn
08062991549
07046881166
07067210195
Call 08064532391
Instagram:glow_with_mgs
Facebook: mg's skincare
Munatura Kaya kowani gari dayardar Allah Amma delivery is not free
*BOOK 2*
...16...
Tun zuwanta tab da bakin ƙofar kafin ta tura take jin nishin hajiyah maryam a cikin
ɗakin.
Cire komai dayake ranta tayi ta afka cikin ɗakin,ma'aikaciyar jinya ce sanye da
kayan likitoci,sai ɗayar kuma kayane haka a jikinta,sai kuma Neelah da take tsaye a
wajen kan hajiyah Maryam,wacce take kwance tana lumshe ido sama sama.
Sumaimah tana shiga da Neelah suka haɗa,wacce kallo ɗaya tayi mata ta ɗauke
kanta,domin hankalin ta yana kan hajiyah Maryam.
Kaman munafuka take takawa har taxo daidai tsakiyar ɗakin,daidai lokacin da hajiyah
Maryam tayi wata ƙara mai cikeda firgici,fizge fizge tafarayi tana ƙoƙarin yage
ƙarin jinin dayake shiga jikinta,yayinda suma suka ƙara ƙaimi wajen rirriqeta.
"Innalillahi kuyi wani abun zasu cire min zuciya,wannan karon kam da ita zasu
tafi,kucewa ƴaƴana su yafemin wayyo Allah nah"
Mai sanye da kayan likitanne ta kalli Sumaimah da take tsaye, tayi suman tsaye.
"Baiwar Allah miƙomin allurar can nayi mata,da alama zafin ciwone
yasakata....Neelah ki riƙeta sosai fah,karki bari ta cire igiyar"
"Ai ba igiya take ja bama,anty indo,da alama ƙirjinta takeson tabawa"
Neelah ta faɗa cikin tausayawa kaman zatayi kuka,daidai kuma lokacin da Sumaimah ta
miƙawa matar allurar.
Ƙarba tayi da sauri ta zuba a jikin carnular,kafin tacigaba da shafa kanta.
Sun daɗe a hakan kafin ta daina jijjigar,jikinta ya shika baccin wahala ya ɗauketa.
Saketa sukayi sauran matan biyun suka bar ɗakin,yayinda itakuma Neelah har yanzu
batayi motsiba tana nan a zaune gefen hajiyah maryam ɗin.
"Mai yake damunta haka?"
Sumaimah ce tayi maganar cikin kiɗima da kuma ɗaure kai,don abin duk wanda ya gani
kam sai ya tausaya mata.
"Uhmm nima bansan sunan cutar ba ballantana nayimiki bayani akanta,yanda kika gani
a yanzu haka nake gani nima tun tashi na. Nida hajiyah Maryam mun daɗe da sanin
kina bibiyarmu da abinda muke,kece mutum ta farko data san abubuwan da su kansu
ƴaƴan ta basu san dashi ba. Kaman yanda muma munsanki mun san wacece ke fiyeda
yanda ƴan gidan suka sani"
Zaro ido Sumaimah tayi tareda kafe Neelah da kallo.
"Kina nufin......."
"Ehh nasan ke wacece,daga garinda kike,da ɗanki wanda yake ɗa a wajen Ahmad duk
munsan komai,saidai shi mijinnaki bai san da hakan ba,wanda kuma hakan shine ya fi
a wannan lokacin"
"Kece kika turomin wannan saƙon kenan,na karna faɗawa Ahmad wacece ni?"
"Uhm nice,amma hajiyah Maryam ce tace na turamiki,abinda kikeyi na bincike nasan
kinayi ne domin kare wanda kikeso,amma ki sani zai kasance ɗayan biyune,ko kiyi
nasarar kare wanda kike so,kokuma ki akasin haka,wanda sakamakonsa shine zaki cutar
da masoyanki fiyeda yanda kike zato,zabi ya rage gareki wanne zaki zaba"
Dumm Sumaimah ta tsaya tana kallon Neelah,yayinda kunnunwanta suka buɗe suna jin
abinda take faɗamata,kenan duk tsawon wannan lokacin sunsan wacece itah,da kuma
abinda takeyi to amma meyasa basu koreta kokuma su cutar da ita ba,indai har da
gaske hajiyah Maryam tana ƙin Ahmad to meyasa tasan tasirinta a rayiwarsa amma ta
ƙyaleta,maimakon haka saima cewa da tayi karta bayyana ko ita wacece. Kai dole
akwai wani abu ƙulalle dayake kai kawo a cikin wannan lamarin.
Buɗe bakinta tayi,wanda yayi mata nauyi kaman an ɗaura mata dutse a kansa.
"Kun san wacece ni,kuma kunsan na ganku a abubuwa da dama,to amma meyasa kuka rabu
dani,yanzu ma kunsan ina biye daku amma maimakon ku gujemin saima biyamin taxi da
kikayi,kikace a shigo dani a har ɗakinnan,menene dalilin hakan?"
Ɗan murmushi Neelah tayi na ƙarfin hali kafin tace.
"Sumaimah karki kuskura ki shaidi littafi daga bangonsa,ki bari saikin buɗe cikin
kinga mai ya ƙunsa tukunna,idan kuma ki ƙi,a sanadiyyar hakan zakiyi nadama da tafi
cikin kwando"
Kafin Sumaimah ta buɗe baki tace wani abu sukaji tarin hajiyah Maryam.
Dukkansu a tareda suka waiga inda take. Itama kallonsu take tareda ƙoƙarin tashi ta
zauna.
"Sumaimah ke kuma menene dalilinki na bin mutum waje kawai dan kinga ya fita cikin
dare,idan wajen halakane kenan haka zaki kai kanki ki cutu,miye amfanin hakan
kenan?"
Duk da muryarta tana ɗan rawa saboda rashin ƙarfin jiki,amma cikin dakewa take yiwa
Sumaimah magana.
"Kiyi haƙuri"
Shine abinda ta faɗa tana sunkuyar dakai.
"Uhm shikenan ya wuce,amma abinda Neelah ta faɗamiki gaskiya ne,kidaina jefa kanki
cikin abu kai tsaye ba tareda ƙwaƙwƙwaran shiri ba,kada ki manta keɗin uwace sannan
kuma kinda waɗanda suka damu dake. Neelah tashi ma mutafi gida dare Yayi sosai"
Tun kafin Neelah tace wani abun ta tashi daga kan gadom zata saƙƙo,tana miƙewa
hajijiya tace jira nake,tayi taga taga kaman zata faɗi ƙasa,a tare Neelah da
Sumaimah suka riƙeta.
"Mommy baki samu ƙarfin jiki ba har yanzu,bazayyiwu mu tafi gida ba,za'a iya zargin
wani abun,ki baridai ko zuwa safiya"
Zaunarta sukayi a bakin gadon tana haki tareda riƙe ƙirjinta.
"To shikenan naji,amma ki maida Sumaimah gida kada a ga batanan,ke ma kuma kije ki
huta,indo zata kulada ni"
"Ahah babu wanda zai nemeni,dama ni ƴar aiki ce,kawai zance na rakaki wani wajene
zan riqemiki wani abun"
"Ni a wajena keba ƴar aiki bace,hasalima baki taba zama ƴar aikin a wajena ba,ko
ita wacce ta turoki tasan bazan taba ganinki a mai aikiba,kuma tasan zan kulada ke
shiyasa bata damu ba ta turoki gidannan,amma duk da haka akwai abinda bazan iya
ba,dan haka kibi Neelah ta maidaki gida,sannan koba niba kada ki sake ganin anfita
yin wani abun kisaka kanki a ciki batareda zurfin tunani ba"
Cikin faɗa take maganar,da alama tsoro da kuma fargaba sun kamata a lokaci
guda,wanda hakan yasa suka haifar mata da yin faɗan da bata shirya ba.
Komawa tayi ta kwanta,alamar ta gama bayani kenan bazata sake jin abinda suke
faɗaba.
Fitowa sukayi daga ɗakin,har suka shiga mota suka kamo hanya babu wanda yace kowa
komai.
A bakin ƙofar gidan Neelah tayi burgi bata shiga ba,kallon Sumaimah tayi alamar ta
fita. Hakan yasa ta tura ƙofar motar zata fita.
"Nasan kinason kisan gaskiyar mai yake faruwa,amma sanin hakan bazai miki komai ba
sai sakaki a hatsari,amma in kinga zaki iya ji to ki tambayi hajiyah maryam da
kanki,zata sanar dake komai"
Ɗaga kai kawai Sumaimah tayi,zata sake fita a motar.
"Kin yarda da itah?"
"Ahah koda na faɗa a cikin raina to hakan bazai zama gaskiya a raina ba,saidai kuma
zarginta da nake na yanke kusan rabi a cikinsa. Ni zan shiga ciki nagode ki
gaisheta Allah ya sawwaƙe"
Sumaimah (POV)
"Sumaimah yau ba baccin asuba ne,mai yake damunki naga ko da daddarema duk sanda na
farka saina ganki kina juyi"
"Uhm ba komai ummi,ki koma baccinki kawai banajin yin baccinne yau"
Tashi nayi daga kan sallayar har rana ta fara fitowa saboda daɗewa da nayi a zaune.
Hijabin na cire na yafa ƙaramin gyale akan rigar jikina na fita.
Gidan tsitt yake babu kowa, sai kukan tsintsaye a lambu.
Leƙawa nayi ruwa yana gangarawa wajen tsirran da suke gurin.. Haka kawai ban sani
ba na tsinci kaina dayin murmushi, domin Allah yayini da son Yanayi(nature).
Zama nayi a kan dutsen danake yada zango ko yaushe idan naje wajen. Kasancewar da
ɗan duhu ma bana ganin wajen sosai.
Jiya kam nayi wani abu waishi tunani,tareda neman mafita na lamarin danake ciki.
Wani bangare na zuciyata nason yarda da hajiyah Maryam dakuma abinda nagani,yayinda
wani bangaren kuma yana gargaɗina da yardar,duk abubuwan dana gani har yanzu saina
cigaba da abinda hankali bazai ɗauka ba?.
Tunowa nayi da ashe an kawo kayan abinci a sashen Ahmad,bamma je nagani ba,ga kuma
ƙarin aikin sashen hajiyah Mammah da zan dungayi,duk da ma shi ba mai yawa bane.
Mariya ce in jisu da faɗa take mata abinci,saboda tafison na gargajiya. Ni gurbin
wacce take ɗan tayata da aikace aikace zan maye,sai goge goge.
Tashi nayi daga wajen na nufo sashen sa,ƙofar falon na tura na shiga,nasan dama ba
rufewa zayyi ba bayan ya dawo daga masallaci.
Kai tsaye kitchen ɗin na nufa,yana cikeda kaya kowanne da gindinsa suka ajiyeshi.
Kama kunkumina nayi tareda jijjiga kai, maza dai sai a gaishesu dan ma Allah ya
taimakeni na gyara kitchen ɗin.
Kayan nafara ciccirewa,kowanne ina sakashi a wajen daya dace dashi,na fridge na
sakasu. Har sun fara tsami,musamman kayan marmarin da kuma kaji.
Saida na gama gyara kitchen ɗin tass kafin na ɗaura girki. Sandwich nayi da kunu
gyaɗa,saboda naga harda garin kunun suka kawo.
Bashida bata lokaci dan haka da wuri na gama,ina cikin goge goge na inda yaɗan baci
naji motsin mutum a bayana.
Juyawa nayi da sauri muka haɗa ido da Ahmad,vest ce a jikinsa sai 3 quarter,shima
zabura yayi daya gannin, domin bayyi zaton nazo ba.
Saurin sauƙe ido nayi da muka haɗa ido,yayinda shima yafara kame kame ya rasa abin
cewa.
To mainene ma ni ɗin na wani sunkuyar dakai.
Ɗaga idona nayi na kalleshi kafin na gaisheshi a taƙaice,har yanzu kaina a cunkushe
yake,aikin ma inatayi duk rabinsa a tunani ya ƙare,har a garin yin kunun saida na
zubar bansani ba.
"Meyasa kikazo da sassafennan?"
"Saboda nagama da wuri kafin ka fita aiki,sannan hajiyah Maryam ta ƙaramin wani
aikin,inason inna gama wannan na tafi"
To kawai yace da kansa,kafin yaje inda fridge yake sai ɗau ruwa,ina gani ya tsaya
yayi jimm yana kallon cikin wajen,nasan bazai wuce yanda yaga na cika wajen da
abubuwa ba,komai da nasa wajen.
Ɗaukar ruwan yayi zai fita,har yaje bakin ƙofa nayi masa magana.
"Nagama abincin,a falo zan ajiye maka kokuma na shigo dashi ɗaki?"
"Ahah ki saka a dining ma ya isa"
Daga haka nacigaba da goge gogena shikuma ya fita.
Jera abincin karyawar nayi a dining kaman yanda yace, daga nan kuma na fara gyara
falon.
Fitowa yayi sanye da kayan aikinsa na uniform,dayake kalar yanada duhu,sai yayi
masa kyau sosai,dana kalleshi wata faɗuwar gaba ce ta riskeni tareda mararin jina a
jikinsa,saidai nasan hakan bazai yiwu ba,koma zai farun banan kusa ba. Dan haka
shiyasa na binne komai a ƙasan zuciyata nacigaba da aikina.
"Uhm da kika gama kallonnawa ai ba aikin zaki cigaba ba,saiki zo ki zubamin abincin
koh?"
Ajiye mopar nayi na nufi gabansa,dama na gama da falon.
Buɗe plate ɗin nayi kawai,saboda bamma sakashi a cikin warmer ba.
Fork na saka masa a gabansa,tareda zuba mata kunun a kofi shima na miƙa mar.
Saida naga yaɗau fork din zai faraci kafin na tafi. Ɗakinnasa nashiga,nan ma saida
na tattare kayansa komai nasaka shi a muhallinsa kafin na share.
Daga wannan sai wannan nakebin aikin daki daki,dan yanzu inaga ko idona rufene to
zan iya yin komai.
Lokacin dana gama na fito daga ɗakin ya riga ya fita,dan haka zama nayi naci
abincin a wanda ya bari na kai kwanukan kitchen.
Bayan na wankesu nasakawa sashen turaren wuta na fito,saikuma da yamma idan na
daidaici yakusa dawowa.
Nafito kenan mukaci karo da hajiyah maryam,shigowarta gidan kenan da alama,amma ba
kayan da tafita dashi bane jiya a jikinta kokuma nace aka fita da ita kai.
Wasu kayanne daban masu kwarjini da suka boye faɗawar da fuskarta tayi,saikuma abin
hannu shima daya boye ƙofofin tabon carnular da take hannunta a jiyan. Amma fah
hakan zai boyune kaɗai ga wanda baisan mai yake faruwa ba,bandani da naga komai.
Gaskiya na jinjinawa ƙarfin halin matar nan,ta tsaya ƙyam akan dogon takalmi cikin
izza,kaman ba itace take nishi da ƙyar ba jiya.
Kallo ɗaya tayimin ta ɗauke kanta,nima banyi niyyar tacemin komai ba ai. Duk da
kuwa zuciyata cike take da zumuɗin son sani mai yake faruwa,domin ta hakanne kawai
zan ga wanne irin taimako zan bawa uban ɗannawa.
SADI-SAKHNA CEH
09035784150
ku tuntubeni domin biyan kuɗinku ko ƙarin bayani.
*SANADIN CACA*
-BOOK 2 (PAID)
Mallakar *SADI-SAKHNA*
09035784150
Bismillahir-rahmanir-raheem
Ki biya kan ki karantamin na biyu dan Allah. ga number ta nan mai son littafi na
ɗaya yayi min magana zan bashi shi kyautane.
Sister's duk wacce batayi anfani da sabulun mg's ba ko kit dinsu inamai shaidamuku
anbarku acan baya domin duk wnd yajaraba mg's sai sanbarka duk wani Mai tantama
Akan kayan gyaranjiki toh tabbas yacire sabulun mg's domin yahadu bakarya
zegyarajiki yafidda dattin fata Dama duk wani matsalan fata duk Wanda kefama da
matsalan fata walau pimples ko spot, sunburn acne,stretch mark dama dukkan wani
prblm yajaraba mg's bi'iznillah komai zaizama labari bayan jikinku yy fresh zaisa
jikinku yy smooth yadinga glowing,gawanda basa San anfani da Mai zaku iya using
😯 wnn new soap din💣ne,😯 bama cika Baki kujaraba
mg's batare da kunbukaci wani Mai bnd
kugane ma idanku domin ance gani yakoriji Kuma siyan daya maida kudi gida
You can check pic👇for the soap reviews🥰
Soap price:4k
maiso yy mgn
08062991549
07046881166
07067210195
Call 08064532391
Instagram:glow_with_mgs
Facebook: mg's skincare
Munatura Kaya kowani gari dayardar Allah Amma delivery is not free
*BOOK 2*
...17...
"Fatee ina zakije"
Hajiyah maryam ta faɗa a dake lokacin dataga Fatee ta dosota da alama fita zatayi.
Da mamaki tayi turuss tana kalon mahaifiyar tasu sai kuma ta cuno baki.
"Mommy dama bakya gida,nifa banyi zaton yauma a,wajen aiki kika kwana ba?"
Da Mamaki na kalli fateen,tayini a haife amma wai har yanzu a ƙaramin hankalin ta
uwarta takwana tanashan jini batada lafiya,amma wai bata sani ba? Hmmm dole mutane
su dunga cewa rayuwar masu kuɗi akwai wuyar sha'ani,koda yake itama hajiyah maryam
ɗin na kula tana son ƴaƴan ta dayawa,amma kuma koda wasa bata nuna hakan a gaban
idonsu,komai yasa oho.
"Ba wannan na tambayeki ba,wannan wacce irin shigace kike shirin fita da itah?"
Ta faɗa tana nuna riga da wandon jikinta,wanda rigar ƙaramace bata rufe wandon
sosai ba,sai kuma gyale shima iya wuya. Yanayin shigar yayi kyau sosai,amma fita
dashi a matsayinta na ƴar musulmai kuma hausawa bayyi tsari ba.
"Uhm uhm mommy mota fah zan shiga,ba a ƙafa zan tafi ba,kuma ma........"
"Jeki cire wannan kayan ki saka wasu"
"Amma mommy......"
Tafaɗa kaman zatayi kuka harda buga ƙafah.
"Nace jeki ciresu koh!!!"
Wannan karon da ƙarfi tayi maganar,kana gani kasan dukkan ƙarfinta na lokacin ta
tattaro tayi amfani dashi.
Cikin fushi kaman zatayi kuka tabar wajen da gudu.
Tana tafiya hajiyah maryam ta tsugunna a wajen tana kama ƙirji.
Saurin matsawa nayi kusada itah na tallafi hannunta na dama,ɗago idonta tayi a
hankali tareda zubasu a cikin nawa.
"Taimakamin na shiga ɗakina kafin wani yazo ya sameni a haka,musamman su fatee"
"Kina fama da ciwo amma meyasa bazaki bari iyalanki su sani ba"
Cikin rashin fahimtarta tayi mata wannan tambayar,shin abin kunya ne mutum yayi
jinya,da bazata iyah bayyanawa ba.
Dariyar ƙarfin hali tayimin kafin ta jijjiga kai.
"Hmmm bazaki ganeba Sumaimah,muje"
Daga nan hanyar ɗakinnata muka nufah,a bakin gado ta zauna,har Sannan haki takeyi
jikinta babu ƙarfi.
"Kona kawomiki abinci kai?"
"Abinci kuma,masu girki sun farane da sassafennan?"
"Uhm akwai wanda nayiwa Ahmad a sashensa,to ko ruwan tea ma"
Na faɗa inason kawar da zancen farkon.
Ƴar dariya tayi tana kallon yanda nayi diri diri.
"Menene na sauya zance Sumaimah,nasan zaki fara yimasa girki ai,hakan yanada kyau
sosai,domin bai warke ba amma kullum yana cikin saka rayuwarsa cikin
hatsari.....hmm marayan Allah. Nagode Allah da kikaso rayuwarsa"
Kallonta nake ganin yanda take maganar cikin damuwa kuma daga ƙasan zuciyarta,shin
yaushe zan gane wannan matar ne.
"Ke ba kishiyar mahaifiyar Ahmad bace,kinayin kaman keɗin uwace data nisanta kanta
da ɗanta,kuma take cutuwa dayin hakan"
Saurin zabura tayi ta kalleni,da alama maganganun da take ɗazun tana zaton a
zuciyarta take furtasu.
"Taya kika san hakan?"
Bayan ta faɗi hakan sake ganowa tayi tasake kwafsawa a karo na biyu,diriricewa tayi
da alama tayi matuƙar razana ganin yanda sirrin dayake ƙarƙashin zuciyarta ya fito
fili.
"Sumaimah zaki iya tafiya inason na jini ni kaɗai"
"Toh"
Shine abinda nafaɗa nayi hanyar fita daga ɗakin. Naji maganar ta.
"Duk da cewar abinda kika gano ɗin gaskiya ne amma ba yanda kike tunani
ba.....Sumaimah har yanzu baki yarda dani ba,kuma baki shiga har yanzu matakin
danake so kikai ba kafin ki san mai yake faruwa,duk ƙoƙarina na nabarki cikin duhu
batareda kinsan komai ba kaman sauran mutanen gidan,amma abu yaci tura,kina cigaba
da gano abinda zai iya vaki wahala. Wannan wacce irin ƙaddara ce.......koma dai
menene kada kowa yaji abinda muka tattauna dake a yanzu,ki barshi a ranki kada ki
fitar"
Daga haka ta kishingiɗa a kan gadonta,da alama ta gama maganar tata.
Jan ajiyayyen numfashi nayi tareda fitowa daga ɗakin na rufe.
Kitchen na nufah na ɗora ruwan zafi,da farko tayi kamar zataci wani abun,maganar da
mukayine tasakata sauya shawara,dan haka nasan a wahale take.
Idan ma abinda nagano gameda itane yasakata yin hakan da ta daina,menene abin
wahalar rashin ganewar,tunda muka haɗu abinda take nunawa tayi kamada wacce take
hora kanta wajen yin abinda bashine a cikin zuciyarta ba,gabaɗaya rayuwarta a wasan
kwaikwayo takeyinta,ciki kuwa harda ƴaƴan ta. A fili ta nuna musu halin ko inkula,a
baɗini kuma sune a ranta har lokacin da numfashinta zai fice,Musamman ma Ahmad,duk
wata damuwar sa da komai nasa tasani,sannan koyaushe cikin kareshi take kota saka a
kareshi daga wani abun,sannan duk sanda aka kawo zancensa inaganin nadama da rauni
a idonta sosai. Wannan za'a ƙira da tsana,soyayyarsa ce a idonta irin na mahaifiya.
To amma ya haka? Mai yake faruwa a wannan kurman gidanne,idan har ba itace take
cutar dashi ba to wanene,duk da itama ban yarda da itah har yanzu ba,amma kuma
zuciyata tana bani,akwai wani wanda yafita dayake aikata waɗannan ayyukan,kuma yake
tilastata akan horon da take bawa jininta bada son ranta ba.
Amma koma waye mai yasa batayi maganinsa ba,kuma ta miƙashi an hukuntashi,ina
matsayinta na wayayyiyar mace kuma mai sani akan shari'ah.
Sashen hajiyah Mammah nayi bayan na kaiwa hajiyah maryam abincin danayiwa
Ahmad,bataci sandwich ɗin bama,iya kunun gyaɗar kawai tasha.
A hanya naci karo da wani soja a ƙofar sashen,yana ɗaya daga cikin masu kulada
security na gidan.
"Am gud morning,please can you send this to hajiyah Mulaifah?"
Yafaɗa yana miƙomin wani akwati irinna package ɗinnan.
Karba nayi kafin nace wani abun har yabar wajen. Banso ba haka na nufi
ɗakinnata,Allah yagani banason duk wani abu dazai dunga haɗani da waccer matar.
Tura ƙofar ɗakinnta nayi bayan na shikenan sashen hajiyah Mammah,ko ƙwanƙwasawa
banyi ba.
A buɗe kuwa yake bata rufe ba.
Wata irin kwanciya tayi akan gadon kaman wata ƴar bori,hararta nayi tareda ajiye
abin akan drawerta,har na juya zan tafi naji maganar ta cikin magagin bacci.
"Ke rainin naki har yakai kishigomin ɗaki kai tsaye kaman wadda muke sharing dake?"
Tsayawa nayi amma ban juyo ba,wai dama idonta biyu?
"Ga waɗannan kayan naɗeminsu kafin ki tafi"
Cije bakina nayi,amma ya zanyi,banason yazamo koyaushe muna samun sabani da itah.
Juyawa nayi wajenda take maganar,a hankali nake takawa har naje gaban wardrop
ɗin,ina buɗewa kaya suka wani sako kai zuwa ƙasa. Saida na tsorita domin banyi zato
ba. Zaro ido nayi ganin kusan duk ilahirin kayanta a cunkushe suke babu tsari.
Wai a hakan zata ƙira kanta mace,kuma maison mallakar wani namijin.
Fitowa nayi da kayan cikin tass nafara jerawa da ɗaɗɗaya.
Wayar tace tayi ƙara,saida tayi ƴar ƙaramar tsuka kafin ta miƙa hannu ta ɗauka.
"Hii padush ykk"
"Ƙalau ke ya akayi jiyanne,abin yayi aiki"
"Hmmm ai nake faɗamiki fiyeda yanda kike zato ma,yace haka ne kam tunda abune da
aka farashi,kuma yayi alƙwarin haɗashi yanzun bazai gagara ba. Yau ma zayyi magana
da Ahmad akan zancen,zuwa gobe kowa zai shaida shirye shiryen aurena da Ahmad"
"Amma bakya ganin shi Ahmad ɗin ya ƙi amincewa"
"Nima nayi wannan tunanin amma hakan bazayyiyu ba,domin Abbah bazai taba daina
yimasa zancen ba idan har ba auren aka yiba,shikuma kinsan wancan karon ma,baya iya
tsallake maganar abban. Dan haka kisha kuruminki ki saurari mai zai faru"
Dariya suke sunata maganganunsu wanda sukayi amanna dasu kuma suke yi musu daɗi..
A yayinda gefe ɗaya kuma ni suke ƙonamin rai fiyeda yanda mai tunani zai tuna,wai
dama matar nan da gaske take,mijina take son mallaka hakan ma kuma ta hanyar
mallakar magani,bawai da son ransa ba?.
Rigar da take hannuna na jefar na tashi na tafi,kunnuwana bazasu iyah jin waɗannan
maganganun ba,in kuma nace zan cigaba da saurarensu to za'a samu cikyakykyen
mishkila.
Ina jinta tanamin magana amma nayi banza da itah nabar sashen.
Kai tsaye sashen hajiya Maryam nayi,saidai tun kafin na shiga nake jiyo maganar
ta,da kuma muryar babban mutum,nasan babu makawa babansu Fatee ne.
"Wai bakida lafiyane naga duk kin sauya,kin rame ba kaman da ba"
"Ohh dama ka damu da hakan,sai yanzu kasani? Kafaɗamin menene yake tafe dakai da
har kazo sashena i yanxu?"
Shuru naji ya gibta,har zan juya na tafi saboda bai dace na zama kullum mai jin
abinda wasu zasuce ba,hakanma kuma sabgar ma'aurata wanda bai shafeni ba.
Turus nayi tareda komawa baya,abinda naji ya faɗa ya shafeni.
"Akan maganar auren Mulaifah da Ahmad ne,tazo tasameni akan maganar jiya da
daddare...kinsan kuma daman abune da har an farashi wancan tsautsayin ya gibta. To
yanzu tunda komai yalafa yakamata a yi auren.
Yanzunnan daga office nake,nazo ɗaukar abune nace barina yi miki maganar,shima
Ahmad munyi magana dashi ɗazu kuma ya nunamin amincewar sa."
"To mai yasa kake faɗamin,a matsayina nawa a wajensa"
"Maryam mai yasa kike hakane,wainikam yaronnan mai ya taremiki ne,da kullum kike
nuna haka?"
"Abban Fatee mai nayi kuma,shin nasake ƙoƙarin kashe maka ɗa ne yanzun,da kake min
wannan zancen. Naji abinda kace,Allah ya taimaka ya kaimu ranar auren,yaushe ka
saka?"
"Wani satinne idan komai ya daidaita,yakamata yayi aure zuwa yanzu,kuma babu
amfanin sake wani shirye shiryen bayan wanda akayi a baya"
"Uhm"
Shine kawai abinda na iya faɗa kafin nabar wajen,nikam mai yasa kullum kunnuwana
sai sun jiyomin zancen wasu ne wanda zai tabamin zuciya?.
Dafa bango nake jikina yana rawa na bar wajen. Itama ta yarda da auren,shima uban
gayyar ya yarda da auren,shikenan daga ƙarshe sun zabi jininsu zasu haɗashi da
ita,dama nasan yafi ƙarfina tun ranar danagano wanene shi,kawai son zuciyane da
yarda da abinda bazai yiyu ba yasa nake ganin watarana zai waiwayeni.
Kukane ya kufcemin mai matuƙar ƙarfi a corridon da zai fitar dani zuwa sashenmu.
Kasawa nayi,na kasa ƙarisawa na gaza,komai yayimin duhu. Nakasa dawowa dashi a
cikin rayuwata,shin dama bana cikin ransa tunda ko kaɗan,da gushewar tunani kaɗai
zai shafeni tass daga cikin kansa?. Dan ban faɗamasa ni wacece ba shikenan koda da
sau ɗaya bazai iya cankar wacece ni ba? Idan ta ɗaukeshi wane uba zan bawa ɗana
kenan,shikenan yanada uba amma kuma tamkar bashida shi_? SANADIN CACA ne yahaɗani
dashi, na tsorata dashi,na ƙyamaceshi amma kuma na daure na amince dashi,na yarda
dashi na taimakeshi na kuma bashi kaina da amanata,batareda na duba mai yayimin a
baya ba kokuma waye shiba a baya. Amma shi mai yasa yanzu yakasa gani na,ya kasa
tuno ni,yakasa karbata a rayuwarsa. Shin mai zanyi nan gaba wanda zai dawo dashi
cikin rayuwata?.
"Wayyo Allah mijina,Allah ka dawomin dashi bada wayona ba kokuma dabarata, zan iya
bin son zuciyata na faɗamasa ni wacece kai tsaye,amma hakan mai zai faru......zan
rushe abinda hajiyah Maryam ta daɗe tana ginawa,zan bayyana ni wacece a idon
maƙiyina. Sannan shima zan sakashi cikin ha'ula'i.
Amma kuma idan na kawar da zuciyata gefe shin zan iya rarrashin zuciyata taga
masoyinta tareda da wata?? Ohh ni Sumaimah naga ta kaina.
SADI-SAKHNA CEH
09035784150
ku tuntubeni domin biyan kuɗinku ko ƙarin bayani.
*SANADIN CACA*
-BOOK 2 (PAID)
Mallakar *SADI-SAKHNA*
09035784150
Bismillahir-rahmanir-raheem
Ki biya kan ki karantamin na biyu dan Allah. ga number ta nan mai son littafi na
ɗaya yayi min magana zan bashi shi kyautane.
Sister's duk wacce batayi anfani da sabulun mg's ba ko kit dinsu inamai shaidamuku
anbarku acan baya domin duk wnd yajaraba mg's sai sanbarka duk wani Mai tantama
Akan kayan gyaranjiki toh tabbas yacire sabulun mg's domin yahadu bakarya
zegyarajiki yafidda dattin fata Dama duk wani matsalan fata duk Wanda kefama da
matsalan fata walau pimples ko spot, sunburn acne,stretch mark dama dukkan wani
prblm yajaraba mg's bi'iznillah komai zaizama labari bayan jikinku yy fresh zaisa
jikinku yy smooth yadinga glowing,gawanda basa San anfani da Mai zaku iya using
😯 wnn new soap din💣ne,😯 bama cika Baki kujaraba
mg's batare da kunbukaci wani Mai bnd
kugane ma idanku domin ance gani yakoriji Kuma siyan daya maida kudi gida
You can check pic👇for the soap reviews🥰
Soap price:4k
maiso yy mgn
08062991549
07046881166
07067210195
Call 08064532391
Instagram:glow_with_mgs
Facebook: mg's skincare
Munatura Kaya kowani gari dayardar Allah Amma delivery is not free
*BOOK 2*
...18...
Saida nayi wanda ya isheni kafin na tashi daga wajen na nufi bakin famfo,fuskata na
wanke wacce tayi ja ta kumbura.
Kai tsaye part ɗinmu na nufa domin na kwanta,abubuwan sunyi mini yawa.
Da Sameer naci karo wanda ya fito daga mota zai shiga cikin gidan dana fito ɗin.
Karo muka kusan yi,hakanne yasa na dan ja da baya ina kallonsa,shima kallon mamakin
yake bina dashi. Bamu taba haɗuwa dashi ba a gidan,kasancewar lokacin dana zo an
turashi wani aiki,idan ya dawo kuma baya daɗewa yake tafiyah.
Ni na ganeshi saboda kamarsu ɗaya da saleem,kalar jikinne kawai da ɗaure fuskar ba
iri ɗaya ba.
Ganin kallon dayakemin ya wuce na misali yasa na raba zan wuce,jinayi yayi min
magana wanda banyi zato ba sam.
"Wacce ke,amma dai ke sabuwa ce a gidannan koh?"
"Uhm"
Shine kaɗai amsata,ohh wata tambayar na kuma jin ya sake jefa min.
"Miye Sunanki"
"Sumaimah"
Daga hakan nayi wufff na bar wajen gudun wata tambayar,nasan zayyi mamakin hakan,in
halinsu ɗaya ma da Mulaifah har yace na rainashi. Amma abinda bana ɗauka shine ƴar
aiki ba baiwa bace,tanada ƴan cinta da kuma ganin dama akan rayuwarta.
Bayan la'asar shine fitowata daga sashenmu,tun ɗazu nake gardama da zuciyata kan
bazan yiwa Ahmad girki ba,amma kuma wani bangaren na zuciyata ya hanani amincewa da
ƙin yin. Koba komai nina ce naji nagani zanyi,sannan kuma bai kamata daga yin ɗaya
na bariba. Koda yake nasan idan yayi aure ma bazan sake ganinsa sosai ba.
Kitchen ɗin na shiga na fara haɗa kayan abincin dazanyi amfani dasu.
Jallop ɗin shinkafah zanyi masa da wake,mai kifi da manja. Ba abincin ƴan gayu bane
amma na marmarine,bansan ko zai ci ba.
Bayan na gama juice kawai na ɗauko masa a fridge na ɗora akan tiren.
Kaina a ƙasa yake nake tafiya wajen dinning ɗin,hankalina kuma baya jiki na
sosai,ya tafi duniyar tunani.
"Mai kike gani haka kina shirin buguwa da table?"
A lokaci guda na dawo hayyacina,na kalli mai maganar kana kuma na sake juyawa na
kalli table ɗin.
"Ohh kayi haƙuri"
"Banine wanda zaki bawa haƙuri ba ƙafarki ce inaga,karki ajiye kawomin nan"
Saida yayi magana nakula ashe ba kayan aikine a jikinsa ba,har yayi wanka ma da
alama,tunda ga nan damshin ruwa a jikinsa.
Kawowa abincin nayi na ajiye a gabansa,daidai lokacin da yake sanja tashar tv.
"Yau ka dawo da wuri"
A hankali nayi maganar,banyi zaton ma zaiji ba.
"Uhm"
Naji yabani amsa.
Daga nan shuru ne ya gibta harna gama zuba masa abincin na miƙamasa.
Karba yayi kafin na ajiye yasaka a gabansa. Yanda ba bata lokaci yafara saka
abincin a bakinsa har saida yabani dariya,amma a yanzu banida wannan mood ɗin.
"Me yake damunki?"
"Ehh!!"
Bansan lokacin dana bashi wannan amsar ba,tambayar tasa ta razanani,ni yake tambaya
wai me yasameni?
"Ehh haka nace mai ya sameki,yau naga yanayinki ya sauya ba kaman kullum ba,bakida
lafiya ne?"
"Ahah babu komai,zan iya tafiya idan baka buƙatar komai?"
Jin shuru baiyi magana ba yasa na ɗaga kai na kalleshi,ashe kallona yake tsawon
lokacin. Kuma kallone mai ɗauke da alamar kulawa,ban taba ganin ya bini da irin
wannan kallon ba sai yau.
Garamm mukaji shigowa cikin falon kaman an jefo bauna.
Ɗaga ido nayi na kalleta cikeda takaici, gabaɗaya wannan kuwa tasan mai ake ƙira da
hankali. Barima na tashi na tafi,domin bazan juri wani tension ɗin ba.
"Ka gama da abincinne?"
Na tambayeshi har Sannan fuskata ɗauke da damuwa.
Ɗaga min kai kawai yayi,har sannan bai daina bina da kallon tambaya ba.
Kwanukan na ɗebe na nufi kitchen,ta gefensa na wuce tana tsaye ta naɗe
hannaye,batamin magana ba bayan hararar dayayimin,nima kuma dama hakan nake so ai.
Juye sauran abincin nayi na wanke kwanukan,tun daga kitchen ina jiyo maganar
Mulaifah,amma dai banajin abinda take cewa sosai.
"Haba D mai yasa kakemin hakane, karka manta fah har an kusa aurenmu wancan abin ya
faru,kasan kuwa irin halinda na shiga. Dana jure sai gashi komai ya wuce.
"Wai nikam banaji ance kinyi aure ba,maiyasa kika kashe shi?"
"Saboda bazan iya zama da wani ba idan bakai bane"
"Shine kawai hujjarki"
Ba kunya ta ɗaga masa kai kuwa.
"Hmmm ki tashi ki barmin sashe,karki ga don na amince da aurenki kiyi tunanin cewar
domin ke na amince,hakan bazai sauya komai ba daga kallon danake miki"
"Karka ce haka D nasan zaka soni idan muka fara zama tare ina ƙarƙashin ikonka."
Daga haka ta tashi tabar falon,duk da maganganun daya faɗamata amma ko kaɗan basu
wani dameta ba,tunda burinta na zama matarsa zai cika.
Da daren ma yau bamu huta ba,ummi sai mita takeyi,gwara suma sunsan ana hakan a
gidan,nida bansani ba fah.
Idan akwai abinda za'a tattauna daman ana ƙiran family meeting irin haka. To ranar
dukka masu aiki zasu haɗu suyi aikin,ayi dinner tare a babban falo kowa ya tafi
bayan an tattauna.
"Mtsww ko akan me za'ayi wannan meeting ɗin kuma oho"
Ummi ta faɗa wacce take zaune a kan kujerar kitchen ɗin..
Kallo ɗaya nayi mata na ɗauke kaina tareda cigaba da zuba fried rice a cikin
warmer.
Muryar inna ladiyo mukajiyo tana shigowa.
"Kun shirya komai da komai kuwa,kowa fah ya hallara yakamata akai abinci zuwa
yanzu"
Cikin sauri na ƙarisa zuba abincin na ɗauka na fita.
Kaina a ƙasa na ajiye abincin a tsakiyar table ɗin.
Suna zaune a can tsakiyar falon,ban da hayaniya babu abinda sukeyi.
Dama haka sukeda ɗan yawa. Amma duk yawanci ƴan uwan hajiyah Mammah ne,sai ƙanwar
babansu wacce take aure a maiduguri da ƴaƴan ta manya haka,Hajiya Aina'u sunata
hira itada Maimuna.
Sai Fatee kuma da suke kallon abu a waya itada wacce naji ƴar hajiyah Aina'u ce
Muneerah.
Bayan mun gama jejjera komai da ɗaɗɗai da ɗaɗɗai suka fara zama a dinning ɗin.Wajen
ya cika har Alhj Aliyu ma yazo da hajiyah Mammah.
Kowa sai gaisheta yake ana mata ya jiki,saboda ƙafarta tana ciwo abinka da jiki ya
sha miya.
"Ahh how sweet,ba'a tabayin family meeting da zayyi min daɗi ba sai wannan"
Mulaifah ce ta faɗa wacce take zama a kujerar da babu kowa akai.
Blue material ne a jikinta yanata sheki,kaman wanda aka cemata yaune bikin.
Bayan an zazzauna iya manya masu wayo ne kawai a wajen,ƙananan yara kuma inna
ladiyo da mai aikin hajiyah Mammah inna kareema sun tafi dasu.
Shuru wajen yayi naga kowa ya juya yana kallon ƙofah,nima waiwayawa nayi ina zubawa
hajiyah Maryam abinci.
Caraf idona ya sauƙa a cikin nasa,don tunda ya shigo wajen idonsa akaina yake.
Inda nake ya nufo kai tsaye,mai kuma zayyimin ya taho wajena.
Kujerar danake gabanta naga yana shirin ja,hakan yasa na jamasa ya zauna kana na
matsa. Fuskar mutanen wajen na kalla,dukkansu kowa yayi mamakin zuwan Ahmad wajen
da alama,banda Alhaji Aliyu dakuma Mulaifah wacce take ta washe baki kamar gonar
auduga.
Plate ɗin gabansa na ɗaga zan saka abinci,wani kallo yayimin nasan na gargaɗi
ne,amma sai nayi kamar ban ganshi ba.
Zuba masa nayi na tura gabansa,haɗa ido mukayi amma bansan ya akayi ba na samu
kaina nuna masa babu komai da idona.
Sauƙar da kai yayi tareda jan abinci gabansa kamar wanda akayiwa yaro dole.
Duk wajen babu wanda ya kulada abinda ya faru sai hajiyah Maryam,Saleem da kuma
Sameer.
A tare nida ummi muka bar wajen,ganin yanzu lokacin sune na tattaunawa.
"Kai nifah masu kuɗi suna bani mamaki,to shi wannan zama a ci abincin menene
amfaninsa ne?"
Ƴar dariya nayi kafin nace.
"Uhm kowanne ɗan adam yanada tsarin yanda Allah yayi masa rayuwarsa ummi,su wannan
ce hanyar da suke bi wajen haɗuwa da ƴan uwansu,bakya ganin waccar ƙanwar babannasu
har daga maiduguri tazo?"
"Uhm ummi dan Allah zoki kai wanann yarinyar tana ta kuka mana"
Lokaci guda ta haɗe fuska,
"Haba inna ladiyo kinsan fah banason shiri da yarannan,ita ɗin menene bazata rike
yarinyar nan,su waɗannan masu kuɗin malalata ne"
Kallon yarinyar nayi wacce take ta tsala kuka gata ƙarama. Da kuma ummi wacce take
zuba mita.
Kodan nima uwa ce,haka kawai na tsinci kaina da jin tausayin yarinyar.
"Inna kawo ta na kaita,tanata kuka bakinta har ya bushe"
Daidai shigata cikin falon najiyo muryar Alhaji Aliyu.
"Dukka nayi magana dasu kuma sun amince,kuma tunda ba abune na fari ba,kuma akwai
halin yin na yanke wani satin za'a ɗaura musu aure"
"Sati ɗaya yayi kaɗan,a matsayina na matar gidannan kuma mai iko da komai to ban
yarda ba"
Kowa kallon hajiyah Maryam yayi,jin yadda tayi maganar a dake.
"Meyasa zakice haka,menene dalilinki na ƙin amincewa"
"Maimuna ta yimaka zancen akwai wanda suka daidai ta zaizo wajenka,sai kace sai
kayi tunani,haka Fatee kafi kowa sanin soyayyar da suke da Sadeeq amma baka bawa
abin hankalin ka. Meyasa sai wannan da bawani damuwa yayi da abinba kake ƙoƙarin
saishi zakaga kawai yayi iyalansa?"
Sakin baki Alhaji Aliyu yayi,ya rasa meyasa hajiyah Maryam take masa irin wannan
tsanar,yana zure cin zarafinta in suna su kaɗai amma a bainar jama'a abin da cin
rai.
Cikin fushi Aina'u ta ajiye cokalinta tareda fuskantar hajiyah Maryam..
"Wai Maryam mai yake damunki,meyasa bakya iya boye zafin kishinki da hassadarki
akan rayuwar Ahmad,kodan saboda kinga shine babba ba ƴaƴan ki ba shiyasa?"
Ƴar dariya hajiyah Maryam tayi kafin tace.
"Baƙin ciki da kishi,na me kenan. Inda ɗansa ne shi da saiki cemin zanyi kishi
kokuma nayi baƙinciki,amma babu wanann tunda ba ɗansa bane."
"What maryam wannan wane irin shirme kikeyi haka?"
"Shirme haka kike gani shirme nake? Ahmad ba ɗan Alhaji Aliyu bane, Maimuna itace
ƴarsa tafari,idan kuma baki yarda ba ga nan uwarki da kuma yayannaki ki tambayesu.
Dan haka batun nayi masa baƙinciki ki ajiyeshi a gefe,in kinga yaci gadon Alhaji
Aliyu to ƴaƴana ne dukka suka mutu"
Tana gama faɗin hakan ta tashi daga kan kujerarta hankalin ta kwance ta bar wajen.
Idone ya koma kan Ahmad,wanda ya rumtse cokalin dayake hannunsa ƙam kaman zai
maidashi cikin hannun,bakinsa yana rawa ya kalli AM Aliyu da jajayen idanuwa.
"Abbb......abba shin dagaskene abinda matarka take faɗa?"
Runtse ido shima AM Aliyu yayi,saboda bashida ƙarfin gwiwar kallon idon Ahmad ɗin
ya tabbatar masa da abinda yakeson sanin.
Kuka hajiyah Mammah ta rushe dashi tareda saka gefen zaninta tana sharewa.
Tunda naji abinda hajiyah Maryam ta faɗa na zama tamkar gunki a wajen,shin ni
wannan matar wacce iri cene.
Gaba da gaba muka tsaya da taxo zata fita daga falon. Wani shu'umin murmushi
tayimin bayan ta dafa kafaɗa kafin tabar wajen.
Juyawa nayi nabi hanyar data bi da kallo.
Bangazata naji mutum yayi yafice daga wajen,iya bayansa kawai na samu gani,tafiya
yake kaman zai tashi sama don sauri..
Ohh dagani har shi sai wahala muke sha a bangare mabambamta,shin yaushe komai zaizo
da saukine?.
Hankalina yayi gaba ji nayi an fizge yarinyar data ke hannuna tana kuka.
Hanyoyi biyu na kalla wanda suke hannun riga.
Wajenda Ahmad yayi da kuma wajenda hajiyah Maryam tayi.
Shin ita zanbi naji mai yake faruwa,kokuma shi zanbi domin na tausheshi akan halin
da yake ciki?
Ku fadamin a comment shin wacce hanya kuke ganin yakamata tabi a ciki?😄😄
SADI-SAKHNA CEH
09035784150
ku tuntubeni domin biyan kuɗinku ko ƙarin bayani.
*SANADIN CACA*
-BOOK 2 (PAID)
Mallakar *SADI-SAKHNA*
09035784150
Bismillahir-rahmanir-raheem
Ki biya kan ki karantamin na biyu dan Allah. ga number ta nan mai son littafi na
ɗaya yayi min magana zan bashi shi kyautane.
Sister's duk wacce batayi anfani da sabulun mg's ba ko kit dinsu inamai shaidamuku
anbarku acan baya domin duk wnd yajaraba mg's sai sanbarka duk wani Mai tantama
Akan kayan gyaranjiki toh tabbas yacire sabulun mg's domin yahadu bakarya
zegyarajiki yafidda dattin fata Dama duk wani matsalan fata duk Wanda kefama da
matsalan fata walau pimples ko spot, sunburn acne,stretch mark dama dukkan wani
prblm yajaraba mg's bi'iznillah komai zaizama labari bayan jikinku yy fresh zaisa
jikinku yy smooth yadinga glowing,gawanda basa San anfani da Mai zaku iya using
😯 wnn new soap din💣ne,😯 bama cika Baki kujaraba
mg's batare da kunbukaci wani Mai bnd
kugane ma idanku domin ance gani yakoriji Kuma siyan daya maida kudi gida
You can check pic👇for the soap reviews🥰
Soap price:4k
maiso yy mgn
08062991549
07046881166
07067210195
Call 08064532391
Instagram:glow_with_mgs
Facebook: mg's skincare
Munatura Kaya kowani gari dayardar Allah Amma delivery is not free
Hayaniya ake tayi a cikin ɗakin taron,kaf cikinsu babu wanda yayi tunanin a haka
abin zai kasance. Kowa yana faɗin albarkacin bakinsa.
Yayinda Sumaimah kuma aka barta a tsaye tamkar gunki a kan mashigar wajen.
Kallon kallo take bawa bangaren guda biyu,da alama ja'inja take da ƙwaƙwalwarta kan
wacce hanya zatabi. Hanyar sashen hajiyah Maryam ta nufah,domin a yau kam tanada
buƙatar son jin menene maƙasudin faruwar komai,menene ainihin tarihin abinda yake
faruwa?.
Har takai daidai shiga sashennata,saikuma wata zuciyar ta tuna mata mijinnata,shin
a wanne hali yake a yanzun,gashi bashida kowa a gidan bare ya waiwayi
lamarinsa,kuma a wannan yanayin dayake ciki yana buƙatar mai zama a kusada shi.
Juyawa tayi da akalar tafiyar tata zuwa sashennasa. Tafiya take ranta cikeda
abubuwa masu dama.
Kai tsaye ɗakinnasa ta wuce,a bakin ƙofar dakin ta tsayah tana kallonsa,yana zaune
a tsakiyar gado ya saka gabansa can. Daga bayannasa mutum na iya gano yanda
ƙirjinsa yake sama yana ƙasa.
Jan ajiyar zuciya tayi kafin tafara takawa a hankali zuwa inda yake.
Tunda ya tambayi Abbansu yaga yayi shuru,hasalima yakasa haɗa ido dashi,hakan ya
tabbatar masa da abinda hajiyah Maryam tafaɗa dagaske takeyi. Wani duhu
yagani,yayinda duniyarsa ta tsaya na wasu daƙiƙu,shi ba ɗan Alhaji Aliyu bane,to
kenan wanene ubansa,shegene shi ina mahaifiyar sa,an ce ta mutu,waye mijinta
kenan,kokuma dawa tayi tarayyah,ko tsintoshi sukayi kai.
Wannan kalaman sune suke ta yawo a ƙwaƙwalwarsa har ikon Allah yakaishi ga
sashensa,babu cire takalmi haka ya hau kan gadonnasa, ƙirjinsa ya riƙe gam jin yana
yimasa wani hawa da sauƙa kaman ana famfo.
Jinsa yayi tamkar shi kaɗaine a duniyar,bashida kowa ballantana yasamu wanda zai
zauna dashi a wannan zazzafan yanayin.
Hawaye ne zafafa suka fara kwaranyowa daga cikin idanunsa. Rayuwarsa kullum cikin
karbar baƙuncin sabon abu takeyi,shin yaushe wannan abin zai ƙare?.
Tsayawa yayi da tunanin jin hannu ya daga bayansa,wanene ya tuna dashi yazo wajensa
a wannan halin,a saninsa dai Sadeeq bayanan kuma bai san mai yake faruwa ba.
"Lafiya kake? Karka damu komai zai wuce sai labari,hakan jarabawa ce wanda idan ka
jure ka cinyeta zakaga sakamako Mai kyau"
Sumaimah ce take yimasa maganar cikin sanyayyiyar zuciya mai cikeda alamar
rarrashi,duk da itama tana cikin damuwar amma yanda yakeji tasan yafi nata.
Kanta ta ɗora a bayansa tana cigaba dayimasa maganganun da tun baya fahimta har
yafarajin mai take faɗa.
Zogin da zuciyarsa take masa ne yasashi sakin wani wahalallen nishi,jij hakan yasa
Sumaimah dawowa gabansa da sauri.
Cikeda damuwa take kallon shanyayyun idanuwansa,masu cike da abubuwa kala kala.
"Ƙirjinahhhh"
Shine abinda ya tsinci kansa da furta mata a hankali.
Hannunta tasaka a saitin ƙirjinnasa kai tsaye bata kawo wani abu a ranta,idon da
zare jin yadda take bugawa da matsanancin gudu fiyeda na kowanne lafiyayyayen ɗan
adam.
"Tana bugawa da ƙarfi,yakamata na sanarwa Saleem da sauri"
Ƙoƙarin sauƙa take akan gadon yayi saurin riƙo hannunta.
"Karki ƙiramin kowa,banason kallon wani daga cikin ahalinnan kowaye shi a yanzu"
Kallonsa take da alamar tausayi,kaman ƙaramin yaro haka taga ya koma mata a
lokacin. Batasan sanda zuciyarta ta ɗebeta da rungumeshi ba. Ga mamakin ta kuma sai
taji shima ya maryar mata da martani.
Duk da cewar yasan kusancinta dashi a lokacin ba abune mai kyau ba,amma kuma
samunta a gefennasa ya rage kaso mai yawa na damuwarsa,saboda abune da bai fiye
samu ba. Shiyasa ya tsinci kansa da kasa hanata,saima sake sakemata da yayi.
Sun daɗe a haka rungume da juna kafin yasaketa tareda cikin sanyin jiki.
Kunyace takamata ta dawo hayyacinta data tuna mai ta aikata,duk da tasan hakan ba
laifi amma kuma shi zaiji ya aikata laifin a ransa..
Saurin sauya iskar wajen tayi tareda sauƙa daga kan gadon. Hanyar banɗaki ta nufah
da sauri tana magana.
"Uhm barina haɗamaka ruwa kayi wanka gumi kakeyi,kafin ka fito kuma na haɗamaka
shayi"
Ƙofar data rufe yabi da kallo tareda jijjiga kai a hankali. Ya rasa meyasa yake
idan yana tareda itah sai yarasa nutsuwarsa da taka tsantsansa,he can't imagine wai
ya rungume mace kuma ba muharramarsa ba,sannan baiji dana sani sosai a ransa ba.
Kodai kai bai warke ba daga halayyar daya gamu da ita a baya? Amma kuma ai bayajin
son yin komai banda wannan ɗin.
Bayan ya fito daga wankan ƙaramar riga yasaka da kuma wando 3 quater,ganin bai
ganta a ɗakin ba yasa ya fito falon,nan ma batanan,amma yana tsaye yaga ta fito
daga kitchen hannunta ɗauke da kofi.
A gaban kujerar dayake zama kullum ta ajiye,itama kuma ta zauna a gefe.
Har tagama komai yana nan tsaye a bakin ƙofar ɗakinsa yana kallonta,shidai yasan
wani abu yakeji gameda wannan matar a cikin ransa.
Da hannu ta nuna masa yazo ya zauna,ganin ya tsaya kaman wani soja (ohh dama
sojanne ashe).
"Ciwon ƙirjinnaka ya lafa ne kokuma na samomaka maganin?"
Ajiye cup ɗin hannunsa yayi tareda yin ɗan ƙaramin murmushi.
"Idan nace ki nemo min maganin a ina zaki nemo?"
"A inda yake zan nemo"
"Wanne magani zakice a baki?"
"Uhmm maganin ciwon zuciya idan akayi mata abinda ba daidai ba"
Maganar tata ce ta bashi dariya,agogon ɗakin ya kalla.
"Dare yayi yakamata ki tafi"
"Uhm amma zaka iyah........"
"Am not a child Sumaimah,nasaba da irin wannan yanayin zan kulada kaina. Nagode da
kulawarki,amma kusancin mu yana yawa,kada ya wuce mizani"
Ɗaga masa kai kawai tayi,domin batada tacewa a yanzun.
Rakata yayi har bakin ƙofa ta fita shikuma ya rufe.
Dare yafara kam,don goma ta wuce,saidai akwai farin wata daya haska gidan.
To kuma zaku kwana a zaunen mu fara,kokuma zakuyi bacci inyaso gobe sai mu cigaba.
SADI-SAKHNA CEH
09035784150
ku tuntubeni domin biyan kuɗinku ko ƙarin bayani.
*SANADIN CACA*
-BOOK 2 (PAID)
Mallakar *SADI-SAKHNA*
09035784150
Bismillahir-rahmanir-raheem
Ki biya kan ki karantamin na biyu dan Allah. ga number ta nan mai son littafi na
ɗaya yayi min magana zan bashi shi kyautane.
Sister's duk wacce batayi anfani da sabulun mg's ba ko kit dinsu inamai shaidamuku
anbarku acan baya domin duk wnd yajaraba mg's sai sanbarka duk wani Mai tantama
Akan kayan gyaranjiki toh tabbas yacire sabulun mg's domin yahadu bakarya
zegyarajiki yafidda dattin fata Dama duk wani matsalan fata duk Wanda kefama da
matsalan fata walau pimples ko spot, sunburn acne,stretch mark dama dukkan wani
prblm yajaraba mg's bi'iznillah komai zaizama labari bayan jikinku yy fresh zaisa
jikinku yy smooth yadinga glowing,gawanda basa San anfani da Mai zaku iya using
😯 wnn new soap din💣ne,😯 bama cika Baki kujaraba
mg's batare da kunbukaci wani Mai bnd
kugane ma idanku domin ance gani yakoriji Kuma siyan daya maida kudi gida
You can check pic👇for the soap reviews🥰
Soap price:4k
maiso yy mgn
08062991549
07046881166
07067210195
Call 08064532391
Instagram:glow_with_mgs
Facebook: mg's skincare
Munatura Kaya kowani gari dayardar Allah Amma delivery is not free
*BOOK 2*
...20...
Sunana Maryam A.M Abubakar Rimi,ni kaɗaice ɗiya tall a wajen mahaifina mace,sai
ƙannena maza guda biyu.
Duk da yanda na faɗamiki wannan muƙami da mahaifina keda shi,amma sam mu a wajenmu
tamkar da babu yakene,domin bamuda yawan haula na dangi,ga mahaifiyarmu ta rasu a
haihuwar Mujaheed ƙanin Taheer,tun bayan rasuwarta abbanmu bai ƙara aureba,haka ya
zauna dagamu saishi sai kuma Wata mai kuladamu Anty Mommy.
Cikin kaɗaici muka tashi da rashin iyaye,domin abbammu baya zama a gida,saboda
babban muƙamin daya samu a ƙarancin shekaru,sannan aikine na sojoji,shiyasa baya
zaman gida sosai. Domin wani lokacin sai yayi sati uku ma baya ƙasar.
Rigima irinta yara duk bamuyi shi ba,koyaushe daga makaranta sai makaranta,in
kinganmu a gida to da daddarene.
Ta inda Allah ta taimakemu shine da muka samu nanny mai mutunci da kuma tausayi a
garemu.
A haka kwanci tashi cikin wanann halin har nayi graduation a secondry,lokacinne
kuma aka kai Taheer makarantar sojoji bayan ya gama juniour school,shikuma Mujaheed
yana jss one.
Kasancewar inada ilimi sosai mashaallah,kuma dama tsawon zamannawa a gidannamu
karatu kawai nakeyi har na girma nayi wayo.
Saina roƙi abbanmu akan yabarni na tafi law school,bai hanani ba,hasalima yaji
daɗin hakan sosai.
Cikin ƙanƙanin lokaci aka shiryamin komai da komai na tafiya law school a nan
abuja.
Kasancewar abbah baya zama sosai,kuma yanzu na tafi makaranta,kuladani zayyiwa anty
mommy wuya,sai abban mu ya tamƙa kulawata a hannun Gen Hammah,wanda shine
mataimakin abbanmu,duk da cewar yafi abbanmu a shekaru,kaman yanda na faɗamiki
ɗaukaka ce tasameshi a ƙarancin shekaru.
Abbah Hamma a lokacin yanada ƴaƴa guda biyar,akwai Muhammad,sai Aliyu sai
Aina'u,sai Mariyah da Zainab.
Muhammad shine babba,kuma ɗan hajiyah Fatima,ƙanwarsa ɗayace Zainab.
Saikum Aliyu shine mai ƙanne biyu,Aina'u da Mariyah,su kuma ƴaƴan hajiyah Mammah
ne,kuma itace amarya a wajen Abba Hamman.
Zaman lafiyar dana gani a gidan farkon shigata da kuma yanda yaran suka tashi abune
da zai burge duk wanda yagani,musamman ma irina da sukayi rayuwa da ƙaɗaici da
rashin iyaye.
Bayan shekara Biyu da fara makaranta ta,abbanmu ya ɗebe Taheer da Mujaheed suka
koma England da zama,babu yanda banyi ba akan ya tafi dani,amma firr yaƙi,a cewar
sa ina mace bai kamata na bishi ba musamman da lokacin karatuna yafara ɗan nisa.
Haka dole inaji ina gani na hakura suka tafi,wanda kuma nasan bazai wuce da saka
hannun Hajiya Mammah ba,don lokacin dana fara zuwa gidan ta jani a jiki sosai,amma
ni ban fiya shiga sashenta ba,saboda bama shiri da Aina'u,nafi shiri da zainab. Ita
kuma mariya lokacin ƙarama ce.
Kayana na tattara daga hostel na koma gidan Abbah Hamma da zama,hajiyah Mammah taso
na zauna a sashenta amma naƙi,badan komai ba saidan abu biyu,. Na farko Banason
faɗan da muke da Aina'u,duk tsiya ita gidansu ne,bai kamata ace nazo ina faɗa da
ƴar masu gida ba kullum,sai kuma magana ta biyu Aliyu yana sona,nikuma har sannan
ban bashi amsa ba gaskiya,bazance bana sonsa ba,bazan kuma ce ina sonsa ba,irindai
kaji mutum yana burgeka amma ba so ba.
Saidai shikuma a nashi bangaren soyayya yake nuna min a gaban kowa,hakan sai ya
fara takurani,shiyasa na sauƙa a sashen hajiyah Fatima dana dawo gidan da zama.
A tsawon dawowata gidan bamu haɗu da Muhammad ba,saboda shi yana England wajen
abbanmu a can yake aiki a wajensa,yawanci mutane ma cewa suke shine mai gadon
abbanmu a wajen aiki,domin yasha cewa Abbah Hamma ya bashi shi,saidai kawai yayi
dariyah.
Bayan shekara huɗu da fara makaranta ta Allah ya kawomu gamawa,a lokacinne na roƙi
abba yazo shida ƙannena dukka.
Duk da cewar dama yana xuwa wani lokacin,kokuma in anyi hutu nina je,amma hakan
baikai a ce dominni zasuzo ba.
Tareda dukka gidan aka haɗu ana tayani murna da kuma shirye shiyen gamawar tawa.
Zuwa lokacin na zama ƴar gida sosai,tun inajina tamkar ba ɗaya daga cikinsu ba,har
yazamto yanzu in ba mutum yasani ba bazaice niba ƴar gidan bace.
Sauri nake hadda gudu gudu na nufi Wajen Zainab,saboda ance min ta karbo mana
dinkinmu da zamu saka.
Jinayi na bugu da mutum,ɗagowa nayi muka haɗa ido da Muhammad,ƙifta ido nayi shine
kuwa,kuma fah shine.
To ko su Abbah yabiyo shima domin zuwa murnar gama makaranta ta kai,kai anya kuwa.
Mutum ne shi mai sauƙin kai da kuma mutunci,amma fah akwai miskilanci dayin
sha'aninsa daya shafeshi,bai fiya shiga harkar mutum ba in bawai an tsoma shi ba.
"Ahh yah Muhammad tare kuka......."
Tun kafin na gama maganar ya ɗagamin kai yana murmushi,nasan ba lallai yabani amsa
ba,murmushin shine amsar,kai mutuminnan yana bani a jikina,duk sanda na ganshi rasa
nutsuwata nakeyi da kuma guntun hankalina. Duk da ma saina ɗaga ido nagano
shi,saboda yanada tsawo,nikuma ga ƙanƙantar jiki kaman ruwan aski.
Daƙyar na janyo ganina daga kansa na rabashi na wuce zuwa wajen abba nah da
ƙannena,nabar batun ɗinki tunda naji ance sun iso.
Da tsalle na faɗa kan abban ina kuka,wanda kowa yasan na farincikin ganinsa ne,a
tsaye suka a ƙofar gidan da Abbah Hamma,ina jinsa yanamin dariya sai sakaliya,nidai
shuru nayi,Allah yaga ai ina ƙoƙari,ace mutum yana rayuwa wai kuma ƴan uwanshi suna
wani wajen daban.
Gaisawa mukayi da sauran ƴan uwannawa, kafin daga bisani muka shiga ciki anata
murna.
Mun zo shiga cikin gidan naji zainab taja hannuna zuwa garden,tambayar ta nake mai
yake faruwa amma sai jana take tana dariyah.
Bayan mun isa sakinta nayi tareda buɗe baki saboda mamakin abinda nagani. Da balloo
akayi amfani wajen haɗa sunana da kuma murnar gama makaranta ta..
Abin ya burgeni matuƙa,har bansan lokacin da yah Aliyu yazo inda nake ba.
"Ina miki murnar gama karatunki maryam,sannan kuma dan Allah a yau ɗin ki karbi
so........."
Tun kafin yagama naji mai zaice zainab tazo akan wai ana kirana a cikin gida,da
alama sun gama shirya walimar kenan.
Haka na juya batareda naji mai zaice ba nabi bayanta.
Riga ta da aka ɗinka saboda ranar,babu taron mutane sosai,amma wajen yayi kyau babu
magana,a dai irin dai zamaninmmu kam abin ya ƙayatar.
Bayan an gama komai magana abba nah ya farayi,ganin yanada muhimmanci sosai yasa
dukka kowa yayi shuru domin muji mai zaice.
Bayani akan murna da kuma farincikin gama makaranta ta,sannan ya miƙa gaisuwa ga
Abbah Hamma,bisa rikeni dayayi amana har zuwa lokacin.
Bayan nan kuma hannun Abbah Hamma ya riƙe kaman mai shirin roƙonsa wani abun,abinda
ya faɗane yasaka dukkan mutanen wajen zare ido,bama kamanni da kuma zainab da
Aliyu.
"Abokina komai dana roƙeka kayimin harda wanda banyi zato ba,samun amini irinka sai
an tona,nagode nagode da karamcinka a gareni."
"Haba Abbakar miye kakeyi hakane,a tunanina kaman mun wuce wannan abin an zama
ɗayah."
"Ehh to in hakane,ina neman alfarmar kabawa ɗana ƴar taka mana aure"
Abbana yafaɗa yana nunani da kuma Muhammad.
Dukka wajen kowa shuru yayi cikeda mamaki,amma babu wanda yace komai ana jira aji
ta bakin Abba Hamma.
"Indai hakane babu matsala na bawa Muhammad ƴa ta Maryam,Allah ya sanya alkhairi a
aurensu ya basu zuri'ah ɗayyaba. Kenan itama zaka janyeta can wajenka koh"
Dariyah abba nah yayi tareda cewa,
"Ba komai saina bar maka Taheer anan ai,dama shine mai son yin aiki anan"
To shikenan abu yayi kyau Allah ya ƙara haɗa kanmu dana ƴaƴan mu."
Haka taron ya ƙare,wasu yayi musu ɗaɗi,wani yayi musu bazata,yayinda Aliyu shida
hajiyah Mammah da ƙannensa duniyar tayi musu duhu,yazamana gani suke tamkar an ware
sune a rayuwar gidan. Amma banda Aliyu,shi abinda yasakashi cikin wani yanayi ganin
yanda soyayyarsa ta subcene akan idonsa,kuma hakanma ba mallakin kowa nake shirin
komawa ba sai dan uwansa na jini.
A bangaren hajiyah Fatima itama taso ƙin amincewa,saboda ta kulada Aliyu yana
sona,amma kuma batada ikon hakan musamman ma da su Abbah sun riga sun yanke
hukunci,nima kuma a lokacin naso kaina,ban kulada halinda Aliyu zai shigaba,nabi
zabin zuciyata wato Muhammad ɗin.
A ƙurarren lokaci aka saka bikin,sai murna nake zan koma kusada mahaifina da
zama,shikuwa Muhammad da akayi masa zancen babu yabo ba fallasa ya amince.
Shirye shiryen biki aka fara,inda a ranar wata juma'a aka ɗaura aurenmu nida
Muhammad. Aliyu bayanan aka ɗaura auren,a cewarsa an turashi aikine ƙasar
spain,amma a zahiri kuma shine da kansa ya cika neman aikin saboda yayi nesa da
gida,a lokacin danaji ance zai tafi ana gobe ɗaurin aurenmu naji tausayinsa
sosai,saboda ni shaida ce irin son dayakemin. Amma kuma bazan iya tsaidashi ɗin ba
saboda banada abinda zan bashi,kai na kokuma wata soyayyar,babu mai yiwuwa a ciki.
Wanda suka san soyayyar da Aliyu yakeyimin haka suka manta,aka cigaba da hidimar
bikina.
Bayan an ɗaura auren bamu tafiba sai a washagari tukunna..
A lokacin nafara kunyar hajiyah Fatima da kuma Mammah,ganin da gaske fah matsayina
ya sauya a gidan,nazama surukarsu.
A daren mun ɗau lokaci da tsawo muna kuka nida zainab,ganin da gaske fah rabuwa
zamuyi na tafi.
Kyauta mai tsoka matan gidan sukayimin,harda Abbah Hamma ma. Tareda Mujaheed muka
tafi,aka bar Taheer anan.
Shikuma Abbah da mijinnawa jiya suka tafi,akan za'amin cuku cukun wajen aiki da
kuma cigaba da karatu.
(Ba anan gizon yake saƙaba,nan hasken dana samu a rayuwata kenan kafin duhu ya
lullubeni wanda bai yaye ba daga duniya ya har yau)
SADI-SAKHNA CEH
09035784150
ku tuntubeni domin biyan kuɗinku ko ƙarin bayani.
*SANADIN CACA*
-BOOK 2 (PAID)
Mallakar *SADI-SAKHNA*
09035784150
Bismillahir-rahmanir-raheem
Ki biya kan ki karantamin na biyu dan Allah. ga number ta nan mai son littafi na
ɗaya yayi min magana zan bashi shi kyautane.
*BOOK 2*
...21...
Kinsan mai na tarar bayan naje ƙasar england,Muhammad yanada mata,juliat amma ta
musulunta ta koma Amina,saboda soyayyarsa yasa ta zama ɗaya daga cikinmu,shikuma ya
aureta ne yasaka ta a ƙarƙashinsa gudun kada ta sake komawa gidan jiya..
Baƙar fatace ƴar garin benue,karatu ya kaita can ta haɗu da Muhammad,anan ta
ƙwadaitu da musulunci amma saidai in zai aureta yazama tana ƙarƙashin ikonsa,saboda
iyayenta bazasu karbeta ba.
Daya zo wa abbanmu da zancen bai ja ba ya amince masa,ganin niyyarsa na inganta
rayuwarta.
Lokacin danaje naga part biyu a gidan tana ɗaya naji tsoron zama da itah,kuma nayi
mamakin yanada aure ba'a sani ba,ashe mu yaran gidanne kawai bamu sani ba.
Bayan sati ɗaya na zuwannawa na saki raina ,ganin tanada mutunci sosai,sabon
addinin nata kawai tasaka a gaba sai kuma karatunta na medicine da takeyi.
Nima a makarantar da take na samu gurbin yin masters wato oxfort.
Muhammad ne yake ajiyemu a makarantar kana ya wuce wajen aiki.
Zamane mukeyinsa na mutunta juna,kowa yana harkar gabansa,a bangaren mijinmu kuma
muna samun soyayyar sa fiyeda tunanin mai tunani,domin shiɗin mutum ne da sai an
bincika kafin a samu tamkarsa wajen bawa mutum haƙƙinsa.
Kwanci tashi har munyi shekara guda da aure,ita kuma amina tayi shekara biyu.
A lokacinne kuma aka zo auren zainab,murna ta komawa ciki tayi,saboda a lokacin ba
dama naje ina project na gamawa ta.
Sai Muhammad ya tafi shida Amina,dama tunda tayi aure bataje ba.
Satinsu ɗaya suka dawo,zainab har kuka tayimin akan banje ba,amma sai haƙuri na
bata.
Tare suka dawo da hajiya Mammah akan zatazo taga ɗakinmu. Itakam daman hajiya
Fatima bazata zo ba tana kunyar dan fari irinna fulani.
A ranar da suka dawo na tashi da zazzabi, dan ma Muhammad na ɗakina,domin nasha
wahala sosai da daddare,amai ga zafin jiki.
Washagari da safe ya kaini asibiti,Amina Da hajiya Mammah basu sani ba suna sashen
Aminan.
Gwajin farko aka cemin inada ciki na wata uku,nayi murna sosai musamman dana shafe
shekara guda daman babu komai..
Shima Muhammad yayi farinciki fiyeda ni,ganin bayan shekara biyu da aure zai samu
ɗa ko ƴa.
Da safen Muhammad ya tashi su hajiyah Mammah ya faɗamusu,itakam Amina ana faɗamata
a take ta rungumeni tana lelleƙani,har ta bani tausayi,saboda ni kaina shaidace
akan son yaranta,don abinda take karanta ma kenan a bangaren karatunta.
Itama hajiyah Mammah kabbara tayi tareda ɗaga hannu sama.
Waya Muhammad ya ciro akan zai ƙira gida,amma hajiyah Mammah ta hanashi,a cewarta
ya barta takai wanann albishir ɗin gida.
Da farincikinsa ya amince da maganar ta.
Tun daga wannan lokacin nafara ganin gata a wajen Muhammad,Amina kuwa ko ban nuna
alamar komai ba saita gwadani. Satin hajiyah Mammah daya ta tafi gida.
A haka nikuma na cigaba da rainon a cikina,akan cewar idan cikina yazo haihuwa zan
koma gida na haihu. Naji daɗin hakan sosai lokacin danaji Muhammad ya faɗa.
A ranar dana shiga wata na tara muka kamo hanyar dawowa gida,murna a wajena bazata
boyu ba.
Bayan mun sauƙa mun kai kaman minti biyar ba motar datazo daukarmu,nikamma harna
gaji,saida suka samamin kujera na zauna,Amina sai sannu takeyimin.
Munan nan zaune wata mota ta zo baƙa,wani mutum haka gajere ya fito daga motar,
wannan kuma wanene,bansanshi a gidan ba ko sabon driver ne.
Nidai tun kafin su ɗakko kayanmu na ja jiki zuwa cikin motar,dama na gaji.
Tafiya muke amma maimakon hanyar gida sai naga suna wani waje daban,Muhammad ne ya
fara ƙoƙarin yiwa drivern magana,amma sai ya shaqa masa abu a hanci.
Ganin haka yasa muka saka ihu nida Amina,domin abin ba ƙaramin razana mu yayi ba.
Duhune ya fara lullube ganinmu,yayinda hankalin mu yake neman hanyar fita daga
cikin kanmu.
Kafin idona ya ƙarisa rufewa naga drivern ya saka facemask,yana kuma magana da wani
ko wata a waya.
Ruwa aka watsamana,shine sanadiyyar buɗe idanummu muka ganmu a cikin wani cell.
Wajen kaman kango yake,amma a rufe kirif domin badan hasken da aka kunna na za'a
samu duhu a wajen..
Jijjiga ƙarfen bakin ƙofar nake ina kuka tareda ƙiran Muhammad da zainab,a zatona
basa wajen,sai can bayan wani ɗan lokaci tukunna naji tarin Amina,ƙiran sunanta
nafarayi sai can ta amsamin a galabaice,mai suka mata? Ina Muhammad yake shi.
Kafin na samu mai bani amsa naji takun sawun mace yana tahowa.
Wata mata ce ta rufe kanta da baƙin ƙyalle,bana gane wanne irin kallo takemin
saboda bana ganin fuskarta sosai..
Batayi min magana ba,sai bada umarni da tayi da yatsun hannunta.
Kaman abin tsafi haka naji ihun muryar Amina da kuma Muhammad..
Zare ido nayi tareda fara jijjiga ƙarfen wajen,wayyo wacece ita mai takeyi musu da
hannunta?.
Maganar data gefenta tayi yafi komai ɗagamin hankali.
"Ranki ya daɗe sun ƙarisa mutuwa a yanzu"
"Ku sakata a wajen ajiyar gawa,shikuma ku kaishi bakin hanya daidai inda za'a
ganshi"
Mutuwa mai take nufi,kashesu tayi kenan meyasa??
Ƙara na sake mai cikeda firgici,wanda sanadiyyar hakan ya haifar min da yankowar
ruwa ta ƙasa na,nishi na fara cikin kukan,wanda bazan iya tsaidashi ba..
Jin kalar nishin danake fitarwa ne yasakata itada matar juyo da hankalin su gareni.
Nan ma kaman abin tsafi ƙofar cell ɗin danake ciki ta buɗe,jan hannuna mataimakiyar
tata tayi zuwa wani ɗakin daban,duk da halin danake ciki amma sai duka nake kaimata
zan ƙwace,shikenan sun kashemin mutane biyu kenan danake rayuwa dasu,shikenan bazan
sake ganinsu ba. Wayyo mijina,zan haihu batareda yana wajen ba,dukkuwa tsananin
muradinsa na son ganin gudan jininsa.
Saboda tashin hankalin danake ciki hankalinnawa ya gushe lokacin da jaririn ya faɗo
daga jikina.
Ihun sane ya dawo dani cikin hayyacina..
Duk halin da nake ciki hannuna na rawa na miƙa hannun zan dauke,amma haka naga wani
hannun dayafi nawa hanzari ya ɗauke.
Binta nayi da ido ganin yanda ta riƙe a jaririn a hannunta tana jijjiga shi da
jininsa da komai.
Hanyar fita daga ɗakin naga ta nufah,da gudu na bita a baya har ina faɗuwa saboda
rashin ƙarfin jiki,domin a zatona kasheshi zatayi kaman yanda ta kashemin mijina.
Inda ta kawoni nagani,babban falone amma ba komai ne a cikinsa ba banda wata
kujera,wazan gani a kai matar nan ce mai hula wacce ta kashemin miji.
Baƙin ciki naji da fargaba lokacin danaga matar tasaka mata yarona akan
hannunta,bai kamata zuwansa duniya kenan ya hau kan hannun waɗannan azzalumanba.
"Maryam"
Naji ta ƙira sunana,muryar tayimin kaman nasan wacece,amma kuma mai zai kawota nan
wajen,mata kamilah mai ɗumbin ilimi.
"Nasan kin gane muryarta,kina shakkane kawai da tunanin nice kokuma ba nice bace,to
niɗin ce dai wacce ƙwaƙwalwarki ta baki"
Saka hannun tayi ta zare hular kanta,"hajiyah Mammah" shine abinda na faɗa cikin
mamaki da ƙarfi.
Dariya ta sheƙe dashi tareda cewa.
"Karkiyi mamakin hakan,komai ya faru ke kika jawo ba kowa ba,san kanki ne dana
mahaifinki ya jawo komai.
Ɗana ya nuna miki so,nima na nuna miki so amma haka kika tsallake kika tafi taki
rayuwar,shi kika barshi a cikin duhu. Duk wanda zan nuna wa kulawa da so ƙarshe
wajen fatima yake komawa,ni a barni dagani sai ƴaƴana,shikansa Hamma ko ƙafarsa zan
tsugunna na lasa haka zai take harshena ya tafi wajenta. Dan haka wannan ya ƙare,
duk sainaga bayan kowa amma bandake ke kaɗai.
Kinsan meyasa? Saboda kece soyayyar Aliyu ta farko,amma akan idonsa yarasata aka
bawa Muhammad saboda son kai,kukayi ta murnar biki da shagali,nikuwa babu wanda ya
kulada ni da ƴaƴana,ina ji ina gani yabar gida amma babu wanda ya tsaida shi bare
yayi masa abinda yake so.
Har lokacin da kikayi aure inada yaƙinin kashe aurenku,ba yanda banyi ba abu yaƙi
yiyuwa,ƙarshe ma wai harda ciki gareki. Hakanne yasa nayi muku gabaɗaya,yanzu
dolene ki auri Aliyu tunda Muhammad ya mutu"
"Bazan aure shi ɗin ba,badai kisane aikinki ba to ki kasheni nima amma bazan aure
shin ba"
Dariya tasake tuntsirewa da itah.
"Mai kike nufi,dama nasan ai zaki ce haka,zan baki zabi guda biyu.
Ko kiƙi amincewa na kasheki,na kuma kashe wanann yaron.
Ko kuma ki amince da ƙudurina,nikuma zan bar ɗanki da rai,amma da sharaɗi duniya
bazata shaidashi a matsayin ɗanki ba,saboda bazai yiwu ki auri ɗana zaki haifamin
jikoki yazamana kuma wanann yana ranki ba.
Dan haka zai shiga alhalin Hamma ne a matsayin amina,dama already na faɗa musu
cewar itace da ciki bake ba"
"Kutt mai kika ce, itace da ciki bani ba?"
"Da mai kike nufi,har abada bazan bada wannan lbarin ba,ke din dan Aliyu aka
halittoki ba Muhammad ba,dan haka bazan taba bada albishir na kinada cikinsa ba
sam.
Yanzu zabi ya rage ga naki. Zan baki wata biyu ki zauna anan ki gama bawa ɗanki
soyayya,daga nan kuma dole tsana zaki dunga nuna masa,ke zaki raineshi amma raino
na azaba,duk ranar da soyayyar sa ta ɗarsu a ranki to sunansa matacce,saiki zaba ko
ceton jinin Muhammad na ƙarshe dayake muradin gani,kokuma mutuwarsa da taki da kuma
ta dukka ƴan uwanki da ubanki?
Wanann shine hukuncinki da butulcin da kikayiwa soyayyar ɗana,kuma haka zaki
girbeta har ƙarshen rayuwarki. Sannan kada ki manta,dukkan ahalin gidan suna
ƙarƙashin ikona ne,kuskure kaɗan zai kaiki ga yin dana sani marar misali"......
SADI-SAKHNA CEH
09035784150
ku tuntubeni domin biyan kuɗinku ko ƙarin bayani.
*SANADIN CACA*
-BOOK 2 (PAID)
Mallakar *SADI-SAKHNA*
09035784150
Bismillahir-rahmanir-raheem
Ki biya kan ki karantamin na biyu dan Allah. ga number ta nan mai son littafi na
ɗaya yayi min magana zan bashi shi kyautane.
*BOOK 2*
...22...
Hajiyah Maryam tana zuwa nan da labarin muryarta da ƙyar take fita saboda kuka.
Yayinda nikuma a nawa bangaren badan kukan da take ba bazan taba yarda hakan ya
faru ba.
Cigaba tayi da maganar wanda zuwa yanzu tana zaune tabas a tsakiyar ɗakin..
"Soyayyar yarona wanda ko zafin haihuwarsa bangama ji ba,ita tasakani amincewa da
kuɗurinta,a tunanina idan yana raye ko bana nuna masa so to ba matsala,ashe vansan
jure ganin ɗanka yana wahala bakada ikon taimaka masa hakan yafima mutuwar
zafi,koba komai Muhammad da Amina su sun huta.
Haka na shafe wata guda ina kulada ɗana wanda nasaka masa suna Ahmad,bayan wata
daya ya ƙare nasake roqarta ta ƙaramin wani watan.
A ƙarshen wata na biyunne na miƙa mata yaron,yayinda wata nurse tayimin allura
yanda alamun haihuwar danayi zasu gushe.
Ina kuka ina komai haka tasaka wani dattijo data cikashi da kuɗi ya kaini gida,akan
wai tsintata yayi a sume a gefen titi inda mukayi accident ,dan cewa tayi wai ƴan
uwan Amina ne suka kashe Muhammad ita kuma suka tafi da itah.
Kowa sai tsinemusu yakeyi,harda marigayiya Amina wacce bataji ba bata gani ba.
Kukan mutuwar Muhammad ne ya dawo sabo saboda bayyanata,kowa na cewa ana ta ƙiran
number Amina amma bata shiga da gangan dama ta gudu.
Bayan sati biyu da faruwar hakan har sannan ko magana banayi,saboda kewar yarona da
kuma mutuwar abokan zamannawa wanda na saba dasu.
A lokacinne kuma wata mata tazo ƙofar gida ta ajiye ahmad ta daddare haɗeda wasiƙa
ta tafi.
Wasiƙar tana ɗauke da cewar wai ɗan Amina ne ta mutu su kuma bazasu riƙe jinin
Muhammad ba,dan haka ga ɗanmu nan,sunansa Ahmad.
Abinnan yayimin ciwo sosai amma ba yanda zanyi,kowa bayyi na'am da Ahmad ba,saboda
baƙin Amina da suke gani,sai hajiyah Mammah wacce ta rungumeshi tamkar
jikanta,hakanne kuma yasa tasake fari a idon mutanen gidan,sai a sannan nagane ashe
abinda take kenan.
Kwanci tashi bayan yaye har hajiyah Mammah ta yaye Ahmad kowa ya manta abinda ya
faru,nikuma saboda bana kula Ahmad yasa aka faramin ganin kaman dan bani na
haifeshi bane,haka na toshe kunnuwana badan komai ba saidan kare lafiyar yarona,duk
da nasan kularda take bashi na munafurcine amma dai yanamin daɗi.
Ana cikin hakanne Aliyu ya dawo,wanda nasan duk matsawar hajiya Mammah ne,lokacin
da aka tada zancen aurenmu kowa ya amince,harshi da dama sona yana zuciyarsa,inaga
kumani da daman munyi yarjejeniyah da itah.
Auren bayyi wani armashi,bansan kosu yayi musu ba,amma nikam jinake kaman an
ɗauramin mutuwa,kulawar dayake banine ma da zuciyarsa ɗaya,tunda nasan shi bashida
laifi shiyasaka ni barin wani abun ya wuce,tunda nasan ƙaddarata ce.
Bayan aurenmu da sati ɗaya zainab tazo gidana ina kuka na faɗamata mai yake
faruwa,shima kuma dan ta faramin faɗane akan kiyayyar danake nunawa Ahmad. Bayan na
faɗamata saida na gargaɗeta tayi shuru amma sai taƙi.
Lokacin tana goyon Neelah, tazo gida wunin arba'in,wannan magana dana faɗamata nayi
dana saninta yafi cikin kwando,domin a daren tana shirin faɗawa hajiya Fatima
bakinta ya manne,tayi tayi tai magana abu ya gagara,haka aka bari akan saida safe
za'a kaita wajen magani.
A daren aka nemeta sama da ƙasa aka rasa,tun masu magani suna cemana tana gari kaza
har muka daina nema muka zubawa sarautar Allah ido.
A sannan ɗin ban daddara ba naso ɗaukar mataki amma banyi nasara ba. Ƙarshe ma wani
abu hajiyah Mammah tasakamin a jikina,duk lokacin danayi yunƙurin bata mata shiri
sai naji kamar yana zuqar jinina ta ciki.
Haka nacigaba da fama da wannan yanayi babu wanda ya sani har na haifi
Maimuna,koshi Aliyu bai san mai yake faruwa.
Tun bana ganin laifin Aliyu da su Aina'u har yazamo ya fara shafarsu,kuma a lokacin
ne na nemi aiki na fara saboda ya ɗaukemin hankali.
Shekarar mu biyu da aure muka tare a sabon gidan Aliyu,wanda shine wannan,a sannan
ne kuma aka bashi muƙamin general.
Naji daɗin dawowar wani gun kuma banji daɗi ba,saboda ninake kulada Neelah,sannan
ina kallon Ahmad duk da bana kulashi,amma kuma koba komai na daina ganin hajiyah
Mammah a kusada ni. Dan babu ɗan adam dana tsana a rayuwata kamarta.
A haka rayuwar tacigaba da tafiyah harna haifi su Saleem inada cikin Fatee.
Lokacin na zama babbar lawyer,shikuma Aliyu yazama air marshall a shekarar,wanda
duk da saka hannun abba nah,saboda rashin Muhammad yasa yake ganinsa tamkar
magajinsa.
Can you imagine wani kisan raini hankali wai su abba Hamma da hajiya Fatima sun
dawowa daga umarah tayar motarsu ta kunce motar ta ƙone. Ko qur'ani aka bani na
danna nasan aikin hajiya Mammah ne,amma ya zanyi toh shikenan suma ta gama dasu.
Lokacin da abban nah yaji wannan labarin shima ciwon zuciyarsa ya tashi,dama ba
lafiyace dashi sosai ba,yamayi retire.
Bayan wani lokaci Aliyu ya damu sai ya dawo da hajiyah Mammah gabansa,saboda ita
kaɗaice dukka yaran gidan sunyi aure. Mariya kamma watan haihuwarmu kusan ɗaya,ta
haifi Mulaifah tanada cikin na biyu.
Ita a haihuwa ta rasu ɗan shima ya koma,nikuma na haifi Fatee aka sakamata sunan
hajiyah Fatima.
Neelah kuma saboda babu hajiyah Fatima saina kaita gidan marayun dana ke
kuladashi,lokacim ma ba babba bane,amma tunda bazan iya riƙeta kusada ni ba gudun
cutarwar hajiyah Mammah gwanda na kaita inda zata dunga ganin yara sa'anninta,kuma
atleast zan dunga ganinta kullum.
Batayi ko wata ɗaya bama Aliyu ya kaisu india itada Ahmad wajen amininsa zasuyi
karatu a can.
Kasancewar lafiya suke yasa na kwantar da hankalina na cigaba da kulada wanda suke
gabana.
Ana nan har akayi auren Maimuna,itakuma Neelah bayan sun gama makaranta ta dawo
gida tana training ɗinta a nan abuja,amma bata zauna a gidan ba saita zauna a
barrack,shikuma Ahmad bai dawo ba sai daya gama komai.
A tunanin sa kokuma nace tunanin da aka saka masa kuma yake gani,nafi kowa tsanarsa
a duniya,nan kuwa a kaff rayuwata dana tashi na tsinci kai na a uwa,kullum banda
lissafi saina suwa yake tareda su,cutar dashi suke kokuma ahah"
Kukane ya kubce mata wanda nima yasakani kukan,dama abinda yake faruwa kenan, tabbb
lallai idan kaga mutum ya kabarshi,wato kenan ita kura ce da fatar akuya tazo ta
labe anan wajen.
"Kenan matar dana gani da wata ta shige jikin bango ranar danaxo gidannan......."
Ɗago ido hajiyah Maryam tayi tareda ɗaga min kai.
"Ita kika gani ba kowa ba,itada wanann shegiyar Raheenan,wacce ta ɗaukemin yaro
lokacin dana haifeshi,su ne kika gani inda sun san kin gansu da tuni bakya
numfashi,shiyasa nake cemiki kiyi taka tsantsan kada ki maimaita kuskurena."
"Wannan hoton dana gani shine baban Ahmad,amma kince bai san Ahmad ba,ya na ganshi
kuma a hoton?"
"Bada shi akayi hoton,ni kaɗai nayi hoton ranar sunansa,wanda na roqi hajiya Mammah
ta barni nayi,shidin bayarwa nayi aka hadamin kamar yana cikin hoton"
Uhm jijjiga kai nayi tareda jajanta lamarin,shin waye zayyi tunanin abinda yake
faruwa kenan idan ba gani yayi ba,lallai in kuwa hakane akwai aiki a gaba.
"Akwai wani aikin da zakiyimin Sumaimah"
Hajiyah Maryam ta faɗa tana tafa ƙafaɗa tareda jan majina,wanda tafito saboda yawan
kukan data sha.
"Please ki zauna dashi a wannan kwanakin,na ɗago cewar shiba ɗan Aliyu bane,dole
za'a faɗamasa waye ubansa,kuma ace shi ɗan tubabbiyane wacce ƴan uwanta suka kashe
ubansa,daganan wanda bai sani bama zai sani,dan haka be with him"
"Ammm........amma taya zan zauna dashi bayan baisan ni wacece ba, bayason ina yin
kusada shi alhalin yana ganina a matsayin wacce ba muharramarsa,saida nayi miki
alƙawarin zan taimaka miki wajen ganin mai yake faruwa,sannan daga gobe zan fara
aiki a sashen hajiyah Mammah,saboda gano wani abun"
"Ahah bazan sakaki wannan aikin mai hatsari ba idan tagano wacece ke bazatayi
tunani na biyu ba zata kasheki,ta kashe ɗanki. Kinsan ke wacece yanzu haka a
wajenta kuwa......?
Matsafanta sun nuna mata wacce zata kawo ƙarshenta matar ɗan data raba da iyayensa
ne wato Ahmad. Sannan matar dazatayi sanadiyyarta itace uwar ƴaƴan sa. Abinda bata
sani ba ya riga yayi auren,da ta sani bazata hana Mulaifah aurensa ba,hasalima ita
zata ƙarfafa hakan. Shiyasa kada ta gano matsayinki ba yanzu ba tukunna"
"Nasan da hakan kuma zan kiyaye,amma ki sani nima rayuwar ɗana data mijina nake
dubawa"
"Shikenan kije ki kwanta dare yayi zanyi tunani akai zuwa safiya."
Da haka na bar sashen hajiyah maryam ɗin zuwa namu sashen,duk da banida waya a
hannuna amma nasan dare yayi sosai,dan tsitt kakeji babu motsin komai a gidan.
Daidai nazo farfajiyar gidan zan wuce sashenmu naga mata guda da alkyabba,wadanda
dai nagani farkon zuwana gidan.
Yanzu kaman wancan lokacin ta jikin katanga suka wuce,daidai inda naga wannan
zanen.
Jijjiga kai na nayi tareda cize baki,wannan karon ko ɗar na tsoro banji ba na wuce.
"Aradu kaman yanda kika gama taggunki to sai ya karye,kodan saboda rayuwar mijina
dana ɗana bazan saurara miki ba sai asirinki ya tonu,wanda kike tsoron karsu gane
kuma kike komai dominsu wato ƴaƴan ki,saisun gane wacece ke"
SADI-SAKHNA CEH
09035784150
ku tuntubeni domin biyan kuɗinku ko ƙarin bayani.
*SANADIN CACA*
-BOOK 2 (PAID)
Mallakar *SADI-SAKHNA*
09035784150
Bismillahir-rahmanir-raheem
Ki biya kan ki karantamin na biyu dan Allah. ga number ta nan mai son littafi na
ɗaya yayi min magana zan bashi shi kyautane.
*BOOK 2*
...23...
Gudu gudu sauri sauri tayi parcking motar a ƙofar wani gida,kaman an turata ko gama
saita ta batayi ba ta buɗe ƙofar ta faɗa gidan fa gudu.
Hannunta na kan bakinta,kana ganinta kasan kuka take tarewa da hannun.
Kai tsaye wani sashe ta nufah a gidan ba cikin gidan ta shiga ba.
Domin gidan kana kallonsa da alama na haya ne amma na masu aji.
Banke ƙofar tayi ta shiga farlon,ba kowa a ciki dan haka ɗaki ta shige.
Wata matashiya ce mai matsaikacin a jiki a kwance akan gado fanka na seseta tata
tana bacci.
Gadon ta hau tareda ɗaga mata duka a hips ɗinta.
Wata zabura mai baccin tayi tareda kallon Mulaifah cikeda mamakin ganinta da tsakar
rana a gidanta.
"Ke lafiya na ganki kaman an jefoki iyanzu,daga ina haka?"
Maimakon ta bata amsar maganar ta saima kuka data kece dashi da danasani da kuma
takaici.
'Magana nake miki Mulaifah amma kinyi shuru vakicemin komai ba"
"Padush na shiga uku shikenan rayuwata ta ƙare nikam wayyo Allah nah"
"Wai maiya farune?"
Wata takarda da take hannunta ta jefawa padush ɗin,wacce take ɗauke da sunan
asibiti.
Da sauri hannunta har yana rawa ta buɗe takardar,zaro ido tayi da alama ta karanta
abinda ya saka Mulaifah kuka.
"Ciki..... Omg how,garin ya hakan ta faru mai kike tunani?"
"Nima bansani ba besty,kuma fah ina amfani da magani yanda ya kamata"
"Uhm na waye to a samarinki,nasan bazai wuce useey ba koh"
Ɗaga kai tayi kawai ba tareda ta bata amsa ba.
"Ya sani amma?"
"Yasani dashi ma mukaje asibitin"
"To kuma miyasa kuka dawo ba'a zubarba?"
"Hmmm sunce wai zan iya rasa raina idan natakura saina zubar,saboda mahaifata
batada ƙarfi,nayi amfani da magani sosai,ga kuma abortion danayi sau biyu,idan
nasake wai zan iya samun bleeding mai tsanani.
Duk da hakan ya takura akan sai an zubarmin shi bai shirya karbar dan shege ba
yanzu,wai sunan iyayensa zai baci,musamman da yana neman minister.
Nikuma sai naƙi a zubar ɗin,dan gaskiya ban shirya mutuwa yanzu ba.
To akan hakane mukayi fada dashi ya tafi,yace kuma idan nasake nemansa sai ya batar
da rayuwata.
Padush ina cikin tsaka mai wuya,dan Allah ya kikega zanyi yanzu?"
"Uhmm badan badan ba akwai wata shawara,cikin wata nawane"
"Two month ne fah,munje yin gwaji ne na kowanne wata aka ganshi"
Wani juya ido padush tayi tareda gyara zama,
"Badama kince har yanzu baki haƙura da auren Ahmad ba?"
"Eh ban haƙura ba amma yanzu kam kinsan bazai yiyu ba ai,tun bayan da aka ce shiba
ɗan abba bane zance ya watse,bama ko magana dashi ma fah yanzu wata biyu
kenan,shine ai na koma wajen usseey rage zafi,kinga abinda na jawowa kaina nan"
"To mai zai hana ki maida cikin na Ahmad inyaso,i think kaman zayyi,kinga idan ya
san cewa nasane to a gidan za'a saka dole sai ya aureki,shima kuma zai dunga kulawa
dake tunda yana tunanin abinda ya aikata miki. Tunda kince cikin two month ne to
definatly a wata bakwai nan gaba zaki haihu kenan... Sai mu kasheshi muce ɗan
bakwaine batareda kowa ya ganshi ba,kinga ke kuma daga kin warware sai ayi muku
aure"
"Wow wannan labarin yayi daɗi,amma taya zai kasance,sanin kanki ne ko karen haukane
ya ciji Ahmad to bazai nemi mace ta wannan hanyar ba"
"Tsiyata dake gidadanci,to dama haka kawai zamu je masa,maganin tada ƙarfaffa
sha'awa zamu saka masa,wanda ko shi robot ne to bazai iya riƙe kansa ba,saikin
tabbatar yasha yafara aiki tukunna saiki je sashennnasa,daga nan ki ɗau wayarsa ki
ƙira numberki.
Idan komai ya wakana da safe saikiyi kukan ƙarya,kice masa ƙiranki yayi,to da kika
zo bakisan mai yake faruwa ba kawai ya afka miki,gashi da ƙarfi ya farmakeki har
kika kasa ƙwatar kanki......haka haka dai nasan dole zaice ki boye abin yazama
sirri,daga nan sai ki nuna masa alamar kinada ciki,saiki kai maganar wajen su
Abbah.
A lokacin vashida zabi daya wuce ya aureki'"
Tun kafin padush tagama bayanin Mulaifah ta rungumeta saboda tsananin murna,ganin
lokaci guda tasamu mafita akan matsalarta.
Daga haka suka cigaba da tsara yanda plan ɗin zai tafi musu a cikin nasara.
Basu tashi ba saida suka ƙira wani doctor saurayin padush ɗin akan a ina zasu samu
maganin amma mai ƙarfi sosai.
Sumaimah (POV)
A tsawon wannan watanni biyu da faruwar zancen auren Ahmad da Mulaifah mun samu ɗan
kusanci kaɗan fiyeda na da nida Ahmad. Wanda kowa idan ya kalla yasan soyayyata ce
tashiga zuciyarsa,kokuma nace zuciyarsa ta ganeni,ƙwaƙwalwarsace dai har yanzu bata
ganeni ba.
Ni abinma wani lokacin har dariya yake bani,idanna ga yana hade rai idan ya ganni
da Saleem ,bama ya Sameer wanda shima ya dawo daga aikin daya rafi yi,shikamma har
kalmar so ya furtamin, a amma lokacin nace masa yayi haƙuri ni matar auece,lokacin
dana faɗamsa bai yarda ba saida na rantse masa tukunna.Tundaga lokacin muke mutunci
dashi,amma shi Ahmad bai sani ba,gani yake kaman soyayya mukeyi,nikuwa ban taba
faɗamasa gaskiya ba,shima ya ɗanɗana yaji yanda naji kokuma nace nake ji. Shima
Sameer yanzu nice nake yimasa abinci a gidan, shikuma Saleem in yana nan a sashen
Ahmad yake ci. Sameer ma abinda yasa baya zuwa don basa shiri da Ahmad ɗinne,har
yanzu yana zarginsa a cewar shiya gani a wajen satar da akayi shekara biyu baya.
A bangaren hajiyah maryam kuwa yanzu har raina nake ɗaukarta tamkar mahaifiya
ta,yayinda itama take ji dani tamkar ƴar ta,amma yawanci mukanyi zancene a sashenta
inna je yimata aiki,duk da ta hanani ma amma nice na nace akan zan dunga yimata.
Yanxu ma a kitchen nake na dukka gidan ina yin abincin karyawa,Ahmad bayanan yaje
Kaduna jiya,da yamma zai dawo.
Dan haka shi yau bashi a abincin safen,iyah Sameer ne kawai da hajiyah maryam,wanda
don ita ma na tashi dawurin saboda zata sha magani,jiya a gidan marayunta muka wuni
an ƙara mata jini. Duk lokacin danaga tana wahala yanxu haushin hajiyah Mammah
nakeji,don nasan itace ummul aba'isin na duk abinda yake faruwa a gidan.
Jallof ɗin taliya nayi mai ruwa ruwa tasha sardine,a warmer na sakawa Sameer
nasa,ita kuma a plate na zuba saina kife da wani.
Saida na kai masa nasa kan dining table kafin na wuce sashen hajiyah maryam.
Neelah bata nan tare suka tafi da Ahmad dan haka nice kaɗai mai kulada itah,tunda
ni kaɗaice nasan abin dayake faruwa.
Bata ɗakin,amma akan gadon akwai alamun bata daɗe da tashi ba,kenan tana banɗaki.
Ajiye abincin nayi na yaye zanin gadon,ganin alamar jini jini daya bata gadon,wanda
nake tunanin inaga daga jikin carnular ta yafito.
Bayan na cire ina shimfiɗa wani tashigo ɗakin jikinta da ruwa,wanka kenan tayi.
Gaisheta nayi tareda yimata ya jiki,ta amsa cikeda fara'ah,ta samu ƙarfin jikinta
ba kaman jiya ba.
A bakin gadon ta zauna na miƙo mata abincin,kana na buɗe drawerta na miƙomata
magani.
Bayan ta gama ɗan zance mukeyi wayar ta tayi ringing,Neelah ce taƙira taji ya
jikinta. Sun fara magana kenan na dauke kwanon na basu waje. Dan yanzu babu wani
zance labe na rigada nasan bazata taba cutar da Ahmad ba,kuma bugu da ƙari nariga
da nasan wacce take aikata komaiɗin.
Lokacin dana maida plate ɗin ummi harta fara wanke wanke,banyi koƙarin tayata ba
dannasan batason hakan.
Ina ajiyewa ma naga wayata tana ƙara.
Yau wace rana nace a raina,yah Musbahu ne yake ƙirana.
Sun fito daga wajen aikin kenan,kai mashaallah dan dama ƙiranmu na ƙarshe dashi tun
kafin nazo gidanann,wai an turasu wani waje aikinsu na farko,kuma wajen ba
service,harsu gama ba waya.
"Yah Musbahu kaine dagske?"
Dariya yayi kafin yace .
"Nine mana mai kika gani?"
"Wata huɗu fah kenan kona ce biyar"
"Uhm Alhamdulillah mungama ai,jiya na dawo gida da daddare,naje gidanki akace wai
bakyanan kin tafi aiki abuja.....Sumaimah meyasa,aikatau fah akace kinayi?"
Shuru nayi na kasa bashi amsa,nasan dama dole sai yaji babu daɗi. Hawayene naji
yana shirin zubomin nayi saurin maidashi. Inata garauniya na manta ashe inada wanda
suka damu dani.
"Lahh yah Musbahu karka damu ba wani aiki bane fa sosai,bawata matsala. Ina su
ammi,kaje gidana kace yasu deeja da Sayyid da inna".
"Duk suna nan ƙalau,banida lokaci gobe zan koma kaduna da nazo na ganki,amma karki
damu bayan mungama da kaduna abuja za'a turamu headquarter indai an tabbatar da
ƙwazonka,Inshaallah idan na dawo abuja zaki bar wani aikin aikatau"
"Tom Sheeshah Allah ya kaimu yah Musbahu nagode"
"Ameen ya Allah"
Cikin sanyin jiki na sauƙe wayar,zai dawo abuja? Kuma zai hanani aiki,idan bangama
abinda zanyi a gidan kafin sannan fah,hajiyah maryam bazata iyah cigaba da yi ita
kaɗai ba,don wannan jinyar da take ma ƙoƙarin taimakon Ahmad tayi ta hanyar bashi
wasu bayanai akan mahaifinsa. Saboda har yafara zargin kansa a matsayin ɗan wacce
ta kashe masa mahaifi. Wannan abin na kana ganin gaskiya kayi shuru yafi komai
sosawa hajiyah Maryam zuciya. Dan a ranar da hajiyah Mammah ta zauna tamkar matar
arziƙi tana zayyano masa labarin ƙaryar hajiyah Maryam kuka tayi ta rabza a
ɗaki,musamman da taga halin da Ahmad ɗin ya shiga,da saida yayi yunƙurin nemo
dangin Amina,injishi dangin mahaifiyarsa. Da ƙyara aka shawo kansa ya haƙura,shiMa
bawai dukka ba,yabarine saboda case ɗin dayake handling.
"Ohh ya zanyi idan yah Musbahu yazo gidannan,komai fah zai iya wargajewa kenan."
Sashenmu na nufah domin na kwanta,dan yau bazanje sashen Ahmad ɗin bama sai yamma
idan yakusa dawowa.
SADI-SAKHNA CEH
09035784150
ku tuntubeni domin biyan kuɗinku ko ƙarin bayani.
*SANADIN CACA*
-BOOK 2 (PAID)
Mallakar *SADI-SAKHNA*
09035784150
Bismillahir-rahmanir-raheem
Ki biya kan ki karantamin na biyu dan Allah. ga number ta nan mai son littafi na
ɗaya yayi min magana zan bashi shi kyautane.
*BOOK 2*
...24...
Hankalinta kwance ta haɗa komai a hankali,don tasan tunda yace bada wuri
ba,wataƙila ma sai wajen magriba su ganshi.
Bayan ta gama komai jawowa sashen tayi amma bata kulle ba,tunda tasan babu mai
shiga idan ba itaba kokuma wani inya gayyaceshi.
Tafiya take tana ƴar waƙa,tamkar babu abinda ya dameta,tana shiga sashensu banɗaki
ta faɗa domin ta ɗauraye jikinta,don tun ranar farkon da Ahmad ya kamata tayi wanka
a banɗakinsa bata sakeyi ba,tanaso ya yarda da itah,idan zatayi nasara to sai ta
haɗa da kiyaye irin waɗannan abubuwan.
∆∆∆∆
A bangaren Mulaifah kuwa tun safe aka kawomata maganin da zatayi aikin dashi,
(sildenafil viagra).
Tana tsugunne a garden taga shigewar Sumaimah ta dawo daga sashennasa,
Hakanne yabata damar itama shigewa sashen.
Bayan ta shiga kunkumi takama tareda yamutsa fuska jin yanda ƙamshin turare yakama
falon sosai.
Takawa tayi zuwa kan dining inda Sumaimah ta jera kayan abinci,saida ta buɗe tagani
kafin ta fito da maganin. Gorar ruwa ta buɗe ta zuba overdose,yanda zayyi aiki
yanda yakamata,kuma ta sanshi sarai idan bai gusar masa da hankali ba to zai iya
riƙe kansa..
Murmushin mugunta tayi tareda rufe komai kaman bata tababa ta juya ta tafi.
Tana fitowa daga falon ta ƙira padush tareda labarta mata.
Lokacin har an fito daga sallahr magriba.
∆∆∆
Bayan Sumaimah tayi sallahr magriba bata tashiba saita fara karatun ƙur'ani har
akayi sallahr isha ta tashi tayi,tana nan zaune akan daddumar taji wayarta tayi
ƙara,sunan Ahmad tagani,ya dawo kenan ta faɗa a ranta.
Ɗagawa tayi tareda yin sallama.
"Ka dawone ya hanya?"
"Lafiya ƙalau,shin kin rufe min drawer ne?"
"Ehh na rufe"
"Ina kika saka key ɗin,zan ɗauki wani document ne akwai abinda zan duba da darennan
a ciki"
"Waii ai na taho da key ɗin a jikin wanda ka vani na sashenka,amma ina wanda yake
wajenka"
"To na wajennawa ne yafaɗi ai banganshi ba,kuma ma yanzu zaki bani ki tafi,nasan
daren yayi ai"
Daga haka ya kashe wayar tasa,kallo Sumaimah tabi da wayar tareda tashi daga kan
sallayar,wato ya ɗebo gajiyarsa yanason hucewa akan ta.
Da hijabinta na sallah a jikinta ta ɗauki key ɗin ta nufi sashennasa.
Ta baya tabi bata shiga ta cikin gidanba,duk da ba komai zatayi ba amma kada su
zargi wani abun.
Ƙwanƙwasa ƙofar tayi shuru,har tagaji ta buɗe ta shiga,a wajen dining ta ganshi,a
gorar ruwa a hannunsa,a ƙasa kuma ya zubarda juice ɗin da ya haɗa.
Juyar da ido tayi tareda miƙa masa key ɗin,wani lokacin mamaki yake bata idan yana
abu kamar yaro.
Ɗauke jug ɗin tayi a ƙasan ta rufeshi,hanyar kitchen ta nufah zata ɗauko
mopa,maganar sa ce ta tsayar da itah.
"Mai zakiyi a kitchen yanxu?"
"Wannan wajen zan gyara mana kafin gobe ya bushe,kuma da alama sai iya shiga ƙasan
kujera"
"Amma dare yayi ki gyara nan wajen kuma......"
"Karka damu yanzu zan gama na tafi"
Ɗaga mata kai yayi tareda shigewa ɗakinsa.
Bayan ta ɗauko mopar hijabinta ta cire ta ajiye akan kujera.
Tazo matsar da gorar ruwan dayasha sai taga abu ya taru a ƙasan robar,abinne ya
bata Mamaki,mai ya kawo wani abu cikin gorar ruwa kuma.
Ɗagawa tayi tana jujjuyawa,kaman an ce takai idonta ƙasa saita hango ƙwayar magani
a ƙasan table ɗin,tsugunnawa tayi da sauri ta ɗauka tana jujjuyata,tabbas ɗazu ta
gyara wajennan bataga komai ba.
To kennan waye yashigo ya ajiyeta a wajen,da alama kuma irinta aka saka a cikin
gorar ruwan,wani abin tashin hankalin wanda aka hara da koma mai nene yariga da
yasha.
Hannayenta ne suka fara rawa kana da dukka ilahirin jikinta.
Saurin tashi tayi kaman an tsikareta tayi ɗakin Ahmad ɗin da gudu.
A bakin gado ta ganshi ya kifah kai,hannunsa kuma yana kan cikinsa ta ƙasa,babu
riga a jikinsa daga shi sai gajeren wando.
Ga drawer ya buɗeta ga kuma kayansa a gefe..
Da gudu ta nufeshi tareda zama a gefensa.
"Wayyo dan Allah kada ka mutu ka tashi muje asibiti,wayyo Allah mai kayi musu zasu
kasheka"
Riƙo hannunta yayi gam,hakan yasakata tsayawa da yin kukan ta kalleshi.
Shima itan yake kallo,idanunsa sunyi jawur tamkar garwashin wuta. Magana yakeson
yi,amma fatar bakinsa rawa takeyi,kana gani kasan yaƙi yakeyi da wani abu dayake
son tasowa a cikin jikinsa.
"Ki......kitafi.....ki rufe ƙofar kada ki kuskura ki dawo..."
"Meyasa mai kake nufi,wanine yasaka maka abu a cikin ruwa Kasha,kuma da alama mai
illah ne,inaga ma guba ce tunda tasaka maka ciwon ciki,dan Allah ka tashi muje
asibiti"
"Nace. ....kkkkitafii Sumaimah,meyasa bakyajin magana,Ko so kike na rasa tunanina
na aikata miki abinda dukkanmu zamuyi danasani....."
Shuru tatsaya tana kallonsa,dan har yanzu bata gano mai yake faruwa ba,saida ya
daka mata tsawa kafin ta tashi ta fita tana share hawaye.
Harta fita daga sashennasa sai kuma tagano alamar motsin mutum yana tahowa zuwa
inda take.
Gabanta ne yafara bugawa,don a zatonta ko hajiyah Mammah ce zatayi siddabarunta.
Komawa tayi a hankali zuwa falon ta rufo ƙofah tana leƙowa ta glass ɗin ƙofar.
Saida ta matso kusa kafin taga Mulaifah ce,tana tafiya tana waiwayawa tamkar
munafuka.
'To ita kuma mai haɗinta danan wajen zatazo goman dare.'
Shine tunanin da Sumaimah tayi wacce take kallonta ta glass ɗin ƙofah.
Ganin sashen Ahmad ta nufo zata shiga,hakan yasa Sumaimah tayi saurin saka key
wanda yake hannunta,saboda kada ta shigo ta ganta a ciki itama da daddaren,amma
kuma Ahmad yana buƙatar taimako. Kai amma ba a wajen wannan ba.
Murɗa ƙofar tayi ta jijjiga amma shuru,kaman zatayi kuka tayi,duk Sumaimah tana
kallonta.
Wayarta ta ɗauko ta danna ƙira,can bayan an ɗauka tace.
"Padush ya rufe ƙofar bayan ma,tayi ta bugawa har mai gadi na yaci yaji,amma shi
bai buɗe ba,kumafah bai daɗe da shiga ba,baici maganin ya fitar masa da hankalin sa
ba zuwa yanzu,kuma hakanne ma zaisa ya buɗe da wuri ai.........ohh padush yazanyi
ne,idan bai buɗe ba asirina zai tonu in aka gane inada ciki a
gidannan..........najira menene,ni haƙurina ya ƙare,idan bai buɗe ba yakwana bayyi
releasing ba maganinnnan zayyi masa illah,karnaje nayi silar hakan,kinsan ina
sonsa..........wayyo nashiga uku,yanzu duk plan ɗin dana wuni ina haɗawa ya
vaci,shiya sani yasan yadda zayyi,in wani abuma ya sameshi babu wanda zaisan nice"
Bayan ta kashe wayar juyawa tayi kaman zatayi kuka,duk abinda take kuma take cewa
Sumaimah tana kallonta. Wani ƙululun baƙin cikine da kuma na tashin hankali suka
haɗu mata a cikin ƙirjinta.
"Oh dama kece,kuma abinda kika saka masa kenan a cikin ruwansa,sai yanzu na kamo
bakin zaren,wato so kike ya kwanta dake ba'a cikin hankalin sa ba,saboda ki laƙaba
masa cikin da kika iyooo"
Hannu Sumaimah tasaka a ha'barta tana jinjina lamarin..
Ta ɗan daɗe a wajen,saida ta tabbatar Mulaifah ta tafi tukunna kafin itama ta murɗa
zata fita.
Har ta saka ƙafarta a waje saikuma maganar Mulaifah ta dawo cikin kunnenta.
Cewar in ya kwana batareda mace ba ya samu matsala shiya sani.
Maida ƙofar tayi ta rufe bayan ta dawo cikin falon.
Safah da marwa tafara tana tunanin abinyi,itadai in tace zata samo makarin maganin
dayasha a daren to tayi ƙarya,sannan shin wa zata nema yabata shawara akan ya
zatayi.
Wayarta ta ɗata ta danna ƙorna Neelah.
Can kaman ringing biyu ta ɗaga,muryar tarau take da alama batayi bacci ba.
"Hello anty Neelah kina jina?"
"Ehh ina jinki,yadai jikin mommy ne ya tashi?"
"Ahah daman............"
Kaff ta zayyane mata abinda yake faruwa,ajiyar zuciya tasake bayan ta gama jin
abinda yake faruwa.
"Kai amma wannan yarinya akwai shegiya,wai su bazasu barshi ya huta bane? Kinsan
miye,yanda ta faɗa gaskiya ne zai iya yimasa illah,tunda tace overdose
tabashi,sannan ni bana nan ina kaduna bare na samo masa maganin dazai karya wanda
ya sha. Abinda za'ayi tunda ke matarsa ce dole kene zakiyi masa magani,kuma dama
hakan haƙƙinki ne......saidai kiyi haƙuri zakiji jiki sosai tunda baya
hayyacinsa....."
"Bakomai dama nayi tunanin hakan,na tambayi shawararki ne kar hakan yazama
kuskure,musamman da rayuwarsa ke cikin hatsari"
"Shikenan kiyi haƙuri kikuma jure,komai zaizo da sauƙi Inshaallah"
Kashe wayar Sumaimah tayi tareda kasheta,hanyar ɗakinnasa ta nufah cikin sanyin
jiki.
A hankali ta murɗa ƙofar ɗakin,yana nan a inda ta barshi,saidai yanzu daga inda
take tana hango yanda jikinsa yake rawa.
Ƙarar maida ƙofar da tayine yasakashi ɗagowa ya kalleta,zuwa yanxu kam ya sanja
kamanni.
Takawa take a hankali tana nufar inda yake,yayinda shikuma yake binta da wani mayen
kallo mai cikeda fassara,gabanta dukan tara tara yake har ta zauna a bakin gadon.
Hannunta ta ɗaga zuwa kannasa hannun,wanda jijiyarsa suka fito raɗa raɗa,tausayinsa
ne ya tsirga mata har cikin ranta,wanda hakan yasakata fashewa da kuka.
"Kayi haƙuri ka yafemin,nasan hukuncina bazayyi maka daɗi a gobe ba,amma kayi
haƙuri dan Allah"
Tana gama faɗin hakan takai bakinta saitin nasa,kaman dama riƙewa yake,amma yanzun
ƙarfinsa ya gaza control ɗin ƙishirwar da take cikin ransa,hakan yasaka mai makon
yaji haƙurin da take bashi,saima sumbatarta daya farayi a zafafe.
Kuka take tana cize baki jin yanda yake yamutsata,tun tana jin da ɗan ƙarfi a cikin
jikinta harta daina ji.
Ta daɗe tana ɗanɗanar azabar,har saida maganin yasakeshi jikinsa ya sake laraff
baccci ya ɗaukeshi,kafin itama tasamu damar runtsawa.
SADI-SAKHNA CEH
09035784150
ku tuntubeni domin biyan kuɗinku ko ƙarin bayani.
*SANADIN CACA*
-BOOK 2 (PAID)
Mallakar *SADI-SAKHNA*
09035784150
Bismillahir-rahmanir-raheem
Ki biya kan ki karantamin na biyu dan Allah. ga number ta nan mai son littafi na
ɗaya yayi min magana zan bashi shi kyautane.
*BOOK 2*
...25...
Yaji dai kaman ya tasa kai da wani abu mai tudu,amma bayyi masa kamada pillow
ba,buɗe idonsa yake a hankali saboda nauyin da yayi masa kafin ya sauƙe akan cikin
Sumaimah.
Ɗaga kansa yayi sai a sannan yaga ashe kan ƙirjinta yasaka kansa,mai ya kawota
ɗakinsa kuma kan gadonsa,sannan ba sutura a jikinsu.
Abinda yafaru jiyane Yafara kwaranyowa cikin ƙwaƙwalwarsa.
Saurin zabura yayi ya tashi zaune tareda ƙarewa yanayinnasu kallo,jini ya gani a
bargon da wajen ƙasanta,wanda yasan ba shakka daga cikinta yake fitowa,saboda
tsabar ƙarfin dayayi mata a jiyan..
Hannunsa dukka biyun wanda suke rawa yasaka a kansa ya dafe,domin ji yake kaman zai
cire saboda tension ɗin dayake ciki,wani ihu ya fashe dashi na dana sani da kuma
nadama.
Hakanne ya farkar da Sumaimah daga baccin da tayi a jiyan,wanda za'a iya ƙiranshi
da ƙanin suma.
Iduwanta fulu fulu sukayi,badan fatar bakinta ta ƙasa inda ta cijeta tayi jawur.
Yunƙurawa tayi a hankali ta tashi zaune tana cicccize baki saboda tsamin da jikinta
yake yimata.
Kallo tabi Ahmad dashi,wanda shiɗinma ita yake kallo tamkar gunki.
Zanin dayake gefenta ta jawo ta saka akan ƙirjinta,kana ta kama gashinta daya bake
akan fuskarta ta ɗaure.
"Meyasa......meyasa......meyasa kika aikata haka,kinsan kuwa girma da kuma munin
abinda kika sanya na........."
"Kana lafiyah,maganin yabar jikinka bazai cutar dakai ba?"
Shine abinda Sumaimah ta faɗa cikin dashashiyar murya.
"Naji Mulaifah tana cewa zai jawo maka babbar matsala idan ta zauna dashi a haka"
"Shine dalilin daya saka kika bada kanki,abinda yafi komai muhimmanci a
wajenki,sannan kika saka na aikata abinda harna mutu bazan manta ba? Meyasa
zakiyimin haka,bayan nace miki ki tafi mai ya dawo dake toh? Akan matsalata ki
kalli abinda na aikata miki,yanzu ya zanyi kenan"
Maganar cikin nadama yake ambatarta kamar zayyi kuka.
Ɗan murmushin ƙarfin hali Sumaimah tayi kafin tace.
"Karka damu nidama ba budurwa bace bare kace na rasa budurcina,Sannan nayi niyyar
tafiya kaman yanda kace,......."
"Wannan shine abinda yakamata muyi magana akai a yanzu?"
Daga haka ya tashi ya shiga banɗaki.
Binsa Sumaimah tabi da kallo tareda runtse ido. Shin wai yaushe zatayi tarayya da
mijinta cikin salama ne,dan wannan ko kusa bazata ƙirata da kwanciya ba sam.
Ƙoƙarin tashi take amma abu ya gagara,ko ranar farkonta bataji wannan azabar
ba,gaskiya bazata taba yafewa Mulaifah ba.
Jingina tayi da kunnen gadon,ganin duk yanda tayi bazata iya tashi daga kan gadon
ba.
Jin motsin takunsa ne yasakata buɗe idanuwanta,jallabiya ce a jikinsa ruwan
toka,sai ruwa daya ke fitowa daga sumar kansa,alamar ya tsabtace jikinsa. Daren
farkonsu ne ya faɗo mata a ranta,yanda tayi fama dashi kafin ya tashi yayi wanka.
Duk da halin datake ciki hakan bai hanata yin murmushi ba,idan tace batayi kewar
goje bama tayi ƙarya.
Ciɗak taji ya cirata sama tareda yin hanyar banɗaki,da kallon mamaki tabishi kana
dabi jikinta ma da kallon,zanin ya cire cinyoyinta duk bushashshen jini. Runtse
idonta tayi wannan kunya har ina.
Da sauri ta buɗesu jinta a cikin ruwan zafi,saida tasaki ƙara jin yanda ya shigeta.
"Ki zauna a ciki zafinsa inya ratsaki zakiji ƙarfin jikinki ki iya gyara kanki. "
Daga haka yabar banɗakin,ajiyar zuciya ta saki tareda sake jikinta a cikin bahon
wankan,tasan yanzu yafijin haushinta ma fiyeda wacce tayi silar shigarsa cikin
wannan yanayin.
Ta daɗe a ruwan,bayan yayi sanyi ma tasake saka wani ruwan zafin.
Saida taji jikinta ya ɗan dawo daidai kafin tayi wankan tsarki ta fito.
Towel ɗinsa ta ɗauka tayi amfani dashi,lokacin data fito baby duvet ɗin ya
cireshi,ko ina ya kaishi oho.
Hijabinta ta ɗauka tayi sallahr asuba,dan rana harta fara fitowa a lokacin.
Addu'o'i ta dungayi daga zaunen,ta daɗe kafin ta tashi ta naɗe sallayar.
Falon ta fito domin hada abinda zataci.
Idonta ne yakai kan dinning inada aka ajiye leda,tasan Ahmad ne ya ajiye,tunda jiya
babu ita a wajen.
Sannan abincin datayi masa jiyan shima yana wajen.
Ƙarisawa tayi wajen ta buɗe ledar,magani ne na relief pain a ciki.
Tea ta haɗa tasha kana ta sha maganin. Daga nan ta tafi sashensu,dan ma Allah ya
taimaketa safiya ce ba mutane sosai,su inna ladiyo kuwa batada matsala dasu ,dan yi
zatayi kaman ta dawo daga sashen hajiya maryam,tunda ko badan haka ba wani lokacin
takan kwana a wajenta.
Bayan ta kwanta akan katifar tata abubuwa ne da dama suka fara yawo a cikin
kanta,shin da wannne ido kenan yanzu Ahmad zai dunga kallonta.....runtse ido tayi
ko bacci zai ɗauketa.
A bangaren hajiyah maryam da taga rana tayi sosai Sumaimah bata zo ba sai hakan ya
tabbatar mata da zancen da Neelah ta ƙira ta faɗamata.
Safa da marwa take a ɗakinnata tarasa abinyi,so take taje taga mai yake faruwa,dan
indai yana cikin magani zai iya yi mata illah sosai.
"Kai wannan mutane wannan mutane,wato so take ta laƙaba masa cikin shegen da tayi?.
Allah sarki koyah Sumaimah take,nasan tunda banganta ba yanzu to tasha wahala a
wajensa"
Waya ta ɗauka taƙira Sumaimah ɗin,saida tayi ƙira kusan sau uku kafin ta daga cikin
magagin bacci.
"Hello Sumaimah kina jina,kina ina ne,sashensa ko kuma naku?"
"Uhmm ina ɗakinmu"
"Dan Allah ko zaki daurewa kizo,idan nace zanzo wajenki hakan zai zama abin
magana,ya jikinnaki?"
Saida tayi jimma kafin ta amsa,wanda hajiyah maryam ɗin rasan kunya taji da kuma
mamakin ya akayi ta sani,amma wannan bashine a gabanta ba dan haka ta basar.
"Ehh.....zan iya zuwa,bacci ne ma ya ɗaukeni"
Bayan ta kashe wayar bayan gida ta shiga,da alama wasu dabaru zata haɗawa Sumaiman
saboda jikinta.
Lokacin datazo ta ƙyar ta haɗa ido da hajiyah maryam,ita a dole kunyar ta
takeji,ita dai bata ce mata komai ba,har ta gama wankan ta fito.
Wunin ranar Sumaimah a sashen hajiyah maryam ta wuni,duk wani abu ita tayimata,tun
tana noƙewa har ta saki jikinta,musamman dataga hajiyah maryam din batayi mata
labarin abinda ya farun ba.
A bangaren Sumaimah kuwa da tunanin Ahmad ta wuni,shin yana ina,ko ya zasu cigaba
oho,shin zai sake yarda ta shiga sashensa ma kuwa? Tasan yanacan yana ɗorawa kansa
laifin abinda ya aikata mata.
SADI-SAKHNA CEH
09035784150
ku tuntubeni domin biyan kuɗinku ko ƙarin bayani.
*SANADIN CACA*
-BOOK 2 (PAID)
Mallakar *SADI-SAKHNA*
09035784150
Bismillahir-rahmanir-raheem
Ki biya kan ki karantamin na biyu dan Allah. ga number ta nan mai son littafi na
ɗaya yayi min magana zan bashi shi kyautane.
*BOOK 2*
...26...
Wajen yamma rana ta kusan faɗuwa suka shiga cikin jejin,a bakin wajen suka
tsaya,basuda wani yawa don basu wuce su goma ba,saboda binciken na sirri ne,ko
mahaifinsa baisan sun tafi ba.
Saidai sun ɗebi makamai masu hatsarin gaske.
Jejin Ahmad yake ƙarewa kallo,haka kawai ya tsinci kansa dajin kaman yasan wajen. I
donsa ya rufe yaja wata iska mai nauyi,haka ido a rufen yafara tafiya a cikin
jejin.
Sudai sauran sojojin binsa suke a baya har suka iso bakin wani ɗutse,babu kowa a
wajen,amma kuma suna jiyo motsin wasu na tahowa ta bayan dutsen.
Hakanne yasa Ahmad yayiwa tawagarsa alamar suyi baya cikin duhuwar jejin su shirya
kai farmaki.
Yana nan tsaye ya saita duk wanda ya zo ya harbeshi,wasu mazajene manyan manya guda
huɗu,kana ganinsu kaga shu'umai suka bayyana,suma tasu bingidar tana ɗane,domin da
alama kaman yanda su Ahmad suka ji motsinsu suma sun ji nasu motsin.
Na gabanne yafara sauƙe bindigar tareda yiwa na bayan magana.
"Kai ku sauƙe ogah gojene fah ya dawo"
Jin sunan yasakasu sauƙe bindigoginsu tareda matsowa,gaisuwa suka miƙa masa tareda
cewa.
"Ogah ya dai sai yanzu ka dawo,ai har anyi taro ganin shuru shuru baku dawo ba yasa
akayi tunanin duk cikinku babu wanda ya rayu, Don 2 a ranar na naɗa sabon Don3 amma
mu bayyi mana ba,dama muna fatan dawowarka"
Duk maganar da suke Ahmad binsu kawai yake da kallo,sai a sannan maganar wancan
barawon da suka kama ta dawo masa,da kuma maganar Sameer shida Abbansu. Kenan dai a
rayuwar da yayi baisani ba a wajensu yayi aiki,Allah yasa ma ba kayan sojojine a
jikinsa ba da sun ganeshi.
Ɗaya daga cikinsu ne ya dawo dashi daga tunanin daya tafi,ta hanyar jan hannunsa
zuwa cikin sansaninnasu.
Suna tafe yana binsu a baya batareda yace komai ba har suka isa Wani ɗaki.
Shiga sukayi ya bisu,ba ɗakin kwana bane,domin hadda kujera da table a ciki.
Don 3 yaji sunce a gaisuwar da sukayiwa wanda yake kan kujerar,shima ƙatone amma
bakaman su ba,saidai ya fisu murɗewar jiki.
"To ogah mai guri yazo mai tabarma sai ya naɗe,ogah goje ya dawo,dama matsayinsa ne
a ka baka"
Daga yanda suke maganar ya tabbatar kam ba sonsa suke ba a shugabannasu.
"Wanne zancen banza kukeyi haka,kunyi farautar da aka saka kune,nida idona naga
goje an soka masa wuƙa,dan haka bai tsira da ransa ba"
Matsawa sukayi daga gaban yayi arba da goje,wanda yake sanye da baƙaƙen kaya da
bindiga a hannunsa.
Firgit ya tashi yana rarraba ido,ashe da gaske sukeyi dai.
Ganin yafara kame kame ne yasa Ahmad ƙarisawa gabnasa tareda yin murmushi.
"Lahh ogah kada ka damu fah,ni yanzu ma inada wasu yaran mun kafa tamu
ƙungiyar,saboda lokacin da abin yafaru na bugu,na manta komai na rayuwata,iya kawai
sunan ƙungiyar ne yazo kaina da kuma inda take shiyasa nazo"
Wani washe baki yayi tareda cewa.
"Ahh toh abu yayi ƙyau sosai,nayi zaton ai kazo ƙarbar matsayinka ne"
"Ahah bashi nazoyi ba,nazone dai wajen Don 2,saboda na tuna zamu haɗu dashi idan
muka dawo a raye,sannan kuma nazo nuna masa mutanen dana haɗa,sun ƙware sosai a
wajen iya aiki,bansani ba ko zasu samu karbuwa suma a........."
"Ahah mai zai hana,dama munyi rashin mutane sosai a harin da muka kai waccar
shekarar,tunda kai ka kawosu to munsan babu matsala.
Kai me kuke jira,ku basu masauki mana shida mutanensa"
Yafaɗa yana bawa wanda suka rako Ahmad ɗin umarni.
"Goje in bazaka damu ba za'a baku masauƙi ku zauna kafin na aikawa da shugaba saƙon
cewar kazo"
"To shikenan bakomai,ni barina je nayima mutanennawa magana"
Bayan ya koma wajen daya bar su Eemran bayani yayi musu akan plan ɗin ya sauya,zasu
saje da barayinne su san komai nasu kafin su kai farmaki.
Hakan kuwa akayi,dan har kaya suka sanja irin nasu,saidai ba kaman yanda sukayi
tunani ba,zasu kai kusan kwana uku kafin wanda suke jira yazo.
Sumaimah (POV)
Bayan Ahmad ya koreni daga sashensa na daɗe a lambu ina tunani,ina ganin fitowarsa
ya ɗau mota ya bar gidan.
Tunda yanzu aikin sashensa ya ƙare,lokacine daya kamata dama na farka daga yi masa
abu batareda yasan koni wacece ba,yanzu zan fara aikin da hajiyah Maryam tasakani a
sashen hajiyah Mammah. Domin itace sanadin dukkan waɗannan abubuwan,da badan itaba
da yanzu na faɗamasa cewar nice matarsa,wani lokacin saina kusan subutar baki sai
na tuna da rayuwar ɗana,idan tagano shima tarwatsa rayuwarsa zatayi kaman ta
mahaifinsa.
Gyara fuskata nayi na nufi sashen hajiyah Mammah.
Tana zaune akan dadduma a tsakiyar falonta,jikinta lullube da babban mayafi kamar
kullum.
Sallama nayi da amsa a nutse,tsugunnawa nayi tareda karkatar dakai.
"Hajiya barka da hantsi ya jiki jikin?"
"Lafiya kalau ƴar nan ya haƙuri da rayuwa"
Hawaye na ƙaƙalo yafara zubomin,wanda bakomai na tuna na zubar dashi ba sai korar
da Ahmad yayimin ɗazu.
"Hajiyah ki taimakeni kaman yanda Allah ya taimakeki, Yallabai nake yiwa aiki,babu
abinda banayi masa,yau da safennan ya koreni wai kada nasake nuna masa fuskata,na
tambayeshi mai ya faru yacemin wai kawai ya gaji danine.
Gashi inada ɗa da kanwa da innata a ƙauyenmu wanda nake tallafawa,miji kuma ya tafi
nema har yanzu shuru bai dawo ba"
Kuka nake kaman raina zao fice,inaji tana cemin nayi shuru amma banyi niyyar
tsayawa haka ba,saina amayar duk abinda na ƙunsa kwanannan.
Saida naji zuciyata tayi sakayau kafin tanafara rage kukan ina jan majina.
Mai akinta Kaltum ta ƙwalawa ƙira,sai gata kuwa tafito daga wani ɗaki.
"Zo kalutume ga wannan yarinyar daga yanzu zata dunga tayaki aiki anan sashen na
ɗauketa aiki"
"To shikenan hajiyah za'ayi yadda kika ce"
"Karki damu ki dunga aikin anan sashen,saidai idan zakiyi min aiki banda gulmace
gulmace,sannan banda rawar kai,duk da naga bakiyi kamada mai hakan ba dama, ki
kwantar da hankalin ki zan biyaki,yanda zaki kulada ƴan uwanki,Allah yaƙara
rufamana asiri"
"Ameen ameen hajiya,nagode nagode sosai,kaman yanda kika taimakeni kema Allah yayi
miki hakan"
Nadaɗe ina kwararo mata Addu'a godiya,ina cikin hakanne kaltum tasake shigowa
tareda raɗawa hajiyah Mammah wani abu a kunne.
Ɗan zaro ido tayi tareda sauya yanayin fuskarta.
"Kin bata maganin amma taƙi sha,mai take nufi kenan,dashi zata zauna har a sani?
Kice mata ta sameni a ɗakina yanzunnan"
Daga haka ta sallameni suka shiga ciki. Ko basu fadaba nasan zancene akan cikin
Mulaifah,nasan dai bazata taba faɗamusu ba,in kuwa suka gane kenan ya wuce wata
biyu.
Ina nan zaune a wajen ina nazari naga Mulaifah tafito daga ɗakinta zata shiga na
gaji Mammah ɗin,harara ta bankamin,tayi wata rama ga fari data ƙara kamar wata
fatalwa.
Murmushin mugunta nayi kafin na fito daga sashen,hmmmm danma bata san nina lalata
mata shirinta ba kenan.
Ban nufi sashen hajiyah Maryam ba saina nufi namu,yanzu dole na rage shiga wajen
hajiyah Maryam ɗin,idan har inaso nasha lafiya.
∆∆∆
Su Ahmad har sunyi kwana uku a cikin sansanin barayi,yauɗinne kuma suke saka ran
zuwan shugaban kungiyar na biyu wato Don 2.
Abubuwa da dama da suke shirin yi da kuma wanda sukayi babu wanda basu sanar da
Ahmad ba,hakan ba ƙaramin dadi yayi masa ba,ganin ya samu dukkan labaran dayake
buƙata cikin sauƙi.
Abu ɗayane dai har yanzu bai sani ba shine sanin shugaban ƙungiyar na ɗaya da kuma
na biyu.
Wannan kaf cikinsu babu wanda ya sani.
Dare ya fara,kowannne lokaci Za'a iya ƙiran Ahmad su gana da Don 2,a zaune yake
shida su Eemran suna plan yanda komai zai kasance.
"Ka gane Eemran ku tabbatar kun saitasu dukka bindiga,sanann gurnet dayake kakkafe
yazama cikin ready,so nake mu tashi wajennan a yau bayan munkama shugaban,kada kowa
ya tsira da ransa a cikinsu.
"Angama shugaba"
Suna gamawa aka zo ƙiransa ya fita.
Wani ɗaki aka bi dashi,wanda tsawon kwanansu uku na gidan basu taba shigaba.
Yanada matsakaicin girma kuma yasha ado kamar ba'a cikin kogon dutse ba.
Wani mutum ne a zaune yasha suit baƙaƙe,ɗan dattijo ne domin yafara manyanta,magana
yake a waya lokacin da suka shigo,sannan fuskarsa da wata baƙar mask tana sheqi.
Bayan ajiye wayar cire mask ɗin yayi tareda juyowa cikin taqama.
"Barka da dawowa jaki na mijin gaske goje,naji daɗin cewar kana raye,domin ko babu
komai nasan jakar da muke nema tana hannun ka,sannan........."
Caff ya tsaya da bayanin ganin wanda yake tsaye a gabansa.. Yana zare ido.
Shima Ahmad ɗin a bangarensa tun lokacin daya juyo ɗin kafeshi da ido baya ko
motsawa saboda razanar ganinsa a wajen.
"Gen. Buhari Bello wanda suke cewa Uncle BB,Aminin mahaifinsu ne tun suna
ƙanana,suma tare suka tashi suka gansu. Komai da AM Aliyu zayyi sai yayi shawara
dashi,amma.......what yana ɗaya daga cikin wakilan ƙungiyar datake maƙiyarsu a
barikin sojoji??
"General mai kake anan badai kaine goje ba??"
Kafin yagama tantancewa Ahmad ya saitashi da bingida,yayinda ya danna wata makunna
a hannunsa,aikuwa wajen ya kaure da ƙarar bindigu da tashin gurneti.
SADI-SAKHNA CEH
09035784150
ku tuntubeni domin biyan kuɗinku ko ƙarin bayani.
*SANADIN CACA*
-BOOK 2 (PAID)
Mallakar *SADI-SAKHNA*
09035784150
Bismillahir-rahmanir-raheem
Ki biya kan ki karantamin na biyu dan Allah. ga number ta nan mai son littafi na
ɗaya yayi min magana zan bashi shi kyautane.
*BOOK 2*
...27...
Duka da naushi Ahmad yake kaiwa Gen Buhari Bello,shima ramawa yakeyi kasancewarsa
tsohon soja,ga Don 3 ya buge bindigarsa tun ɗazu.
Ganin faɗan ya ɗauke musu hankaline yasa don 3 ɗauke wayar Gen BB ya fita.
Sun daɗe suna faɗan kafin Ahmad yasamu nasara akansa,ta hanyar ɗaukar bindigar
tasa,saita shi yayi da ita yana haki.
"Miye alaƙarka da wannann kungiyar,dama tsawon lokacin nan amanar sojoji kake
ci,irinkune kesa a dunga yiwa jami'an tsaron ganin marasa gaskiya koh.......
(kwafɗama sa ƙasan bindiga yayi saida ya faɗi)........kaine don 2 to wanene
shugaban ƙungiyar,inaso ka faɗamin yanzunnan kokuma na jajjage kanka da bindigar
nan"
Cikin ƙaraji da tashin hankali yake maganar.
Wata dariyar baka isa ba gen BB yayi wa Ahmad,cikin sauri yasaka ƙaramar wuƙa ya
yanke wuyansa da itah,yana kakarin mutuwa Ahmad ya jefar da bindigarsa ya ƙarisa
wajensa da sauri.
Tallafoshi yayi a razane,ga jini yanata zuba a wuyansa,abin har yakai ya kashe
kansa akan yafaɗa masa wanene shugaban ƙungiyar nan?
"Yaaa....rrro kenan,mai amfanin na faɗamaka tunda nasan dama mutuwa zanyi idan ta
gano kasanni........bazaka taba sanin wacece itttt.......ba"
"Dama macece ka faɗamin, wacece w......"
Shuru yayi tareda sakinsa ya koma gefe,ganin ya riga ya mutu,abin yayi matuƙar
razana shi sosai.
Wayarsa ce tayi ƙara,hannunsa yana rawa ya ɗauka ganin Eemran ne.
"Hello sir mungama dasu,saidai wannan shugabannasu mun sameshi yana waya da wani"
"What definitely shugabarsu yake faɗawa mai ya faru"
"Eh nima nayi tunanin haka,na harbeshi a kafaɗarsa da dama"
"Ohh yakamata mu tafi,abin bai tafi yanda ake so ba,amma dai Alhamdulillah hakan ma
mukeda nasara"
∆∆∆
Mun daɗe muna tattauna,wanda duk yawanci gargaɗi hajiyah Maryam takemin akan nayi
taka tsantsan, lamarin,tunda yanzu yafi nada muni,ga zaman dazan ƙarayi a sashen
hajiyah Mammah,domin inkana son kama damisa dole saika shiga sansaninsa.
A ranar Ahmad yadawo daga yankinnamu,anyi murna sosai da nasararsa ciki kuwa harda
hajiya Mammah,kaman ba fadarta ya ruguza ba. Musamman A.M Aliyu ba ƙaramin farin
ciki yayi ba da nasarar. Ana ta murna amma bandani,domin wajen zamannawa na kullum
wato lambu na tafi na zauna. Zuciyata nason ganin Ahmad domin nayi kewarsa
sosai,amma kuma ina tuna kashedin da yayimin na cewar kada na kuskura nasake nuna
fuskata a gabansa.
∆∆∆
Bayan sati ɗaya da wannan nasarar da gen Ahmad yasamu nutsuwarsa ta ɗan dawo ba
kaman da ba,saidai duk da haka yakasa tsintar kansa da jin komai ya ƙare. Koda yake
dama yasan akwai sauran rina a kaba,tunda har yanzu bai kama shugabar ƙungiyar
ba,amma tunda yasan macece yanzu zarginsa kashi tamanin a cikin ɗari yana kan
hajiya Maryam ne,don abinda yake kwanannan kenan saka mata ido na shige da
ficenta,domin ya kula tashiga cikin tashin hankali da abinda yafaru,sannan ta tsiri
zama cikin busy.
Biron hannunsa yake dannawa yana ɗagoshi,duk da hakan akwai wani abun da babu.
"Ohhh that girl why....meyasa nake missing ɗin matar wani,kaddai na fara son matar
da bazata taba zama mallakina ba kai,ahah no ba sonta nake ba,inajin haushi ne da
kuma zunubin abinda na aikata mata"
Cije cije yake yace wancan yace wancan shi kaɗai,a iya sati guda daya wuce gabaɗaya
yaki ko gidan baya son komawa,domin yana shiga zaiji yana so ya ganta,wanda kuma
yasan bazai gantan ba,shida kansa ya bata umarnin kada ya sake ganinta a inda yake.
Kai inaga barin ƙasar zayyi naɗan wasu watanni ko zaiji daɗi,dama abbah yabashi
hutu tunda yasamu wannan nasarar.
Yana cikin wasiwasinne Eemran ya shigo office ɗin.
"Eemran kayimin arrenging na zuwa hutu gobe"
"Ogah anya kuwa hakan zayyi wu,don an fitar da aiki daga headquater,kuma naga hadda
kai a cikin wanda zayyi supervising"
"Supervising ɗin me"
"Uhmm a cikin trainee ɗin aka dauka masu ƙwaxo zaku tafi dasu Russia na tsawon wata
Uku"
Komawa jikin kujerar Ahmad yayi tareda sakin dogon numfashi.
"Yaushene tafiyar?"
"Gobene ogah"
"Ohk"
Abin yabawa Eemran mamaki,yayi tunanin zaice bazai jeba,amma saiyaji sabanin
haka,kenan so yake yabar garin kota wacce hanya.
Washagari bayan an gama tsara zaman sojojin a jirgi sun tafi kafin manyan suka bisu
a private jet,duk cikinsu Ahmad ne kaɗai ƙarami.
Lokacin dazai taho ko ƴan gidan bai fadamusu zai tafi ba,iya Neelah ce kawai tasani
sai Saleem.
Masauƙinsa aka kaimasa kayansa, bayan ya watsa ruwa yasaka riga marar nauyi ta shan
iska.
Fitowa yayi wajen cin abinci,amma shi a hadene da sauran ƙananan sojoji.
Bayan ya zauna an saka masa abinci,har zai fara cin abinci yaga wani yazo ya zauna
a opposite ɗinsa,mamaki abin yabashi,dan yasandai baizo dasu Eemran ba bare su
zauna.
Ɗagowa yayi suka haɗa ido da wani matashi,zaiyyi shi a haife,kallon rashin sani
yake masa,amma kuma sai yaji kamar ya taba ganinsa. Shima kallonsa yake ko ƙiftawa
bayayi,sai can kafin yace.
"Goje mai kakeyi a nan,bayan batanka kaima soja ka shiga,amma meyasa baka faɗi inda
kake ba,kasan kuwa halin da Sumaimah tashiga a sanadiyyar rashinka?"
Maganar da bawan Allahn yayine ta dakeshi da ƙarfi,zaro ido yayi tareda ajiye
cokalin yana kallonsa.
SADI-SAKHNA CEH
09035784150
ku tuntubeni domin biyan kuɗinku ko ƙarin bayani.
*SANADIN CACA*
-BOOK 2 (PAID)
Mallakar *SADI-SAKHNA*
09035784150
Bismillahir-rahmanir-raheem
Ki biya kan ki karantamin na biyu dan Allah. ga number ta nan mai son littafi na
ɗaya yayi min magana zan bashi shi kyautane.
*BOOK 2*
...28...
Number dakinsa kawai yabashi tareda yimasa alamar ya sameshi a can ɗin,
Yagane mai yake nufi kuwa,sai yayi shuru da zancen akan zai sameshi a ɗakin.
A zaune yake da labtop akan cinyarsa lokacin da musbahu yayi sallama a ɗakin,bayan
ya zauna shuru sukayi babu wanda yace komai,saida suka ɗan ja kaman mutuna kafin
Ahmad yayi masa magana.
"Naji kana magana akan goje,ga dukkan alamu kasanni lokacin ina a matsayinsa,kuma
kasan inda na zauna"
Kallom mamaki Musbahu yabi Ahmad dashi kafin yace.
"Ya kake magana kaman ba kaine goje ba,shin mai yake faruwane,ka rasa hankalin ka
ne a hatsarin dakayi,shiyasa ka manta komai,amma bakayimin kamada wanda ya rasa
hankalin sa ba"
"Eh ba hankalina na rasa ba,nayi recovaring hankalina ne,saikuma na manta rayuwar
danayi a wanda kake faɗa. Kafin muce komai zanso nasan wanene kai kuma menene
alaƙata dakai a rayuwar bayan.
Sunana Ahmad Aliyu,General under Investigation division"
Zaro ido Musbahu yayi jin matsayin da Ahmad ya faɗa.
"Shin mafarki nake kokuma idan har kaine goje yaushene kayi karatu haka,a sanina
dai dabanci kakeyi da kuma aiki ma ƴan siyasa. Sannan kana nufin baka ganeni
bane,nine fah Musbahu yayan Sumaimah matarka,duk da bakaje wajen ɗaurin aurenba
amma ai muna haɗuwa a gari san......."
"Bangane wanne labari kake min ba,kaine yayan matata,kuma banje wajen ɗaurin aure
ba,meyasa toh? Barina baka labarin abinda yasa bansan kokai wayeba,sannan inaso ka
bani labarin abinda yafaru daga farkon rayuwata a wannan gojen dakake faɗa har
ƙarshe,harma da labarin ita matar tawa."
Bayan yabashi labarin abinda yasameshi ya rasa hankalin sa har yayi rayuwa a
matsayin goje,ba ƙaramin mamaki yabawa Musbahu ba. Shima labarin rayuwarsa daya
sani a matsayin goje ya faɗamasa,da yanayin aurensa da kuma yanda Sumaimah tasha
wahalar zaman aurensa harda tafiyar dayayi ya barta.
Abin ba ƙaramin tayarwa Ahmad hankali yayi ba sosai,shin dama haka yake a rayuwar,a
ina zai samo wannan baiwar Allah,mai zaice da ita irin wannan abun daya jawo mata.
Kama kai yayi tareda jan numfashi,tsawon lokaci ya ɗauka yana jimamin abinda ya
aikata.
"Zan shirya komawa gida gobe,zamu tafi ka nuna min itah"
"Ahah hakan bazai yiyu ba general,duk da nasan kai ogah ne,amma inna bika zan samu
matsala a nawa training,nayi ƙoƙari sosai kafin na samu wannan matsayin.
Sannan kuma ita kanta wacce kake son zuwa wajenta bata nan,ta tafi garin abuja
aikatau,saboda bayan tafiyarka hatta makarantar daka biyamata kuɗinta had ta gama
sun hanata certificate,duk wani abu mutane sun washe ganin an ɗau shekara baka dawo
ba,shiyasa ta tafi neman abinda zata rufamusu asiri"
Wani irin sanyin jikin Ahmad ya sake jin wannan batun,gabaɗaya ya rasa mai yake
masadaɗi.
Wunin ranar gabaɗaya ƙareshi sukayi Musbahu yana yimasa labarin goje,batun zuwa
wajen Sumaimah kuwa sun barshi akan suna komawa zasu nemi inda take yaje.
∆∆∆∆
Sumaimah {POV}
Yau tun safe na tashi da tashin zuciya,abu kaɗan sai naji zanyi amai,da sabuluna
nafarayi a banɗaki.
Bayan rana tayi har sannan ban saka komai a cikina ba,saboda banajin son komai.
A zaune muke nida ummi bayan mun gama aikin ranar,inata magana niban kulaba ashe
kallona takeyi,ɗaga mata gira nayi da alamar lafiya.
"Lafiya kalau,kawai naga kin sauyaminne kwanannan,duk da ke farace amma ƙin ƙara
fari,ga wayan bacci dakikeyi,komai inkin fara saikice kin gaji"
Maganganun da ummi tayi dukka nima na kulada su,amma babban abin tashin hankalin
shine abinda na zarga,wanda ban kawo shiba sai yanzun.
Wani zabura nayi nai banɗakinmu da sauri,a gaban madubi na tsaya ina kallon
kaina,mamana na kalla wanda naga sun ƙara girma,rabonsu da haka tun inada cikin
Sayyid.
Zaro ido nayi tareda shafa cikina,rabona da al'ada wata biyu kenan,wayyo mai nake
tunda ban kulaba sai yanzu.
"Innalillahi yanzu ya zanyi kenan,kenan ciki na samu a ranar? Mai yasa dukka biyun
suka faru a rashin saninsa,nasan wannan zaisan nasane,amma da wanne zai kalleshi
shine tashin hankalina,ahhhhh"
Ƙarar danasaka ne yasa ummi yin magana daga cikin daki.
"Sumaimah lafiyarki kuwa?"
"Ba komai ummi"
Fitowa nayi daga bnaɗakin ina rarraba ido,yanzu wazan tunkara da wannan zancen
kenan,nasan hatsarin danake ciki nida wannan cikin Allah ne yasan iyakarsa. Don
yanzu su hajiyah Mammah babban burinsu shine gano ni wacece,tunda yanzu babu komai
ya ruguje. A bangaren hajiyah Maryam kuwa kullum ƙara rauni takeyi,Neelah kuwa
batada lokacin kanta tunda Ahmad ya tafi ya barmata ragamar hidimominsa.
Hanyar sashennasa na nufah,haka kawai na tsinci kaina dayin hakan.
Buɗewa nayi na shiga,alamun rashin mutum duk sun nuna a wajen,har ƙura ta taru a
falon.
Ina shiga naji wani ƙamshi a falon,wannan wanne turarene haka dayaƙi washewa tsawon
wata biyu.
Ɗakin na bude na shiga,nan kamma har yafi falon,dan ji nayi wata nutsuwa tana
sauƙamin.
Duddubawa nakeyi ina neman turaren,saida na shinshina dukka turarensa amma ban
jishi a ciki ba.
Wardrobe ɗinsa na buɗe,inda ya lanƙaya kayan daya saka a gefe,a jikinsu turaren
yafi yawa,ɗakkosu nayi ina shinshinawa,na daɗe ina abu ɗaya,sai daga baya nagane
ina abu tamkar kuliyah. Kuma mai wai tsaya,kenan ba turare hancina yake shinshinowa
ba,guminsa ne,yaushe na zama mai iya shinshino yanda gumin mutum yake?.
Ajiye sauran kayan nayi na ɗauki riga ɗaya na boye,kan gadonsa na faɗa,ahhh nan ma
jinayi kamar yana kai. Nice nake kewarsa kokuma ɗan cikina duk bai shafen ba,tunda
naji daɗin kwanciyar bacci zanyi kawai.
Bacci nayi na ƙoshi sai don kaina natashi,amma duk da haka banji ya wani isheni
ba,mitstsike ido nayi,sai sannan na hango gari ta window yafara duhu.
What bacci nayi na kusan tsawon awa shida ko biyar.
Banɗakin sa na faɗa da sauri nayi alwala,mayafin kaina na yaye nayi sallah kafin na
fito zuwa kitchen ɗinsa ko zan samu abinda zai iya shiga cikina.
Tundaga lokacin dana gano inada ciki,sai yazama kamar hurashi akeyi,tsorona ɗaya
nasan zayyimin girma fiyeda na sayyid,dan daga ganinsa ma.
Nashiga damuwa sosai da lamarin,ga banida waya ta faɗi a ruwa bare na ƙira inna na
faɗa mata.
Kullum inna tashi da safe sainayi shiri mai kyau,gashi na tsiri saka hijabi da kuma
ɗaurin zani akan cikin. Sati uku da fara laulayin har na rame na yi fayau.
Fitowa nayi daga wanka kware kwaren danayi,to wankane babu sabulu,towel ne a jikina
ina gogewa ruwan,kullum a banɗaki nake shiryawa,amma yau dayake naji su ummi suna
aiki a babban falo shiyasa ban yi a banɗakin ba.
Motsin tafiya naji,hakan yaa na rarumi hijabina na saka.
"Dama kin ajiye hijabin,wannan boye boyen ya isa haka,nariga nasan cikine dake
malama,inna tacemin wai ai mijinki ya kawoki ziyara,shine daga bada tsarabar ciki
sai ya tafi,bazai tsaya a gaisa ba?"
Sauƙe ajiyar zuciya nayi bayan naji bayanin ummin,kenan daman sunsan inada
ciki,musamman abinda inna ladiyo tafaɗawa ummi,yayi min daɗin matuƙa,kuma ya kareni
daga amsa tambayoyi.
"Miye kikayi wani tsaye kamar gunki,kije sashen hajiyah Maryam wai tana
nemanki,inna ladiyo ce tace na faɗa miki"
Karisa shiryawa nayi cikin doguwar riga ta atamfa,nasaka hijabina na tafi.
Kafinnan saida nabi ta wajen inna ladiyo tukunna tana kitchen.
"Inna dama kinsan......."
"Haba ƴar nan,muna tare a ɗaki ɗaya har mu kasa gane halinda kike ciki? Abinda zan
faɗamiki shine ki daina wannan boye boyen haka,wanda yasani yariga yasani,wanda
baisani ba kuma zaki jawo hankalin sa ne yasaka ayar tambaya"
Ɗaga mata kai kawai nayi batareda nace komai ba,kuma maganar tata haka ne.
"Kije hajiyah Maryam tana nemanki a sashenta"
"Toh"
Shine kaɗai amsata kafin na wuce can din,sai a lokacin naji rashin kyautawa ta,don
rabona da sashen nayi sati biyu,wasan buya nayi tayi da ƴan gidan,saboda karsu gane
inada ciki.
Magana naji sunayi tun kafin na shiga,da waye haka suke surutu.
tura ƙofar nayi na shiga,wani saurayine amma ba zai wuce shekara sha bakwai ba.
Daga yanda suke maganar zaka gano cewar ɗan uwanta ne.
"Wai huzaif yayar babanka nake fah ba kakarka,tashi to ku tafi gatanan ta shigo"
Dukkansu kallona sukayi itada shi,kallo ɗaya mutum zayyi masa ya gano kamar da suke
da hajiya maryam,tunda tace yayar banbansa to ɗan Taheer ne kenan,babban dansa.
"Okay ni barina je waje,ki sameni a mota"
Rabawa yayi zai wuce tagaba na hajiyah Maryam tayi masa magana.
"Kai banason sakarci,bata girmeka bane da bazaka gaisheta ba"
Cikin ɗaɗɗagawa irinta masu sabuwar samartaka ya gaisheni,nidai na amsa a taƙaice
ya fice. Ƙarisawa nayi muka gaisa da hajiya Maryam,sunkuyar da kaina nayi,don naji
kunya sosai.
"Hhhh yau kuma kunyata kikeji,kijr zai kaiki gidansu ne akwai wanda zaki haɗu
dasu,bansan ko ki kwana ba ga wannan ki riqe,amma ki tabbatar ki dawo gobe. Kije
maza Allah ya tsare,ki kula sosai dan yanzu ba kaman da ba,na fadamasa
kada yayi tuƙin ganganci"
Nidai da toh na amsa mata dakuma godiya. Saikuma kaina a ɗaure shin dawa zan haɗu a
gidan da ban taba zuwa ba..
A haka dai na bi bayan wanda taƙira da huzaif ɗin zuwa motarsa. Ina shiga ya tayar
da itah ya hau hanya ko magana bayyimin ba.
SADI-SAKHNA CEH
09035784150
ku tuntubeni domin biyan kuɗinku ko ƙarin bayani.
*SANADIN CACA*
-BOOK 2 (PAID)
Mallakar *SADI-SAKHNA*
09035784150
Bismillahir-rahmanir-raheem
Ki biya kan ki karantamin na biyu dan Allah. ga number ta nan mai son littafi na
ɗaya yayi min magana zan bashi shi kyautane.
*BOOK 2*
...29...
Bayan mun shigo gidan fita nayi daga motar ya nufi wajen parcking,ina nan tsaye ina
kallon ƙyauye naga ya wuce ta gefena,baicemin na biyoshiba nabi bayansa da
sauri,wani falo muka wuce kafin mukazo wani daban. Bai shigaba da hannu ya nunamin
na shiga,shikuma yayi wani wajen daban.
Kaman wata baƙuwar kaza haka na kutsa kai ina rarraba ido.
Wazan gani inna ce da deeja dakuma Sayyid.
Suman tsaye nayi ina kallonsu,har deeja ta rungumeni banyi motsi ba,wannan wanne
irin bazata ne haka. Nayi kaina tambayar,in suna haka tsaf zasu saka kaina yin
kwancewa.
"Innaaa......"
Shine kawai abinda nasamu faɗi,dariya sukayi tare,har matar danake tunanin matar
ƙanin hajiyah Maryam ɗince,wacce suke cewa Hajiya Shukurah.
"To anan dasu bazaki iso ba,duk mamaki ne yanaki motsawa"
Da sauri nazo inda inna take na rungumeta da ƙarfi,kukan Sayyid naji yana jan
hijabi nah.
Juyawa nayi na tsura masa,kama naga yanayi da hajiyah Maryam,kodan nasan yanzu
jikantane,amma idon kam na ubansa ne. Tureni yake yana tiro baki,waina matsa a
jikin inna. Dariya abin yabani,wannan kam halin babansa ne.
Hannu nasa na ɗaukeshi,zuciyata cike dason yaron,wai dana riqeshi saina tuno
labarin hajiyah Maryam,gaskiya ba ƙaramin azantuwa tayi na sosai.
Kallona yake yaƙi sakin jikinsa dani,deeja tana matsowa ya miƙa mata hannu. Dariya
abin yabani,wato har ya mantani kenan. Inna na kalla tareda haɗe rai.
"Inna kiga ya mantani,laifinki ne bakya bashi labarina"
"Ohh jimin,labarinki ma kike cewa,keda kika figeshi a nono kika gudo saboda duniya
tamiki zafi,kuma ma dakike can ɗin wani rainonsa kike daya miki zafi. Kinshigo
gidan mutane ko gaishesu bakiyi ba kina ta danki koh"
Maganar da tayine yabani kunya,kuma fah ban gaisheda matar gidan ba.
Cikin rusunawa na gaisheta,dariya tayi kafin ta amsa.
"Lahh kada ki damu Sumaimah,ai kinyi kewarsune shiyasa. Dan ma kada ki damu anan
zasu zauna"
Kallon inna nayi da sauri,anan zasu zauna kaman yah. Ta gano wanne tunani
nake,saita bani amsa.
"Nice nake neman wacce zata tayani aiki,shine Anty Maryam tacemin daman tanason
inna ta dawo da aiki,sune suka zauna a sashen hajiyah Mammah suka raini Ahmad itada
Inna ladiyo. To bazata manta dasu ba har abada."
Cikeda murna dakuma mamakin dama ashe inna tasan Ahmad tun yana ƙarami na kalleta.
Murmushin manya tayi kafin tace.
"Kiƙara mata godiya har deeja zata saka a makaranta,dama nayi tunanin tafiya da
itah zan koma garinmu,to saiga mota wai ƙira daga hajiya,shine muka taho"
Bayan na gama godiyar wani abune ya fadomin.
"Inna meyasa zaki tafi garinku"
"Hmmm wata shida kenan da gaji ta matsawa baba audu kan cewar ya siyar da
sashenmu,yanzu haka wanda suka siya sun matsa mu tashi"
Wani takaicine naji yazomin wuya nah menene haka mutanennan suke nufi. Duk kuma
wajen bai zama gadon inna ba,ɗanta ya mutu ita tuminin takaba kawai za'a
bata,sannna Ahmad ba ɗan ta bane.
Ɗakin da aka bawa inna muka koma,anan sabon hira ya buɗe.
Deeja na kalla tana shirya kayansu,hankalin yarinyar yabani mamaki,dan lokacin dana
tafi ba wani har can bane,yanzu ta zama tamkar uwar Sayyid komai wajenta yake zuwa.
Yau jina nake tamkar an tsundumani a aljanna,abu kaɗan saina kallesu na sake
kallonsu,jinake kamar na maidasu cikina.
Labari kuwa har raba dare mukayi munayi,nasu gaji da kuma gidanmu.
Bayan mun gama hirar Deejah tayi bacci itada Sayyid tashi nayi na shiga banɗaki.
Bayanna fito rigata na cire nayi sama da zanin,ina shirin kwanciya naji maganar
inna.
"Shin kun daidaita ne a tsakaninku?"
"Uhmm ni dawa?"
"Zaki fara wannan juyar da maganar kamar baki gane ba, mijinki mana nake nufi"
"Ahah bamu shirya ba,har yanzu baisanni ba"
"Baisani ba ya akayi kuma naga ciki a jikinki"
Shuru nayi na rasa ma mai zance mata.
"Uhm.....inna uhmm lokacin baya cikin hankalin sa ne,wata tabashi magani sai shine"
Ganin na duburburcene yasa ta juyar da kanta tareda cewa.
"Allah ya kyauta,ya daidaita ku bisa lokacin daya dace"
Ameen nace a hankali daga nan na kwanta.
Da safe bayan mun tashi nice nayi aikace aikacen gidan dukka,bayan mun gama karyawa
muna zaune hajiyah Shukurah tashigo da waya a hannunta.
"Sumaimah ga kira nan daga hajiyah Maryam waiki koma driver yazo ɗaukarki"
Zaro ido nayi kaman zanyi kuka,dan har raina gidan ya isheni sosai,don ba yadda
zanyi ne. Dan kwana ɗaya danayi dasu inna har naji daɗi,gashi bangama ganinsu ba
kuma zan tafi.
"Uhm hajiyah ki bata haƙuri dan Allah na ƙara"
"Ahah ki koma kici gaba da aikinki,bakya tunanin a halin da kike ciki zamanki
kusada su ma hadari ne,dan haka ki koma kici gaba da kula Allah yakiyaye,matsalar
hajiyah Mammah tariga tasan take a matsayin wacce tasan mai take ciki,zamanki kusan
danginki zaisa ta binciko dawa kike tare."
Ɗaga kai nayi alamar na fahimta. Badan naso ba na shirya komawa.
Naso tafiyah da Sayyid amma nasan bazan fara wannan gangancin ba mai suna gani
kasheni,dan haka sallama nayi musu na dawo.
Tun a hanya naji kamar banje ba.
Watan su inna ɗaya kenan da dawowa,amma bangansu sosai ba,sai nayi tabi kafin
hajiyah Maryam ta barni naje.
I zuwa wannan lokacin cikin jikina ya fito,saboda girman dayakeyi nan da nan,don ya
shiga wata na huɗu a satinnan.
Ana Sayyid saida yayi kusan wata bakwai kafin yakai haka,amma shi yanzu haka yakai
kusan cikin wata bakwai a matan da basa girman ciki.
Kowa a gidan yanzu yasan inada ciki,saidai ban damu ba,saboda duk a zatonsu na
mijina ne daya tafi rani.
Ita kanta hajiyah Mammah har kyauta takemin,tareda cewa mijina bai kyauta ba daya
barni da ciki yasake komawa. Nidai saidai nayi murmushi nace uhm.
Bayan nayi sallahr asuba bacci nakoma mai shegen nauyi,gashi nayi wata ƙiba saboda
yawan cin abinci kaman gara,cina har ya wuce na cikin Sayyid. Ummi har boye
abincinta take inta ganni,inna ladiyo ce da hajiyah Maryam haka hajiyah Mammah suke
bani abinci duk sanda suka ganni.
Bayan na miƙe daga kan katifar madubi na ɗauka na kalli fuskata,taƙara fari da
ƙiba,haka ma jikina. Ƙafafuna kam ba'a magana.
Wanka na shiga ina fitowa nasaka doguwar riga,daga cikin materials ɗin da hajiyah
Maryam ta ɗinkamin saboda goyon ciki,naji daɗinsu kuwa sosai ba kaɗan ba.
Ummi ce tashigo ɗakin ina shafa mai,hijabi ta ɗauka tasaka da kuɗi a hannunta.
"Ke kuma fah ina zuwa haka,nasan baki fiye zuwa aike ba,an fi tura mai gadi
shikaɗai"
"Hmmm wai Yallabai ne zai dawo shine inna tayimin lissafin abinda zan siyo,Sannan
kuma ki faɗamin mai kike so zaki haɗamasa"
Zaro ido nayi tareda kallonta,wanne yallabaiɗin badai Ahmad ba,gabaɗaya na manta da
ashe zai dawo,bana tunashi sainazo kwanciya na rungume rigarsa tukunna.
"Kinga tsaya tsaya basai kinje ba zanje"
"Ke dalla kimin lissafi naga bake kika sakani ba, yanzuma daga sashensa nake na
gyara,kina bacci ɗazu na ɗauki key"
Kallonta nake da mamaki,nasan inna ce tasakata,itama kuma tana tausayina nasan.
Rungumeta nayi ina zuba mata godiya,ba ƙaramin daɗi naji ba data gyara ɗin.
"Nagode ummi,barinaje na dudduba sashen,sannan na gyara kitchen ɗin. Kafinnan zan
miki lissafin abubuwan"
Lokacin dana shiga sashen tsaf yake ta gyarashi koni zanyi iya haka.
Saidai ɗaki da kuma banɗaki dana ɗan ƙara gyarawa.
Kuɗi da yawa hajiyah Maryam tabawa inna ladiyo na abincinnasa,ni kaina shaidace
yanda take ji dashi a cikin ranta.
Hmmm koya zamu kaya nidashi idan ya dawo,shin wacce amsa zan bashi ne idan yayimin
tambayar miye a jikina.
Kitchen ɗin na gyara na fitar da abinda zanyi amfani dashi.
Ina cikin haka ummi ta dawo,sosai ta tayani har muka gama aikin wajen daya na
rana,lokacin kam nasan anty thing a kowanne time zai iya dawowa,da sauri muka
ƙarisa nabar sashen,domin banaso ya dawo ya sameni,ban shirya ganinsa a yau ɗin ba.
Lokacin da muka koma daki nayi sallah waje na samu na zauna ina haki tareda sauke
numfashi,don ba ƙaramin gajiya nayi ba,jikina nauyi yakemin kwanannan.
Ruwa mai sanyi ummi ta miƙomin tareda ajiye abincin mu a tsakiyar ɗakin.
Saida na zuqe ruwan naja ajiyar zuciya kafin nace.
"Kai gaskiya ummi a tafawa ruwa,ruwa rahama ce,mai rowar ruwa ya cika marowaci"
Dariya tayi kafin tace.
"Ehh lallai yau gana mai yiwa ruwa santi,haba kema da laifinki,ji yanda kika dage
kina yimaza aiki kaman wani mijinki,ko wanda kike aure bakya yimasa bautar da kike
masa,Sannan abinda yabani mamaki ban taba ji kince ga salary ɗin ki ba. Ko yake
shima wannan mijinnaki da nice da tuni ai munyi wacce zamuyi,na taho aikatau domin
mu rufawa kanmu asiri,amma shine hakan bai isheka ba ka biyoni kayimin ciki ka
haɗani da wahala,inama zan ganshi da sai na tsayar masa"
"Hhhhh ummi kinada abin dariyah,zaki iya tsayar masa idan na hadakun?"
"Ehh mana bari ki gani Allah ya kaimu"
Murmushi nayi batareda nasake cewa komai ba na saka hannuna a abinci.
Muna gamawa na kishingiɗa domin na kwanta na huta.
*SANADIN CACA*
-BOOK 2 (PAID)
Mallakar *SADI-SAKHNA*
09035784150
Bismillahir-rahmanir-raheem
Ki biya kan ki karantamin na biyu dan Allah. ga number ta nan mai son littafi na
ɗaya yayi min magana zan bashi shi kyautane.
*BOOK 2*
...30...
A jirgi ɗaya Musbahu suka taho shida Ahmad,zaibi normal jirgi ya hanashi akan zasu
taho tare. Don a dan wannan wata ukun da sukayi sunyi sabo sosai,wanda duk sanadin
labarin Matar sa ne.
Bayan sun sauƙa kowa jawo jakarsa yayi suka fito.
"Toh general ni daga nan zan hau motar gida"
"Ahhh habadai,kazo muje gida mana ayi ka huta in yaso gobe saika wuce,sannan ya
zancen .......dakace zaka haɗani da itah,gashi numberta tunda ka bani kullum saina
gwada amma ban sameta ba"
"Shiyasa nakeson tafiya gida ai general,saboda nasan inna tasan inda take zata bani
address ɗinta. Sannan karka damu na gode da dukkan halaccinka,inna dawo nayi maka
alƙawarin zanzo har gida,saimu je inda take tare."
"Yaushe zaka dawo,nan da sati biyu za'ayi bikin nasararku"
"Eh kafin lokacin zan dawo Inshaallah"
Sai bayan da Musbahu ya shiga motar garinsu kafin driver yazo ɗaukar Ahmad zuwa
gida.
Sashensa ya wuce direct ta ƙofar baya,dan tun abinda ya faru yakejin kamar shida
ƴan gidan basu hada wani jini na azo a gani ba. Mahaifinsa ne ɗan uwansu to baya
raye,dangin mahaifiyar sa kuma na can wani gari daban,daɗin daɗawa kuma basa Ga
maciji da su.
Ɗan tsayawa yayi daga bakin ƙofa yana kallon yanda aka gyara ɗakin,Sumaimah ce ta
faɗo masa a rai,yasan babu mai wannan aikin sai itah.
Ɗaki ya wuce ya ajiye jakarsa ya watsa ruwa.
Falon ya fito yana dadanna waya,daga idon da zayyi suka haɗa ido da saleem,wanda
yake hakimce akan kujera yana kallon yayannasa.
Hade ido yayi ya kafeshi dasu kaman shine babba,abin ba ƙaramin mamaki yabawa Ahmad
ba.
"Kaikuma fah ya haka'
"Dole ka tambaya mana yah Ahmad,yanzu baka gidannan tsawon wata uku ka dawo amma ka
wuto sashenka kawai,ƴan cikin gida nacan suna zancen"
"To so what suyi maganar ma,dama sun damu dani ne,kaima in zancen dazakamin kenan
to kama hanyarka kayi waje"
Jijjiga kai Saleem yayi tareda jan numfashi,yana son yayannasa kuma wani lokacin
baya ganin laifinsa,yanayine yasakashi zama hakan.
Wajen dining ya nufah ya buɗe kulolin,ƙamshin abincine ya bugeshi saida ya lumshe
ido.
Zama yayi ya zuba abincin yaci yayi nak,ko ci kanka baicewa Saleem ba,yayinda
shikuma ya zuba masa ido yana cin abincin kaman ya samu tv.
"Hmmm kana cewa ba ruwanka da yan aiki gashinan kuma kazo ka ci abincin mai aikin
gidan.
Ni inaga ƙoƙarinta ma,da ciki tayi maka wani gyaran sashe da kuma abinci,saikace
mijinta"
Yana cikin goge bakinsa ya cakk jin abinda Saleem yafaɗa,ciki ciki kuma wanne iri .
"Saleem mai kake cewa cikine da wa?"
"Sumaimah mana mai aikinka,ohh da kanace budurwace,naga dama ka fara nuna kishi
akanta,tun wuri gwanda ka bari,naji an ce cikine da itah,mijinta yazo ganinta sai
gata da ciki,lallai wannan miji ya iya bugu sosai"
Wani zimmm kan Ahmad yayi,a ransa yana ta maimaita Allah yasa dagaske na mijinnata
ne bashine ba.
Gumin daya keto masa ya goge tareda cewa,
"Cikinnata zaikai kaman ya"
"Oho nina sani,naji dai ana cewa yayi babba kawai"
Duk da abinda Saleem ya faɗamasa hankalin sa bai kwanta ba.
Wayarsa ya ɗauko ta gida wanda takeda layinsa na nigeria..
Ƙiranta ya farayi amma shuru bata shiga,haka har ya Haƙura don kansa.
Faɗawa yayi zurfin tunani Gabaɗaya ya gagara barwa kansa cikin jikinta ba
nasane,kai yasan ma nasane.
Hannun Saleem yagani yana yawo akan fuskarsa,hakanne yasakashi firgit ya dawo
hankalin sa.
Tashi yayi zaune yayi hanyar ƙofar dazata shigar dashi cikin gidan.
"Ina kuma zakaje ogah ta wannan ƙofar?"
"Zan shiga na gaisar da mutanen gidanne sarkin tambaya"
Sakin baki yayi saida yaga ya shige kafin yabi bayansa,a bangarensa kuwa don ya
haɗu da Sumaimah zai shiga.
Ba kowa a babban falon gidan sai Sameer wanda yabada hankalin sa gabaɗaya kan wayar
hannunsa..
Jin shigowar mutum yasa ya ɗaga kansa,yana ganin Ahmad ne ya cigaba da harkar
gabansa.
"Don kana zargina meyasa bazaka zo gaba da gaba ka tuhumeni akai ba,saika dunga
binciken hakan a bayan fage?"
Ajiye wayar Sameer yayi jin topic ɗin da Ahmad ya ɗauko.
"Hmm menene abin zuwa gabanka na faɗamaka,bayan nasan bazaka fadamin gaskiya ba.
"Taya zan faɗamaka gaskiya bayan nima a lokacin bansan ta ba? Zarginka gaskiya ne
amma ba yanda kake tunani bane. Nine wanda mukayi faɗa dakai harka cakamin wuƙa"
Yafaɗa yana ƙarisa maganar tareda buɗe masa gefen cikinsa.
Zaro ido Sameer yayi,yayinda fuskarsa ta nuna rashin jin ɗaɗin yanda yayi masa
raunin,amma shima ai ya dukashi sosai.
Shuru sukayi babu mai cewa komai,sai can kafin Ahmad yace.
"In kanada kokwanto ka daina kawai gaba,ka tunkareni dashi"
Yana gama faɗin hakan yayi masa ɗan Murmushin kwarewa.
Duk maganar da suke Sumaimah na jinsu,wacce take tsaye cak tayi suman wucin
gadi,jikinta rawa yake wanda ta ɗauki tiren,kaddai Ahmad ya tuna rayuwarsa ta
goje,in kuwa hakane to zai ganeta tana shiga.
Har ta juya zata koma taji muryar Sameer.
"Yadai naga kin tsaya kuma zaki koma,ko kin manta wani abune,sauri nake fah zan
fita"
Shigowa tayi kanta a ƙasa,ta gefen ido tana kallon Ahmad wanda ya tashi zai fita
daga falon,da alama bai san zata shigo,saidai tunda ya riga ya tashi kawai ya fice.
Yazo giftawa ta gefenta tayi ƙamshin turaren datake shaƙa kafin tayi bacci a
jikinsa,wannan har yafi wancar shigarta,nutsuwa da kasala ya sauƙar mata a lokaci
guda,har bata san lokacin data ja dogon numfashi ba.
Sai bayan ya wuce ta dawo hankalin ta kafin ta kulada Sameer wanda yake binta da
kallon mamaki.
"Yadai naga kin tsaya ido rufe kaman mai addu'ar kirista,idan bakya jin daɗi waye
yace kiyi aiki?"
Bata bashi amsa ba sai ajiye masa abincin da tayi ta fita,gaba ɗaya tunda yanxu sun
gane tana aure kuma harda cikin basa yin maganar da sukeyi da,kuma ma cikin ya
maidata marar magana,ga yawan gajiya.
Bayan ta fito daga falon har zata wuce taga Ahmad tsaye a bakin shiga
sashensa,diriricewa tayi zata yi hanyar kitchen da sauri,sai kuma taji muryasa.
"Kizo yanzu ina son magana dake"
Daga haka ya shige ciki. Ajiyar zuciya tasake tana bin ƙofar da kallon. Banda sunan
Allah babu abinda take ambata.
Tiren ta mayar kitchen kafin ta dawo zuwa sashennasa,zuciyarta cikeda zullumin
yanda zasu ƙare,tasan dole yaji labarin cikinta kokuma ma yagani da idonsa.
Tura ƙofar falon tayi ta shiga,yana zaune akan kujera yana kallo,amma daga gani
kasan hankalin sa baya kan kallon.
Ɗauke idonsa yayi daga kan tv ya mayar kanta,tasan bakomai yake dubawa ba sai yanda
ta sauya sosai. Duk da hijabine a jikinta amma dole a gane hakan.
Saida tazo kusada shi kafin ta zauna a tsakiyar falon tana kallon tiles..
Takai minti biyar a haka kafin ta ɗago,desame ita yake kallo har zuwa lokacin.
Saida suka haɗa ido kafin yayi magana..
"Shin ban cancanci kimin bayani ba,cikin waye a jikinki. Ni kokuma mijinki? Karki
bani amsar daba haka ba,domin idan kika boyemin dole zan gano gaskiya domin zanyi
binciken mijinnaki a garinku nagano hakane koba hakane ba. Dan haka ki amsa min
*cikin waye?*?"
Shuru Sumaimah tayi bata bashi amsa ba,banda rawa da jikinta yake ba komai..saboda
yanda yake kausasa mata murya.
"Na mijinki ne?"
Ɗaga masa kai tayi
"Na wane?"
Nan ma ɗaga masa kai tayi,daka mata tsawa tayi kagin tana bashi amsa guda biyu.
"Ki bani amsa da bakinki cikin waye a jikinki"
A yanzun bude bakinta tayi tareda cewa.
"Cikinka nehhhh"
Runtse ido yayi tareda komawa jikin kujerar ya lafe,shidama hakan yayi tunani,yasan
babu wani mijinta,tayi hakanne domin ta boye,kuma hakan yayi domin zai ara masa
lokacin mai ya kamata yayi.
"Innalillahi wa inna ilaihi raji'un"
Shine abinda yake ta maimaitawa idonsa rufe..
Kallonsa Sumaimah tayi tareda fara hawaye tana jijjiga kai.
"Cikin shege dashi zan fara ajiye jinina a gidanmu,da wanne ido zan kalli mutane
kenan,shin ke kanki mai zancemiki bare mijinki *KAICO NAH* (littafina na huɗu,wanda
ya tara ɗumin darasi kenan mai yamin magana).
Da wannan zunubi da kuma ɗanyen aiki dana aikata,shi kanshi ɗan na cuce shi
na..........."
"Ya isa haka"
Shine abinda Sumaimah ta faɗa da ƙarfi tareda ƙara sautin kukan ta.
"Kada kasake faɗin hakan akanka da kuma ɗan cikina,domin dukkanku baku cancanci
wannan bayaninnaka ba sam,idan laifine ma nice mai laifin kuma na ɗauka,sannan ciki
dama ban dangantaka dashi ba,duk da cewa kaine mafi kusantuwar dashi.
Duk abinda kakeji akansa kanada damar kaji,amma na roƙeka kada kasake furtamin
wannan kalmar. Ka ɗauka tamkar wannan abin bai faru ba,ta hakanne zaka manta dashi
ka koma tamkar yanda kake. Sannan yanda kake daukan abubuwan ba haka suke ba.
Zan dawo aiki gobe,saidai bazan dunga shigowa ba sai ka fita,haka kafin ka dawo
bazaka ganni ba,ba'a samu wata mai aikin ba shiyasa,kafin a samu zan dena."
Tana gama faɗin hakan ta miƙe daga zaunen da take tana goge hawayen fuskarta,harta
kai bakin ƙofah taji maganar sa a cikin dashashshiyar murya.
"Watansa uku kenan"
"Eh"
"Lafiya kike"
"Eh"
Kici gaba da jira amma dolene zan ɗau mataki akai,zan nemi mijinki akan
maganar,dolene na karbi hukuncin abinda na aikata,abin yayi muni dayawa"
Wannan karon Sumaimah bata bashi amsa ba ta fita,tana jin yanda muryarsa ta karye
tayi raunin ba ƙaramin tausayinsu take ji ba a wannnan alaƙar,daga itah har
shi......
Fatanta Allah ya bata lafiyar cigaba da kulada jaririnnasu,Sannan kuma yabata da
sauƙi.
Ɗazun bataso faɗa masa cikinsa bane,gudun kada yayi bincike ya gano komai ne yasa
ta amsa masa da eh ɗin.
*SANADIN CACA*
-BOOK 2 (PAID)
Mallakar *SADI-SAKHNA*
09035784150
Bismillahir-rahmanir-raheem
Ki biya kan ki karantamin na biyu dan Allah. ga number ta nan mai son littafi na
ɗaya yayi min magana zan bashi shi kyautane.
*BOOK 2*
...31...
Anyi sati guda da Ahmad ya gane cewar Sumaimah tanada cikinshi,kuma har zuwa yanzun
hankalin sa bai kwanta ba,har mafarki yake mijinta yasaka masa wuƙa a wuyah,abinda
yake bashi mamaki kuma mijinnata kamarsu ɗaya dashi,saidai yana zuwa masane a salo
na daba.
Yau ma tun Dare abinda ya kwana yanayi kenan,da asuba bai koma bacci ba,karatun
qur'ani yayi tareda neman gafarar Allah bisa wannan dumbin zunubi nasa.
Da wuri ya fita daga gidan, gabaɗaya abubuwa sun isheshi.
Lokacin dayaje office babu kowa a headquarter sai masu shara da gyare gyare,aikin
dayake kansa ya dauka ya fara,ko zai rage abinda yake cikin ransa.
Wajen misalin ƙarfe sha biyu yaga kira a wayarsa,sunan Musbahu yagani,dama yana
expecting kirannasa tun jiyah amma shuru.
Yana ɗagawa sallama sukayi yace masa.
"Yah Musbahu naƙira ka baka ɗaga ba,gobene fah za'ayi bikin baku matsayin"
"Oga wanann yayan da kake ƙirana dashi na kasa sabawa dashi,gani fah a ƙofar
headquater bansan office ɗin ka ba"
"Okay ka tsaya ganinan zuwa yanzu"
Ajiye aikin dayake yayi ya fita daga office ɗin,binsa wani squad na ma'aikata
sukayi,dama yana ciki,babu wanda yaga ya fito tunda suka zo.
Da sauri sauri ya fita harabar wajen,daga nesa ya hango Musbahu a tsaye wajen da
ake parking motoci.
Tun daga nesa daya ganshi ya taho daga wajen suka yi gaisuwar musabaha.
"Barkanka da zuwa muƙarisa"
"Lahh ogah da basai ka shigo bama,in ka yimin kwatance ma zanzo"
"Ahah karka damu ƙarisa,bayan abinda yake tsakaninmu inayi maka kallon aminina ne"
Tafiya suke suna tattaunawa har suka isa,ruwan sanyi yabashi don shine abinda
yakeda shi a office ɗin.
"Ga ruwa kasha hanya,barina ƙarisa wannan saimu tafi gida kaci abinci"
"Zan sha ruwan dai abinci kam daka barshi,dan har nayi booking na hotel,muna
gaisawa zanje na sauya kaya sai mu haɗu. Har yanzu ina kiran wayar ta ma baya
shiga,bansan meyasa ba. Hmmm inaga akwai matsala........."
Jim Musbahu yayi daya faɗi hakan,wanda hakan yasa Ahmad bashi dukkan nutsuwar sa
donjin wacce matsala ce.
"Basa garin,daga innan da Deejah dakuma Sayyid,na tambayi matar gidan kuma tana
cemin wata baƙar motace tazo ta daukesu wancan watan zuwa nan abuja,bansan waye
ba ,amma jikina na bani ko gidan da Sumaimah take aikine"
"Amma kana gani wanne wajene haka,mai ya faru dukka suka tafi gabaɗaya,basusan inda
suke ba address ɗinsu?"
Cikeda damuwa Ahmad yake tambayar,gaba ɗaya hankalinsa ya tashi. Ji yake duk
laifinsa ne dabai nemeta ba,gashi har ta shiga duniya neman aikatau saboda rashin
abinyi.
Rarrashinsa Musbahu ya fara yi ganin yanda hankalin sa ya tashi,don yasan kansa
yake ɗorawa duk laifin abinda ya faru. Shikansa ba ƙaramin tausaya masa yayi ba,ace
ka yi rayuwa da mata harta haihu amma baka sani ba,to amma meyasa ya kasa tunawa.
Shine wasi wasin da Musbahu yakeyi,wanda shima Ahmad yayi irinnasa.
Sun dade suna zance duk akan matar tasane,saikuma wanda yake damunsa aransa na
Sumaimah.
"Bakomai Musbahu karka damu,Inshaallah Allah zai bayyana su. Yanzu dai muje gida
tukunna daganan sai mu wuce gidan tv bada information ɗinsu,da kuma radio,maybe
idan sunji ko wani yasansu ya ƙira. Ga matsalar babu hotunansu."
A motar Ahmad suka fita daga headquater zuwa gidansu.
Direnct sashensa ya wuce dashi basu shiga cikin gidan ba.
Shidai Musbahu binsa yakeyi a baya,don ya damune ma yabiyoshi,sannan shima yana da
buƙatar son ganinsu,musamman Deejah wacce yakejin kaman nauyin kulada itah a kansa
yake.
A falo yamasa iso ya zauna,motsin mutum yaji a kitchen,sannan kuma babu abinci a
dinning,sai sannan ya tuna ya rage awa guda hadda rabi akan lokacin
dawowarsa,ajiyar zuciya yayi yasan abinci take,koba komai zata fiddashi kunya,da
har yayi niyyar kuwa hanata yi masa aiki,yanzu ma daga ya samu matarsa sai Yanda
zayyi da case ɗinta.
Kitchen ɗin a yashiga ya sameta a kan stool tana wanke kwanukan da tayi amfani
dasu,a gefe kuma ta jera kayan abincin a kan tire,da alama tagama gyara wajen take
kafin ta tafi.
Aikinta take a hankali ko kuladashi batayi ba,hakanne yabashi damar ƙare mata
kallo,tayi fari tayi ƙiba fiyeda da,wanda kuma yasan cikinne ya sakata,don gashinan
yafito a jikinta,dayake doguwar rigace a jikinta,kuma ta fara kamata saboda cikin.
Kyau tayi masa a hakan,inaga matarsa take masa wannan hidimar da cikinsa a jikinta.
Inama matar dayake ta nema ce. Wani runtse ido yayi tareda jijjiga kai,ahah wannan
matar wani ce wanda yaci amana.
Tabon dayake zuciyarsa na abinda ya aikata ne ya dawo sabo.
Jinginar dayayi a jikin ƙofar kitchen ɗinne yasaka ƙofar yin ƙara,wanda kuma ya
ankarar da Sumaimah wacce kanta yake sunkuye,kallonsa take da alamar mai ya dawo
dashi a lokacin.
Lokaci guda ya tsime tareda yin gyaran murya.
"Nayi baƙo ne mun dawo dashi,zan ɗauki cup ne na shan ruwa,sannan idan kin gama
abincin ki kawo shima yanzu"
Yana gama faɗin hakan ya ɗauki cup biyu a inda ta jera ya fita,itadai da kallo
kawai tabishi tareda tabe baki.
Gabaɗaya ya dagula mata lissafi da ƙamshin jikinsa,wanda yake rikitata,aman da take
ji ɗazu ma yakoma.
Bayan ya fita cigaba tayi da wanke wankenta,saida ta gama kana ta ɗau kwanukan
abincin da saka su plate da komai zata kai musu.
Lokacin data shiga da Ahmad suka haɗa ido,saboda shine yake facing kitchen
ɗin,shikuma baƙonnasa ya bawa kitchen ɗin baya,magana taji sunayi akan yaɗa
labarinta ko za'a sameta,har zuwa taje ta ajiye kayan abincin akan dining table,
juyowar da tayi zata tafine idonta ya sauƙa akan Musbahu,yayinda shima itan ya
kalla a lokacin daidai yakai gorar ruwa bakinsa.
Dawowa yayi dashi da sauri tareda zare ido.
"Sumaimah!!!!"
"Yah Musbahu"
Itama ta faɗa cikeda mamakin ganinsa a nan ɗin.
Ahmad ne ya kalleshi tareda cewa.
"Kasanta ne?"
"Itace fahh dama kuna tarene tuntuni?"
"Itace wa,muna tareda itah a ina?"
"Mai kake nufi,bakasan wacece ba,ko aljana ce kai ni kaɗai nake ganinta,Sumaimah ce
fah matarka wacce ka bari ka tafi. Itace muke nema"
Da wani mungun sauri Ahmad ya kalleta a razane,ganin kallon dayayi matane yasakata
sauƙe idonta,wani kuka ne da batasan na menene ba ya kufce mata,dama abinka da
yanayinta ya koma na kukan.
Zuba mata ido sukayi dukka ganin yanda take ta kuka kaman an daketa.
Musbahu ne yayi ta mazan yi mata magana.
"Mai aka miki kuma kika fara kuka,zo nan ki faɗamin mai yake faruwa"
Takawa ta farayi kaman wacce ƙwai ya fashewa a ciki,ta gaban Ahmad ta wuce zuwa
inda Musbahu yake,shidai binta yayi da kallo kaman ya samu tv. Tun daga tambayar ko
kwaƙwƙwaran motsi bai ƙara ba.
"Miye ya faru da wayarki nayi ta ƙiranki bata shiga,ya akayi kike zaune da mijinki
amma bai san ke bace,yana can yana nemanki. Ina kuma su inna suke,domin dana koma
gida an ce suna garinnan?"
"Uhm uhm wayar ta baci banda wata kuma,su inna kuma suna gidan Hajiyah Shukurah
ƙanwar hajiyah Maryam. Ta ɗauki inna ne aiki,kawu audu ne ya koresu bayan tafiyarsa
(tafaɗa tana kallon Ahmad kafin ta ɗauke idonta). Tunda wai dama wajen ya zama
nasa. Ina baba yake dasu Ammi?"
"Baki ƙarasa bani amsata ba Sumaimah,meyasa dakika haɗu da mijinki baki faɗamasa ke
wacece ba,ko rashin ganeki da yayi ne yasa kika ƙullaceshi akan sai sanda ya sani
da kansa?"
Jijjiga kai tayi da sauri tareda cewa.
"Ahah ba haka bane,ba a son raina naƙi faɗamasa ba,saidan yazama dolen,mutanen da
suka yi sanadiyyar zamansa a goje suna tareda shi,idan suka sanni wacece bazasu
ƙyaleni na dakuma shi,shiyasa ban faɗamasa ba"
"Mut......."
"Dan Allah kada ka tambayeni dalili yah Musbahu,inasu baba da ammi baka faɗamin ya
suke ba.......baka ga Deejah ba tayi hankali kaman ba itah ba"
Tayi hakane domin ta kawar da maganar ɗazun,duk da tasan hakan bazayyi yu ba.
Ganin kallon da Ahmad yake yiwa Sumaimah mai cikeda abubuwa da dama yasa Musbahu
cewa..
"Suna nan ƙalau,yanzu dai bani address ɗin inda su inna suke,ni yanzu zan tafi,kina
buƙatar yin magana dashi"
Jimm tayi jin abinda yace,amma haka ta bashi ba yanda zatayi.
Kitchen ta koma tanajin fitarsu shida Ahmad ɗin.
Hannu ta ɗora akan zuciyarta wacce take bugawa fatt fatt.
A bangaren Ahmad kuwa da Musbahu yace zai tafi kasa hanashi yayi,domin a yanzu
burinsa ɗaya shine jin bayani daga bakin Sumaimah,na akan me ta ƙi faɗamasa
matsayinta a wajensa.
Ganin har suna shirin rabuwa Ahmad baice komai ba yasa Musbahu cewa.
"To ni zan tafi gen. Ga yanda abu ya kasance,amma ni abinda nake gani ka bita a
sannu ta faɗamaka mai yake faruwa,ni kaina shaidane akan irin son da take maka a
lokacin baya,bata haɗaka da komai,duk da mutane suna jin tsonka amma kaine wanda
take burin komawa gareshi idan tayi nisa dashi"
Da kalamai masu dadi cikin hikima ya taushi Ahmad kafin ya tafi ya barshi,yana musu
fatan shiryawa mai ɗorewa.
Kaman jira yake yana tafiyah ya koma sashennasa,bai sameta a falon ba,har yaji babu
daɗi kaddai tafiya tayi,sai kuma ya gano ƙofar kitchen a buɗe.
A kaban kitchen table ɗin take tsaye tana kallon window,ta bawa ƙofar baya.
"Can you explain your self please?"
Tajishi sarai amma bata juyo ba,wani kukan tasake fashewa dashi har yafi na ɗaxu.
"Am sorry am sorry please i....i can't..........."
*SANADIN CACA*
-BOOK 2 (PAID)
Mallakar *SADI-SAKHNA*
09035784150
Bismillahir-rahmanir-raheem
Ki biya kan ki karantamin na biyu dan Allah. ga number ta nan mai son littafi na
ɗaya yayi min magana zan bashi shi kyautane.
*BOOK 2*
...32...
SADI-SAKHNA CEH
09035784150
ku tuntubeni domin biyan kuɗinku ko ƙarin bayani.
*SANADIN CACA*
-BOOK 2 (PAID)
Mallakar *SADI-SAKHNA*
09035784150
Bismillahir-rahmanir-raheem
Ki biya kan ki karantamin na biyu dan Allah. ga number ta nan mai son littafi na
ɗaya yayi min magana zan bashi shi kyautane.
*BOOK 2*
...33...
Bayan an gama jan jinin an ɗaura mata kafin aka barsu suka shiga.
Zuwa lokacin anyi mata allurar bacci.
Fatee ce a zaune a gefen kanta sai su Sameer a tsaye,Sumaimah kuma na gefe a zaune.
Can kaman an ɗan daɗe ta fara juya kanta kaɗan kaɗan.
Fatee da Maimuna ne suka ɗan ɗagota tareda saka mata pillow ganin tana ƙoƙarin
tashi.
Idonta akan Ahmad ya sauqa wanda shima ita ɗin yake kallo cikeda soyayya irin ta ɗa
da mahaifi.
Sannu sannu su Sameer suka mata,fatee kam rungumeta tayi tana kuka.
"Mommy bakida har haka amma baki faɗamin ba har kwanciya fah kikayi"
"Kin damu ki sani ne,miye ya dameki banda kanki uhm"
Hajiyah Maryam tafaɗa tana dafa kanta..
"Habadai mommy you know i love you"
"Umm naji i love you too,yanxu dai ɗagani bake kaɗai bace a ɗakin koh?"
Ƙin matsawa tayi saida ta tureta tukunna,sai turo baki take kaman zai faɗi.
"Sannu Ummee jikinnaki yanzu"
Ahmad yafaɗa a nutse cikin kulawa.
Murmushi tayi tareda ɗaga masa kai.
"Ummee ya jikin?"
"Alhamdulillah Sumaimah....kinci abinci kuwa?"
"Ahah"
"Tabb Ahmad ka ɗauketa ku tafi gida taci abinci,batayin awa uku ma bataci ba,cikin
jikinta mai neman abincine"
"Ahah yau banajin yunwar zan zauna har a sallameki saimu tafi"
Cikeda rigima tayi maganar,wanda hakan yasaka hajiyah Maryam haɗa rai.
"Ahah ku tafi nima yanzu zan tafi idan jininnan yaƙare,uhm yau kuma a wanne bawan
Allah aka ɗauka?"
"Mommy yah Ahmad ne yabayar,yaushe kuka shirya dashi da har yabaki jini kuma ya
kawoki asibiti,ga waccar mai aikin sai wani kula kike da ita kamar wata mai
muhimmanci"
"Buge bakin Fatee hajiyah Maryam tayi tareda cewa.
"Ƙaniyarki da ce mata ƴar aiki,tunda har kunga ya haka yakamata kusan mai yake
faruwa.
Ahmad ɗanane na fari kafin na haifi Maimuna,sannan ita kuma matarsa ce wacce ya
aureta a lokacin da yayi shekara biyar baya nan. Tanada ɗa mai sunan mahaifin Ahmad
kuma yayan babanku wato Muhammad,ana ƙiransa da Sayyid.. (Ta faɗa tana kallon
Sumaimah. Wannan suma itan suka kalla cikeda mamaki)
Wannan shine abinda baku sani ba,sauran boyayyun labaran kuma sai daga baya. Sannan
wannan maganar banaso tabar wajennan,akwai wanda sanin hakan a wajensu daidai yake
da shiga hatsari dukkanmu"
∆∆∆
"Sani kuma na nawa Maryam,lallai kin raina wayona da kuma abinda zan iya sosai"
Hajiya Mammah ta faɗa wacce take zaune gabanta dauke da ƙwaryah wacce take ganin
abinda yake faruwa a ɗakin asibitin.
Muje zuwa..........
SADI-SAKHNA CEH
09035784150
ku tuntubeni domin biyan kuɗinku ko ƙarin bayani.
*SANADIN CACA*
-BOOK 2 (PAID)
Mallakar *SADI-SAKHNA*
09035784150
Bismillahir-rahmanir-raheem
Ki biya kan ki karantamin na biyu dan Allah. ga number ta nan mai son littafi na
ɗaya yayi min magana zan bashi shi kyautane.
*BOOK 2*
...34...
∆∆∆
Bayan gama bayanin tashi Ahmad yayi akan zai mayar Fatee da Sumaimah gida,in yaso
gobe saisu dawo.
Sun fita kenan sukaji hajiyah Maryam tafara jijjiga kamar zata karya gadon da take
kai..
A rikice dukka suka juyah kanta tareda da daddane sassan jikinta..
Sukam su Fatee kuka suka fashe dashi ganin abinda takeyi.
Jini ne yake fita ta hancinta,yayin idonta kuma ya koma fari soll kamar ba'a taba
halittar ƙwaya daga cikinsa ba.
Ahmad ne yayi ƙarfin halin yin magana a wajen, sauran daga mai kuka sai wanda yayi
suman tsaye.
"Saleem maza ƙira likita yanzunnan"
To yace cikin karyayyiyar murya ya fita.
Tun kusan magriba suke abu ɗaya har dare ya fara.
Mazanne sukaje sallah,matan kuma anan gidan marayun sukayi sallah,an basu abinci ma
amma babu bakin ci.
Bayan sun dawo daga masallacin wata mota suka gani ta shigo wajen baƙa.
A.M Aliyu ne ya fito daga cikin motar a razane zuwa cikin asibitin.
Ahmad ne ya kalli su Sameer.
"Waye ya sanar dashi,yaushe ya dawo garin?"
"Bansan yaushe ya dawo ba,amma ai dole dama zai san mai yake faruwa ba,abin yayi
zafi sosai wanda da alama sai an fita da itah wata ƙasar"
"Uhm uhm ba abinda ya shafi wata ƙasar bane,da sannu zamu samu mafita"
Karisawa sukayi inda yake,yana ganinsu yazo inda suke da sauri,in mutum ya ganshi
bazaice shine dakyakykyen sojan nan ba,lallai ba ƙaramin so yakewa hajiyah maryam
ɗin ba.
Hannun Saleem ya kama tareda cewa.
"A ina aka kwantar da itan,ya jikinnata. Fatee tace wai ta daɗe batada lafiya ana
ƙaramata jini,yaune yayi tsanani sosai"
Ganin yanda yake maganar a gigice ne yasa Ahmad jijjiga kai,wato Fatee ce ta
faɗamasa mai yake faruwa,duk da an hanata,this thing is no more secret,dolene su
ɗau matakinsa da wuri. Abin tsoronsa ɗaya wacce ake tsoron da sani tariga ta
sani,abin sauƙin ɗaya batasan sunsan wacece ita ba.
"Eh batada lafiyah Abbah,ɗazu kam da sauƙi har tayi magana,daga baya abin ya rikice
sosai,amma dai likitoci suna kanta domin yin nasu ƙoƙarin"
"Tun ɗazun jikin ya rikice amma ba'a sanja asibiti ba,mai yasama aka kawota wannnan
wajen,yakama ta in fitane ma an fara shirye shirye zuwa yanzun"
"Itace batason zuwa wani asibitin,saboda batason asan batada lafiyah,Sannan da
alama jinyarta kaman bai shafi asibiti kaɗai ba,hadda na musulunci za'a haɗa,wato
islamic medicine"
"Eh to sai ayi ai dukka,yanzu dai barinaje naga jikinnata"
Yana gama faɗin hakan ya nufi cikin asibitin,waya ya ɗauko daga cikin aljihunsa,jin
ya ambaci sunan Mammah yasa Ahmad runtse ido tareda barin wajen.
Shikenan is no more sceret,duk da yasan tasan dama mai yake faruwa.
"Salam Mammah muna asibiti ashe maryam ce badata lafiyah,nima dawowata garin kenan
nasani......eh ba lallai ki sani ba wai bataso a sanine........ya kawoki wannan
gidan marayun data gina anan aka kwantar da itan. Eh shi to shikenan Allah ya
kawoki lafiyah"
Daidai ya isa wajen da su Fatee suke ya kashe wayar,duk sunji abinda ya faɗa.
Zaro ido Sumaimah tayi tareda haɗiyar yawu,batason ko yaya hajiyah Mammah tazo ta
sameta a wajennan.
Tashi tayi ta gyara mayafinta kana ta kalli su Fatee.
"Anty Maimuna ni zan koma gida naji cikina yana........."
"Ahh dama yakamata ki koma gida,kar hakan zaman ya miki illah gaki bake ɗaya
ba,kije gida kici abinci ki hutah"
"Tom barina leƙata kafin na tafi,dan Allah idan hajiyah Mammah tazo karkuyi mata
zance nah please"
Murmushi Fatee tayi tareda cewa.
"Karki damu matar bro bazamu ce komai ba,dama mai kamata kowa ya saniba sai mommy
ta warke muyi miki official introduction,kina kirki kin dace da yah Ahmad,Allah ya
barku tare"
"Ameen ya Allah nagode,Allah ya bawa ummee lafiya ya tashi kafaɗunta"
"Ameen ya Allah"
Fatee tafaɗa cikin rawar murya tana shirin kuka.
Tashi tayi zuwa wajen windown da take ciki.
An bar A.M Aliyu ya shiga inda taken,har sannan jijjiga takeyi,kodaga nesa ka gani
kasan tana jin jiki sosai.
Hawayen idonta tashare tareda cewa.
"You are not deserve this,Allah ya baki lafiyah ya saka miki. Da sannu sai taga
sakayya akan abinda takeyimiki......ina miki fatan samun sauƙi"
Sakin ƙarfen windown tayi tabar wajen.
Inda su Sameer suke ta nufah,Ahmad baya wajen.
"Saleem ina Ahmad yayi?"
Ta tambaya cikin ƙaramar muryah.
"Yaje yin wayah ne yanzu,gashi can"
Ya nuna mata ɗan gefensu kaɗan.
Ɗaga kai tayi tareda nufar inda yake,daidai lokacin ya gama wayar,kansa ya ɗora
akan saman motarsa yayi shuru.
Cikeda tausayawa take kallonsa, a yau yagane matsayinta a wajensa,a yau kuma yake
ganin kamar zai rasata,ganinta cikin wannan hali ma abune da duk wani ɗa sai yayi
da gaske ya daure.
Takawa tayi a hankali zuwa bayansa,hannunta tasaka ta saqalo ta bayansa kana ta
ɗora kanta a bayannasa.
Shuru sukayi na wasu mintunan kafin ya ɗaro nasa hannun akan nata.
"Lafiyah kike,kin gaji koh,ko yunwa kikeji,yanzu nake shirin tafiya neme muku wani
abun"
"Ahah ba wannan bane,inason tafiya ne kafin hajiya Mammah ta tarar ni a nan
wajen.....bayan haka ƙalau nake,kaifah ykk nasan kana cikin damuwa,amma ka daure ka
jure. Kowanne tsanani yana tareda sauƙi. Sannan bawa bazai zama mai miƙa lamuransa
ga Allah ba face ya jarrabeshi da gurare da dama. Idan ka jure kaci sai komai yazo
da sauƙi"
"Uhm naji bayaninki,nagode da samunki. da Sannu zan cigaba da yimata addu'ar samun
lafiyah,itakuma da take ba daidai ba Allah ya yi maganinta."
"Ameen ya Allah"
"Muje na saukeki a gida"
Hannayenta ya kama ya buɗe mata motar ta shiga kafin ya zagaya ɗaya bangaren.
Tafiyah suke babu wanda yake cewa komai,kawai hannun ta yakama yana tuƙin,ɗan
Murmushi tayi,dan ya kula yanason kama hannunnata.
Sun barin wajen driver ya kawo hajiyah Mammah itada Kultum,lokacin tara na dare
yayi.
Ta ɗau wani glass tasaka,tana tattakawa a hankali.
Hannun A.M Aliyu yakama suka shiga inda take. Tana ganin halinda hajiyah Maryam
take ta fashe da kuka tana gogewa da gefen zaninta.
"Allah sarki baiwar Allah,wannan wacce irin wahala ce haka kika gamu da itah ƴar
nan?"
"Wlh nima Mammah bansani ba sai yanzu,a she ciwon yaci ya yacinyeta. Naso ma fita
da itah,amma su yaran sun ce yakamata ayi na islamic ma,saboda abin yana kama da
kamun aljanu"
"Eh to hakane kam kace wani abun,amma kasan fah akwai wani lokacin da ciwukan
zamani sai kaga kaman na aljanu,sai anke asibiti kaga ashe zallan kamen ciwone"
"Wasu kam suna zuwa da haka,abinda yasa na yarda da maganar su likitocin munyi
magana dasu,sunce wai basuga komai ba a jikinta,ko ɗagawar da kirjinta yake sunce
basuga komai ba."
"Hasbunallah,shikenan sai a yi na musuluncin,akwai wani malami zanyi masa magana
akan matsalar"
"Hakan ma yayi,Allah ya bata lafiyan ya tashi kafaɗunta"
A.M Aliyu ya faɗa cikin damuwa.
Kallonsa hajiyah Mammah tayi tareda cewa ameen cikin ƙasan maƙoshinta.
∆∆∆
A bakin get Ahmad ya sauƙe Sumaimah,bayan yabata nata abincin,yaso rakata har
sashensa,dan shi a son ransa yafison ta kwana a can, amma taƙi yarda,haka yayi mata
sallama ya juyah.
Sashensu ta nufah,ummi da inna ladiyo sunata hira sun kunna fitila kasancewar
sannan aka ɗauke wutah,ba a kunna generator ba.
Sallama tayi tashiga ɗakin,shuru sukayi suna kallonta,ganin yadda take tafiyah
kaman an yi mata mutuwa.
"Ke kuma daga ina haka tun rana,kikaje kika ɗebo damuwa?"
Zama tayi tareda ɗora kanta a kan cinyar inna ladiyo.
"Inna ciwon hajiyah Maryam ya tashi,wannan karon har yafi nada,inna bakiga ba kaman
bazata waye safiyar gobe ba,duk da rai da mutuwa na hannun Allah"
Hannunta ta ɗora akan Sumaimah tareda jan numfashi.
"Tana ganin jarabawa kam a gun matar can,amma in Allah yasa da sauran kwananta sai
kiga komai yazo da sauƙi. Ki kwantar da hankalin ki,Inshaallah zata samu sauƙi"
Da haka inna ladiyo ta lallami Sumaimah taci abincin ta tazo dashi,hankalin ta kuma
ya ɗan kwanta ba kaman nada ba..
Dare ya fara kowa ya kwanta,amma Sumaimah gabaɗaya ta kasa bacci,sai juye juye
take,tunowa da wani abu tayi. Zumbur ta tashi Zaune tareda saka mayafinta.
Lallabawa tayi a hankali ta bude ɗakinnasu saboda karsu ummi su jita.
Ko tsoro bataji ba haka ta nufi sashen hajiyah Mammah ga duhu.
Tafiyah take kaman wata mai shiga ɗakin fatalwa jikinta yana rawa,amma taurin kai
ya hanata juyawa da baya.
SADI-SAKHNA ce
09035784150
*SANADIN CACA*
-BOOK 2 (PAID)
Mallakar *SADI-SAKHNA*
09035784150
Bismillahir-rahmanir-raheem
Ki biya kan ki karantamin na biyu dan Allah. ga number ta nan mai son littafi na
ɗaya yayi min magana zan bashi shi kyautane.
*BOOK 2*
...35...
Motsi kaɗan taji saita haska,kuma dayake tasaka hakan a ranta har muryoyi takeji
suna amsa mata kuwwa.
Key ɗin falon ta ɗakko,dan dama tana dashi saboda tana yi mata aiki.
Abinda zai bata cikas shiga ɗakin hajiya Mammah ne,wanda batasan yana buɗe ba
kokuma a rufe.
Murɗa ƙofar tayi,amma wannan kam babu zancen zai buɗe a lokacin.
Hankalin ta ya tafi wajen buɗe ƙofar,bata tsammata ba sai muryar Mulaifah taji a
bayanta.
"Ke kuma mai kike anan wajen da wannan daren"
Cikin alamar maye take maganar tana tangaɗi,kana ganinta kasan ta hau air.
Ganin hakanne yasa Sumaimah wata dabarar ta faɗo mata.
Gyara fuskarta tayi alamar damuwa kafin tace.
"Am dama hajiyah Mammah ce tace na gyara mata ɗaki,to kuma na manta ne sai yanzu
nazo,gashi bata nan banaso tazo taga ban gyaraba"
"To kuma gyaranne zakiyi shi yanzu,ina Mamman taje ta?"
"Dare bayyi bafah sosai bakya ganine,ita kuma taje asibitine hajiyah Maryam batada
lafiyah. Dan Allah kozaki buɗemin na gyara mata,yanzunnan zan gama"
Shuru tayi kaman mai tafiyah tunani kafin ta gyara tsayuwarta.
"Uhm banida key ɗinta,amma nasan tana ajiyewa a Drawer tv stand dinta,amma fah ba
ruwana in kika ɗauka,don ta hana"
Tafaɗa tana saka hannun ta a baki,kana ganinta kaga marar hankali.
Murmushi Sumaimah tayi jin barin zancen da Mulaifah take,kai dole ace giya
haramunce,Sannan tana saka mutum yin komai da aka hana.
Bayan ta shige ɗakinta wajen data kwantanta mata ta nufah. Cikin sa'a kuwa saiga
key ɗin,guda uku ne saida ta gwada dukkansu kafin ta samu wanda ya shiga.
Ɗakin duhune ƙirin,baka ganin komai,ga batada wayah bare ta haska.
"Kince zaki gyara ɗaki amma bakida haske a hannunki,ga fitila ki gyara mata kizo ki
fitah,dan bawani sonki nake ba kinsani. Ohhh"
Tana cikin maganar tasaki amai a ɗakin.
Matsawa gefe Sumaimah tayi tana kallonta,itah harta manta tana gidan ma,rabonta
data shigo gidan ta kusa wata uku,yau mai ya dawo da itah oho. Ga nan cikin jikinta
ya fito sosai.
Miƙowa Sumaimah fitilar tayi tareda yin Murmushin masu shaye shaye.
"Ahhh abinka da mai ciki tana shaye shaye,so nake ba ya mutu kar yazo da
rai,banason haifarsa ko kaɗan"
Taƙarisa maganar tana jijjiga hannunta alamar ahah.
Karbar fitilar Sumaimah tayi ta koma gefe tana kallonta,duk rayuwar data tsinci
kanta taji tausayin kanta,amma wannan ta damata ta cinye akan wacce za'a tausayawa.
Bayan ta gama magangunun ta fita jan ajiyar zuciya Sumaimah tayi tareda rufe ƙofar.
Dube dube takeyi ko zata samu wani abu daya sabawa hankalin ta a ɗakin,amma bata
gani ba har ta shafe wasu mintuna.
"Wayyo Allah nah shin ina take ajiye abubuwan ta ne? Ohh ƙarƙashin gado,anan naga
wannan fatalwar ta fito"
Tsugunnawa tayi ta leƙa ƙarshin gadon,har nishi take saboda girman da cikinta ya
fara.
Ido biyu tayi da akwatin,batayi wani tunanin ba ta jawoshi waje.
A buɗe yake sai wasu kwalabe guda biyu a ciki. Ɗayar a bude take ba komai a
ciki,sai kuma ɗayar da wani jan abu a ciki.
Ɗaga su tayi a hannunta tana kallo.
"Wannan kuma mai nene,ya nagansu a buɗe,ina abin cikin?"
Motsin mutum taji,ga fitilar da Mulaifah ta bata tana ta rawa,itama kuma jikinta
yana rawa.
Dan muryar kaltum babu makawa taji,mai ya dawo da itah yanzu.
Bakin ƙofar tazo a garin tafiyah tayi tuntube kwalbar hannunta guda ɗaya ta
faɗi,taji fashewarta kuma a lokaci guda ta taka bata saniba.
Zafine ya ziyarci ƙafartata har cikin kanta,bata tsaya duba ciwon ba ta fito daga
ɗakin,daidai lokacin da kaltum tashige ɗakinta,hakanne yabawa Sumaimah damar ficewa
daga sashen.
Muryar Kultum taji tana fadin.
"Waye anan,Mulaifah kece?"
Gudu Sumaimah ta fara jin Kultum ta biyo bayanta,wani lungu ta shiga da wasu
fulawowi a wajen. Ban nishi babu abinda takeyi,tana cikin wannan halin aka kawo
wuta wajen ya ɗau haske,Allah ya taimaketa Kultum ɗin ta wuce.
Kwalbar da take hannunta da kallah,sai yanzu ta gane ainihin kalarta,baƙace samanta
a tsuke. Wani baƙin zarene a cikinta an cika shi tamm.
Zarewa takeyi tana zubarwa har saida ta cireshi tass tukunna ta mayar kwalbar ta
rufe ta nufi sashensu.
___A bangaren Kultum kuwa ganin tabiyo sawu bataga komai yasa ta koma,a hanyar
juyawar tata aka kawo haske.
Jini tagani ya tako tun daga cikin ɗakin hajiyah Mammah zuwa waje,zaro ido tayi
tareda shiga ɗakin da gudu.
"Yau waye ya shigo sashennan?"
Shine abinda ta faɗa a razane,musamman da taga akwatin da yafi rayuwar hajiyah
Mammah kanta daraja a ƙasa a buɗe,hannu ta ɗora a ƙirjinta ta dafe.
"Nashiga uku waye ya shigo cikin ɗakinnan haka"
Waya ta ɗauka hannunta har rawa yakeyi ta ƙira hajiyah Mammah.
"Hajiyah hajiyah akwai babbar matsala fah,wani ya shigo ɗakinki ya buɗe akwatinki
na ƙarƙashin gado"
"Akwati kuma dama a bude na barshi,waye yasamu key ɗin dakina,babu wanda ya sani
banda Mulaifah,ita kuma batasan inda na saka akwatin ba"
"Hajiyah babu komai a cikin akwatin,sai wata fashashshiyar kwalbar an takata ɗakin
duk jini"
"What jini kuma? Ganin nan dawowa yanzunnan,akwai kwalba biyu a ciki ina suke?"
"Ga ɗaya mai zan abu ta fashe,ɗaya kuma bata nan"
"Wayyo nashiga uku,ganin nan dawowa yanzunnan driver zai dawo dani a darennan,amma
ba Mulaifah bace tayi?"
"Ba ita bace,tana bacci a ɗakinta, wani ne fah ya shigo,na bishi ma yagudu ɗazu"
"Kuma mai kike da kika daina binsa,koma waye sai ya karbi hukuncin lalatamin
shirina na tsawon shekara da shakeru,ganin zuwa idan wanda ya ɗauka ya lalata
kwalbar ko wanne lokaci hajiyah maryam zata iyah tashi"
"Mammah keda waye kike magana haka naji hankalin ki a tashe?"
Maimuna ta tambayeta ganin yanda take haɗa gumi,itah mai sunan tazo wajen jinya
amma gabaɗaya hankalin ta na wani wajen daban..
"Inason komawa gidane yanzunnan ƴar nan,an samu matsala,ciwon zuciya na ya
tashi,dama yakan yimin idan naga mai jinya. Ko zaku kulada itah kafin......."
Lahh karki damu Mammah kije gidan kawai,sha ɗaya tayi bazan iya tuƙin dare ba,amma
bari na faɗawa Saleem ya maidaki gida"
Godiya ta dungayiwa Maimuna har tagama ƙiran Saleem ya kaita gidan.
Shiga tayi wajen hajiyah Maryam wacce akayi wa allurar bacci tana kwance tamkar
gawa,kuka tayi a gunnata da kuma wasu surutai kafin ta fito suka tafi..
Sai sannu suke jeramata tana saiƙe nishi ɗaɗɗaya..
Har bakin sashenta Saleem ya rakota kafin ya wuce nasu part ɗin,dama jini ya bata
masa kaya daya taimakawa likita wajen sakama hajiya Maryam na'urar iska.
Tana ganin yabar wajen ta jefar da gyalen jikinta tareda miƙewa tsaye.
Kultum wacce ke falon a tsaye sai ganin tayi kamar an jefo ta ciki.
Hancinta ta ɗaga sama ta shaƙi iskar ɗakin kafin ta buɗe ido..
"Koma wacece zata gane kuranta,abinda ta ɗauka yafi ƙarfin sata"
"To amma hajiyah wannan data fasa babu komai,Sannan wacce ta tafi da itah inta
fasata fah itama"
"Wacce ta fashe aikin dana yiwa Maryam ne,a yanzu bazan ƙara amfani da jininta na
dawo da ƙuruciyata ba,Sannan ina buƙatar ƙarin ƙarfi da gaggawa,domin idan wani abu
yafaru da kwalbar Harsheelah nasan kaina zata dawo,domin kullum burinta shine taga
raunina"
Buɗe hannunta tayi a iska saiga wani ƙoƙo a cikeda jini ya bayyana.
Jinin da Sumaimah ta yanku a tsakiyar ɗakin ta dandala kana ta ɗiga a cikin na
ƙoƙon.
Cikin ƙanƙanin lokaci aka fara zaro mata bayi kamar rediyo..
"Macee macecee da ciki a jikinta,itaceeee wacce ta kasance masomin
alƙadarinki,surukar gidannan ta wannan da'rar mai samun nasara akanki idan baki
kawarta ba, Sannan kuma itama jinin gidannan ce"
"Me.....me kike faɗi Matiful duluk. ......wacce matar kenan badai matar Ahmad ba
danake nema ruwa a jallo,dama tana gidannan ne? Kuma jinin gidannan ce ta yaya
kenan?"
"Hhhhhh aiki ya ganki uwar gijiyar Harsheelah,dolene ki dage in kinason cigaba da
aiki da dodo,idan ba haka ba ƙarshenki ne kema yazo kamar yanda na wanda suka wanzu
kafinki ya wuce"
Ganin sun fara mata dariyar ƙeta ne yasa ta kawar da ƙoƙon ,domin bashine a gabanta
ba yanzu.
"Kultum ƙiramin Mulaifah inason in tambayeta,nasan dole tasan wanda ya shigo ɗakina
tunda har ya samu makullina"
"Amma hajiyah da alama tayi shaye shaye yauma,ba lallai tah.........."
"Ban tambayeki yin ja'inja dani ba,babu ruwana da shaye shayenta,inta kama zan
zaqulo duk abinda ke cikinta ciki kuwa harda shegen ɗan da ya baje koli a
mahaifarta idan zan samu amsata. Mtsw matsama kiga naje da kaina"
Bangaje Kultum tayi ta nufi ɗakin Mulaifah,tana kwance tayi ɗaɗɗayah,ko takalminta
bata cire ba.
Hajiyah Mammah na zuwa ta nuna hancinta wani hayaƙi ya fita,aikuwa cikin firgici
Mulaifah ta tashi ta zauna tana sosa hanci da atishawa.
"Maza faɗamin wa kika faɗawa inda key ɗin ɗakina yake?"
Ganin wacce take gabanta kamar kakar tata amma kuma tafita yarinta yasa ta murza
ido.
"Mtsw saida Sport G yacemin dama zanga abinda hankalina bazai ɗauka ba,amma hadda
zafi a hanci kaiii"
"Dallah ki ware kokuma namiki abinda yafi na hanci,don tsabar rashin sanin daidai
kinada ciki kike shaye shaye koh,in kika mutu ai ke kika sani,na rasa uwarki ma
ballantana ke. Ki faɗamin akan shashancinki wa kika bawa bayani ya shiga ɗakina?"
"Uhm na'am ni.....bansani ba iya kawai gyara tace zata miki na kaya shiyasa nace ta
shiga amma ni baruwana. Saboda ta gama miki da wuri har na bata fitila. Saboda
kullum kina cewa na zama mai kirki"
"Wacece itah baki santa bane?"
"Nasanta mana,wai granny mai ya shiga kankine,na ganki ma kaman wata sa'a ta
fahhhh"
Wani wawan hawa hajiyah Mammah tayiwa gadon Mulaifah tareda cafkar wuyanta.
"Faɗamin wacece ita,kokuma na ƙarisaki yanzunnan,matacciyah kawai"
"Wayyo Sumaimah,Sumaimah cefah mai laifina danna barta tashiga ɗakinki,naga dai
tanayimiki aiki sosai"
Sakin wuyan Sumaimah hajiyah Mammah tayi tareda daskarewa a wajen,meyasa ma bata
taba zarginta ba duk zamanta a gidan. Kenan.......kenan......mijinnata wato Ahmad
ne,kenan itace matarsa daya aura a rayuwarsa ta shekara biyar.......jinin mace mai
ciki Matiful duluk ya faɗa,kuma tanada ciki.....kenan tasan mai nake ƙulllawa
tsawon wannan lokacin,kallon ayaba kawai takeyi mata.
Wata dariyar takaici hajiyah Mammah tasaki lokaci ɗaya kuma ta haɗe rai ƙaman
hadarin marka marka mai shirin zubar da ruwa........
SADI-SAKHNA ce
09035784150
*SANADIN CACA*
-BOOK 2 (PAID)
Mallakar *SADI-SAKHNA*
09035784150
Bismillahir-rahmanir-raheem
Ki biya kan ki karantamin na biyu dan Allah. ga number ta nan mai son littafi na
ɗaya yayi min magana zan bashi shi kyautane.
*BOOK 2*
...36...
Bayan ta dawo daga sashen hajiyah Mammah banɗaki ta wuce,anan taga ciwon dataji da
kwalbar data fashe,tafin kafarta ne ta dama ya tsage,
Wankewa tayi ta ɗaure wajen kafin tazo ta kwanta,ɗaya kwalbar kuma dagata tayi tana
kallonta.
"Ko itama na fasata kaman yanda ɗayar ta fashe kai?. Ahah idan na fasata kuma wani
abun ya shafeni fah?"
Ruwa ta tara a cikin roba ta karanta ayoyin karya sihiri a ciki,bude kwalbar tayi
ta juye ruwan a ciki ta rufe.
"Bansani ba kozai karya abinda yake ciki ko ahah,amma Allah ina roqonka Allah yasa
yayi aiki"
Ajiyewa kwalbar tayi a cikin kayanta kafin ta kwanta.
Bayan ta kwanta ta daɗe bacci bai ɗauketa ba,shin abinda tayi daidaine kokuma saka
kanta tayi a haɗari.
Rufe idonta keda wuyah taji wata iska ta zagayeta,da guguwa ta taho amma ƙarfinta
ya ragu kafin ta iso gareta, tana gudu haka ta ɗauketa zuwa wani waje mai duhu.
Buɗe idanunta tayi daga mafarkin,saidai sabanin ɗakinsu a wani waje ta tsinci kanta
mai matuƙar duhu,dagane ba ɗakinsu bane saboda jin tana kwancene rairayi.
Hannunta takai kan cikinta,yana nan babu abinda ya sameshi. Tasbihi da fara da
salati duk wanda ya samu zuwa bakinta.
A haka tana wannan halin har haske yafara fitowa da gabas. Tunda ta tsinci kanta a
wajen take zaune bata motsaba har zuwa wannan lokacin.
Motsin takun mutum tajiyo yana zuwa,ɗauke numfashinta tayi har zuwa lokacin da aka
dalleta da wani abu mai haske.
"Hmmm wai dama kece ashe? Kinyi wasanki yanda ya dace,amma bari kiga naki ƙarshen
yanzunnan"
Kultum ce take maganar cikeda jin haushin Sumaimah.
Jin wanda yake magana maimakon taji tsoro sai maida martani da tayi.
"Kinyi mamaki ne da kikaganice,zatonku ku kaɗai kuka iya shiri,komin ƙanƙantar
allura ƙarfece,dan haka ba abar rainawa bace kuma akan iyalina babu abinda bazanyi
ba. Ganin baku kasheni ba duk da kunsan ni wacece to aikin danayi a sashennata ita
shugabar taki yayi mata illah sosai koh?"
Wani mari Kultum ta bawa Sumaimah mai ƙarfi.
"Hmmmm zatonki dan kinyi wannan ke wata shegiya ce,jira tazo tasameki kiga yanda
zata gama da ahalin da kike komai dominsun. Ke kuma zakiga baƙar wahalar da zaki
sha kafin mutuwarki"
Dunƙule hannunta tayi tareda faɗin wata kalma,nan da nan wani tururi ya kunnu a
dukkan ilahirin jikin Sumaimah,tana jin zafin kuwa ta fasa wani ihu mai cikeda ban
tausayi.
Bayan an sakashi a ɗakin duhu ya daku wajen Ahmad kurtun sojojin suka iyo dashi
yana makyarkyata,a awa ɗaya har kamanninsa sun sanja daga yanda suke.
Ƙafar Ahmad ya kama yana ƙiƙƙifta ido,ba sakin fuska haka ya buge hannunsa tareda
riƙo fuskarsa.
"Maza faramin bayanin ya akayi kasan Sayyadar da kake ambata"
"Iyee kamin rai aradu idan tasan mai zan faɗamuku zata kasheni muss har lahira"
"Sai akace maka nikuma zan ƙyaleka koh,idan kasake shafe wata daƙiƙar baka bani
bayani ba saina ballemaka maƙogaro."
Yawu ya haɗiya tareda cewa...
"Nida itah munsan juna tun ba yanzu ba,domin nine nake bata aljanun dazasu kaita
wajen ƙungiyarsu,ita kuma tana bani Abubuwa da dama,domin itace wacce shugaban
aljanu ya yarada da itah saboda tafi kai mata abinda yake buƙata,hatta manyan ƙasa
masu buƙatar nasara sukan shiga ƙungiyarta, mu kuma in an kawo mana bugun ƙasa
aljanun dake mata aiki sunfi bada irin waɗannan bayanan..
Yanzu haka ta bani wani aiki na wata yarinya dana ɗauke zuwa tsohon
gidanta,idan........"
"Wacce yarinya ce?"
"Bansani ba,kawai tace na ɗauketa daga cikin gidanku ne,daga nan bansan inda ta
kaita ba,amma nasan halinta yanzu haka ta kasheta,in kuma bata kasheta ba to tanada
wani shiri akanta ne"
"Innalillahi nasan Sumaimah kake nufi,ka faɗamin inda kuka kaita kafin na fasa
kanka
yanxunnan"
"Na faɗamaka gaskiya bansan inda take ba har raina,bansani ba,amma mai aikinta ce
ta sani haka itama,idan kuka bi ɗaya daga cikinsu zaku sameta"
Ciza baki Ahmad yayi tareda cewa.
"Ku maidashi kuci gaba da ta'bashi yanda kukeso,saina buƙaceshi tukunna"
SADI-SAKHNA ce
09035784150
*SANADIN CACA*
-BOOK 2 (PAID)
Mallakar *SADI-SAKHNA*
09035784150
Bismillahir-rahmanir-raheem
Ki biya kan ki karantamin na biyu dan Allah. ga number ta nan mai son littafi na
ɗaya yayi min magana zan bashi shi kyautane.
*BOOK 2*
...37...
Duk yanda Ahmad ya matsa amma ya kasa samo wani ƙwaƙwƙwaran bayani akan inda
matarsa take.
An fara samun sauƙi daga wajen hajiyah Maryam dan yanzu har tashi take amma bata
magana saidai tabi kowa da ido.
Yanxu ma a zaune suke Maimuna tana haɗa mata maganin dazata sha da zuma. Tun jiya
da malam hadi yazo ya ganta baice komai ba,sai magani daya bayar na wanka sha
dakuma turare,dukka kuma babu wanda ba'ayi mata ba a ciki,gashi har an samu sauƙi.
Fatee bazakije makarantar bane,yakamata ki gyara caurse ɗinnan ki tafi services
fah"
Karya kai tayi tareda kallon hajiyah maryam wacce take zaune sun data kanta da
pillow.
Kallon Fatee take da alamar itama tanaso ta tafi ɗin.
"Kingani ki shirya ki tafi,karki damu zata samu sauƙi sis ta tashi tacigaba da
tambayarki kinci abinci kuwa?"
Ta ƙarisa maganar cikin janta da abin wasa.
Ƴar dariya tayi ta rungumeta kaɗan kafin ta kalli mommy tasu.
"Mommy ki fara magana da wuri,i miss you"
Bayan ta fita zama Maimuna tayi a kusada itah tareda fara bata maganin kaɗan kaɗan.
Tana cikin bata maganinne hajiyah Mammah ta shigo tana daddafawa.
Da Maimuna suka gaisa tana tambayarta ya jiki.
"Da sauƙi maimunatu,ya jikin ummantaku,mai maganin yana kawowa dai koh naga tana
samun sauƙi"
"Eh yana kawowa,saidai ba wancan ɗin bane,wani yah Ahmad ya kawo shiyake mata
maganin"
"Ahmad kuma ahh gaskiya ya kyauta sosai"
"Ya jikinnaki hajiya da sauƙi dai koh? Naga kema jikin sai a hankali"
"Uhm na samu sauƙi,saina samu labarin wai Sumaimah matar Ahmad ce kuma abin
jajantawar daga gano hakan saita bata,ko suwaye suka ɗauketa oho. Allah dai ya
bayyanata"
"Ameen ya Allah,ni nafi tunanin koh a garin zata koma asibitine ta rasa hanya,ko ta
haɗu da wasu bata gari,amma Inshaallah za'a ganta,koma waye asirinsa zai tonu"
"Hakane kam Allah ya bayyana tah,ni bari zan fitah da driver zamuje likita ya
dubamin ƙafafuna."
"To shikenan hajiyah Mammah saikin dawo Allah ya sawwaƙe"
"Ameen Allah yabata lafiyah"
Duk maganar da suke hajiyah Maryam ta tsurawa hajiyah Mammah ido ko ƙoftawa batayi.
Ita kaɗai tasan mai yake faruwa.
Hajiyah Mammah tana fita Maimuna ma ta tashi zata maida kayan abincin da aka kawo.
Riƙo rigarta hajiyah Maryam tayi tareda cewa.
"Maza ki faɗawa yayanku Ahmad cewar yafara aikin,ke kuma kibi hajiyah Mammah a
bayah,duk motar data shiga ki faɗamasa wacce ce shiyasan mai zayyi akai. Yi sauri
babu lokaci,kada ta tafi baki san waccece ba"
"Mmmmmommy dama ......dama kina maganaaaa wayyo Allah na gode maka amm......."
"Godiya ga Allah yana da daɗi,amma kiyi sauri kiyi abinda naceee"
Cikin saurin jiki Maimuna ta fitah daga ɗakin domin ganin wacce motah hajiyah
Mammah zata shiga.
Tana fitah hajiyah Maryam ta tashi daga kan gadon,duk da har yanzu jikinta a riƙe
yake ga ciwon da ƙirjinta yakeyi,amma dai da sauƙi sosai.
Wayarta ta ɗauka ta ƙira Neelah,bugu ɗaya ta ɗauka.
"Hello Neelah kina ina,tafita yanzu Ahmad zai turamiki lokacation ɗin da motar
takebi ki zama cikin shiri,koda yake ma kizo ki ɗaukeni mutafi zan iya inaga"
"Ahah mommy ko barshi jikinki ba zai iya jurewa ba"
"No dolene naje,ta hakane zan jawo Abbansu zuwa wajen,so nake yau yaga abinda
uwarshi take aikatawa,koda kuwa hakan zai zama ƙarshen numfashina,na gaji haka"
Tana haki take maganar tareda saka hijabinta. Ta ƙofar baya ta dafah ta fita inda
zasu haɗu da neelan.
∆∆∆∆
Sumaimah (pov)
Yau kwana na uku kenan a wajennan,har yanzu banga hajiyah Mammah ba duk da nasan
itace ta bada umarnin a kawoni wajennan,sai wannan mai aikinnata mara imani,jinake
da inada dama zan iya yimata komai.
Jikina kaman an jefani cikin ruwan zafi haka nake jinsa,hannuna na saka a kan ɗan
cikina,tausayinsa nakeji sosai,yunwar da suke barni da itah abinci sau ɗaya,ga kuma
rashin bacci da azaba,nasan dukka sai ya shafeshi..
Hannuna na ɗaga sama ina addu'ar sirri ta Allah ya kawomin mafitah.
Yau har an kai hantsi amma bata zo ba,komai yasa oho. Duk da zata cutar dani amma
abincin datake bani shima wani abunne.
Hannuna na kalla wanda aka ɗaureni da sarƙa zuwa jikin ƙaramin gadon dayake
ɗakin,to wai tukunna ma nan inane. Gidane mai kyau amma ba kowa a ciki,ko a wanne
garine wanne ƙarnine oho.
Jan jiki nake na isa bakin window gidane mai kyau sosai, amma ginin na ɗan dane .
babbane sosai kuma bakowa,ko ihu zanyi baza'a gane ba.
Wani hawayene ya zubomin kan kuncinah. Ƙarar buɗe ƙofar naji hakan yasa na juyah da
sauri,nasan ma wacece tazo....
Ga mamakina wazan gani ya shigo,hajiyah Mammah ce itada kaltum. Wani murmushi
tayimin kaman na matar arziƙi,ja da baya nake harna danganta da bangon ɗakin.
Ƙirjina banda bugawa babu abinda yakeyi.
"Ohh kinsanma mai kikayi kenan,tunda daga shigowa har jikinki ya fara
karkarwa,bansan ke wacece ba inata nemanki,sai gashi kin nunamin kanki da kanki a
ruwan sanyi. Kece makasudin karyewar komai nawa,kama daga rushewar ƙungiyata,yaron
dana tsana nake son yabi duniyah,shine kika zauna dashi a matsayin miji harda yaro
koh?".
Kujera kaltum ta miƙomata ta zauna tana yiwa Sumaimah kallon ɗan tsako.
"Yanzun zaki faɗamin inda kika saka kwalbar da kika ɗauka kokuma saina miki abinda
nayiwa wacce ta gabaceki tukunna"
Kimm Sumaimah tayi da taurin zuciya ga ido a soye tana kallon hajiyah Mammah,vatace
komai ba amma kana ganinta kasan batada niyyar yin magana.
Abinda kaltum ta azabtar da itah ta nuna mata,kuka ta saka tana shashshafa jikinta.
"Bazaki samu abinda kike nema ba har abada."
"Nikuwa zan samu,kinsan harda na nuclear information ɗin zaki bani,shi ya manta mai
yasameshi a baya,amma keda kike matarsa nasan bazaki gagara sani ba. Zaki ce in
inaso na kasheki,amma karki manta nasan raunin mu mu mata......kaltum shigomin
dashi"
Tana faɗin hakan Kultum ta fita sai gata da sayyid ta riƙo hannunsa,yaron sai kuka
yake yana ƙiran deeja,idonsa cabb da hawaye.
Deejah ce ta shigo wani ƙaton mutum ya hankaɗota ɗakin itada inna larai,dukkansu
jikinsu ya baci ka shatar duka.
Zaro ido Sumaimah tayi tareda jan hannunta wanda yake ɗaure,jikinta yana rawa ta
kalli hajiyah Mammah tana jijjiga kai.
"Karki tabamin ahalina,kada ki kuskura ki tabamin ahalina,su basumiki komai ba,ki
barmin su"
Kuka take tana fincikar hannunta zata isa wajenda su Deejah suke.
Dukkansu sun nuna alamar tausayi banda Deejah wacce ta haɗe rai tana hararar
hajiyah Mammah.
"Meyasa kika yiwa Anty Sumaimah haka,mai tayi miki zakiyi mata haka. Uhmmmmmmm(taja
numfashi tareda rufe ido).
Baƙin ruhi,ke baƙin ruhi ce,sannan kuma kina amfani da baƙin ruhi......yana kusa
ina jiyishi,kin haɗa ruhinki dana Jinsin nas'ass(jinsin aljanune rabi mutum rabi
aljani). Mayaudara kana marasa amana"
Bayan ta gama bayanin buɗe idanunta tayi ta kalleni. Nasan mai take shirin yi dan
haka nayi mata magana.
"Deejah mai kike haka,kada ki kuskura ki koma gidan jiyah,bayan wahalar da kika sha
muma muka sha,ban yadda ki koma wannan rayuwar ba"
"Ba komawa zanyi na,tarayyar danayi dasu na tun ina yarinya ne,duk da mun rabu dasu
tunda na zabi mutane akansu,amma hakan bashi ya hanasu yimin alƙawarin taimako daya
sashi jinsunsu ba. Karki hanani,bake kaɗai suka taba ba,sun tabamin sayyid wanda
bazan iya haƙuri ba,yanzunnan zan dawo,zan arawa Harƙeelah jikina na wani lokaci.
Kada ki damu tanada mutunci,itace ta cinye kazar inna rammah"
Tana gama maganar tayi Murmushi,kallon mu tayi ta kalli Hajiyah mammah ma kafin ta
rufe ido..
Yin hakan keda wuyah ta ta faɗi a wajen kaman matacciyah.
"Mai take aikatawa,harƙeelah badai .......aljanar daji bace"
Zaro ido hajiyah Mammah tayi tareda zare wuƙah zata cakawa Deejah,ganin ta tura
mata tsafi amma yaƙi cinta.
Ihu nayi tareda runtse ido na,shikenan zata kasheta shikenan........
Jin shuru ne yasani buɗe ido,Abbah nagani ya riqe hannun hajiyah mamman,idanunsa
sun kaɗa sunyi jajur. Bayansa neelah ce,yah Musbahu Ahmad da kuma su Sameer. Iyah
Fatee ce kawai babu saisu inna ladiyo da ummi.
Wani daɗine da fatan nasara ya jiyarceni,saidai me.
SADI-SAKHNA ce
09035784150
*SANADIN CACA*
-BOOK 2 (PAID)
Mallakar *SADI-SAKHNA*
09035784150
Bismillahir-rahmanir-raheem
Ki biya kan ki karantamin na biyu dan Allah. ga number ta nan mai son littafi na
ɗaya yayi min magana zan bashi shi kyautane.
*BOOK 2*
...38...
Wunin ranar baƙi na dungayi,saida Ahmad yatsaya akan zan huta kafin suka tafi
gida,sunata mitar waina koresu. Sayyid ma inna yabi da Deejah.
Bayan ya rakasu dawowa ɗakin yayi,a baƙin ƙofa yatsaya yana tsuramin ido,kunya ce
ta kamani ganin kallon dayake min.
Takowa yayi zuwa gabana,kafin nace wani abun naji ya hade bakinsa da nawa,ban
hanashi ba dannasan dole zai buƙaci hakan sosai.
Sarrafani yakeyi a zafafe har kaina yafara daina ɗaukar darasin.
Cire bakinsa yayi numfashinsa yafara nauyi. Cikin dashashshiyar murya yafara
magana.
"Wannan gadon yayi kaɗan,muje ɗaki ina fatan kinada ƙarfin dazaki iya ɗaukar
wannan tuzurun koh"
Murmushi nayi tareda ɗaga masa kai.
"Nida na dauki goje waye bazan ɗauka ba?"
Dariyah yayi ganin tsokanarsa nakeyi,ɗagani yayi daga kan gadon zuwa namu ɗakin.
SADI-SAKHNA ce
09035784150
*SANADIN CACA*
-BOOK 2 (PAID)
Mallakar *SADI-SAKHNA*
09035784150
Bismillahir-rahmanir-raheem
Ki biya kan ki karantamin na biyu dan Allah. ga number ta nan mai son littafi na
ɗaya yayi min magana zan bashi shi kyautane.
*BOOK 2*
...39...
"Beb ganinan nagama shiryawa ma,hodace kawai ya saura da lip gloss na saka kayan"
"Ohh hayatee awarki biyu kenan kina shirinnan,har inna ta gyara Sayyid sun gama sun
shiga mota ke kinanan"
Shagwabe fuska tayi tareda juya masa bayanta.
"Zugemin zip ɗin to nagama shikenan,ga zafi kace saina saka hijabi dogo,motace fah"
"Uhm uhm saka hijabinki kinsan banason gyalennan sosai"
Hijabin ya miƙo mata onion color tasaka kafin yaja hannunta zuwa motah..
Tayi fari ta ƙara kyau ga jiki da cikin ɗan wata shida ya ƙara mata.
Gaban motar tashiga Sayyid da Deejah na baya.
Sai kuma motar da hajiyah Maryam da inna larai suke.
Bayan munje naso na kwana biyu amma Ahmad yaƙi,saboda inaso na zaga danginnamu, duk
da a baya basu nunamin ƙauna ba,amma badansu zanyi ba ai.
Haka ina gani mukayi kwana ɗaya muka kamo hanyar dawowa, zuwa gidana kuma cikin
dangin mahaifiyata,wacce yanzu nasan asalinta.
Bayan shekara biyu da haihuwar ƴan biyuna dukka mata, Maryam da zainab wanda ake
ƙiransu Islam da ilham. Dukkansu babu mai kamata,Neelah islam ta iyo,ilham kuma
hajiya Maryam har jikin.
Cikin ƙoshin lafiyah na rainesu har na yayesu,lokacin kuma Sayyid yashiga
makaranta,wanda yadawo hannuna da zama. Dan so nake nayi masa tarbiyyah yanda ya
kamata bata iyayen zamani ba.
Bayan yayennasu makaranta na shiga Jami'a,zan karanci Qur'anic science,dan inada
burin sanin ilimi a fannnin,a lokacin ne nayi planing na haihuwa,soyayya kawai muke
sha nida mijina Sannan kuma ina samun lokaci na yarana sosai.
****
Ina faka motar dana kasheta shigowa cikin gidan nayi,da islam naci karo ta dawo
daga sashen inna larai,wandonta ya jiƙe da fitsari,jijjiga kai nayi dam
takaci,magana saita siyarka amma tana fitsari a wando.
"Daga ina kike islam?"
"Gujin inna nake Unni"
"Ina ɗayar taki?"
"Tana bacci gujin inna"
"Kekuma kina yanda kikaga dama koh,yayah fah yana gidan Ummee ko wajen inna "
"Bashu dawoba da abbah"
"Hmm wuce to muje nacire miki wannan wandon"
Saida na gyara mata kafin nashiga kitchen a gurgune,ina cikin yi naji muryar Ahmad
a falo shida yaransa.
Jallop ɗin taliya nayi na fita da itah.
Sannu da dawowa nayi masa kafin na juya zan shiga ɗaki..
"Hayatee ke bazaki ci abincin bane zaki tafi yau?"
"Ahah banajin yunwa beb wanka ma nakeson yi,kuci abincinku kada ya huce"
"Ahha baki isa ba dawo ki zauna,banason zama da yunwa,zona baki a baki"
Zaro ido nayi bayan na zauna a gefensa,ganin zai bani kunya a gaban yara na saka
hannu mukaci tare.
Kallonsa nake yanda yake sakawa su ilham abincin a baki. A raina nace Alhamdulillah
da wannan baiwar da dddaɗar rayuwa.
Nima sainace ALHAMDULILLAH a fili tareda ajiye alƙalaminah. Kuyi haƙuri ta katse
littafin a haka,banida zabine exam ta matsoni. Da fatan zaku fahimta. Kowa in bai
masa ba yasake maimaita ƙarshen a kundin hasashensa😁.
✍🏼
THAMMAT BIHAMDULLAH......